quranm◉

Sura Al-Fil الفيل

#
105
↓
M
Aya
5
Fassara
Abubakar Mahmood Jummi

◉

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

105:1

أَلَمۡ تَرَ كَيۡفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِأَصۡحَٰبِ ٱلۡفِيلِ ﴿١﴾

Ashe, ba ka ga yadda Ubangijin ka Ya aikata ga mutanen giwa ba?

105:2

أَلَمۡ يَجۡعَلۡ كَيۡدَهُمۡ فِي تَضۡلِيلٖ ﴿٢﴾

Ashe, bai sanya kaidin su a cikin ɓata ba?

105:3

وَأَرۡسَلَ عَلَيۡهِمۡ طَيۡرًا أَبَابِيلَ ﴿٣﴾

Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a.

105:4

تَرۡمِيهِم بِحِجَارَةٖ مِّن سِجِّيلٖ ﴿٤﴾

Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.

105:5

فَجَعَلَهُمۡ كَعَصۡفٖ مَّأۡكُولِۭ ﴿٥﴾

Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?