quranm◉

Surah At-Tur transliteration

◉ Sura · ∞

52:1

وَٱلطُّورِ ﴿1﴾

Transliteration: Waalttoori

Translation: Inã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã).

52:2

وَكِتَٰبٖ مَّسۡطُورٖ ﴿2﴾

Transliteration: Wakitabin mastoorin

Translation: Da wani littãfi rubũtacce.

52:3

فِي رَقّٖ مَّنشُورٖ ﴿3﴾

Transliteration: Fee raqqin manshoorin

Translation: A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa.

52:4

وَٱلۡبَيۡتِ ٱلۡمَعۡمُورِ ﴿4﴾

Transliteration: Waalbayti almaAAmoori

Translation: Da Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda).

52:5

وَٱلسَّقۡفِ ٱلۡمَرۡفُوعِ ﴿5﴾

Transliteration: Waalssaqfi almarfooAAi

Translation: Da rufin nan da aka ɗaukaka.

52:6

وَٱلۡبَحۡرِ ٱلۡمَسۡجُورِ ﴿6﴾

Transliteration: Waalbahri almasjoori

Translation: Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa).

52:7

إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ لَوَٰقِعٞ ﴿7﴾

Transliteration: Inna AAathaba rabbika lawaqiAAun

Translation: Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce.

52:8

مَّا لَهُۥ مِن دَافِعٖ ﴿8﴾

Transliteration: Ma lahu min dafiAAin

Translation: Bã ta da mai tunkuɗẽwa.

52:9

يَوۡمَ تَمُورُ ٱلسَّمَآءُ مَوۡرٗا ﴿9﴾

Transliteration: Yawma tamooru alssamao mawran

Translation: Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo.

52:10

وَتَسِيرُ ٱلۡجِبَالُ سَيۡرٗا ﴿10﴾

Transliteration: Wataseeru aljibalu sayran

Translation: Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa.

52:11

فَوَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ﴿11﴾

Transliteration: Fawaylun yawmaithin lilmukaththibeena

Translation: To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.

52:12

ٱلَّذِينَ هُمۡ فِي خَوۡضٖ يَلۡعَبُونَ ﴿12﴾

Transliteration: Allatheena hum fee khawdin yalAAaboona

Translation: Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã.

52:13

يَوۡمَ يُدَعُّونَ إِلَىٰ نَارِ جَهَنَّمَ دَعًّا ﴿13﴾

Transliteration: Yawma yudaAAAAoona ila nari jahannama daAAAAan

Translation: Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa.

52:14

هَٰذِهِ ٱلنَّارُ ٱلَّتِي كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ ﴿14﴾

Transliteration: Hathihi alnnaru allatee kuntum biha tukaththiboona

Translation: (A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita."

52:15

أَفَسِحۡرٌ هَٰذَآ أَمۡ أَنتُمۡ لَا تُبۡصِرُونَ ﴿15﴾

Transliteration: Afasihrun hatha am antum la tubsiroona

Translation: "To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani?"

52:16

ٱصۡلَوۡهَا فَٱصۡبِرُوٓاْ أَوۡ لَا تَصۡبِرُواْ سَوَآءٌ عَلَيۡكُمۡۖ إِنَّمَا تُجۡزَوۡنَ مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ ﴿16﴾

Transliteration: Islawha faisbiroo aw la tasbiroo sawaon AAalaykum innama tujzawna ma kuntum taAAmaloona

Translation: "Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

52:17

إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّـٰتٖ وَنَعِيمٖ ﴿17﴾

Transliteration: Inna almuttaqeena fee jannatin wanaAAeemin

Translation: Lalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima.

52:18

فَٰكِهِينَ بِمَآ ءَاتَىٰهُمۡ رَبُّهُمۡ وَوَقَىٰهُمۡ رَبُّهُمۡ عَذَابَ ٱلۡجَحِيمِ ﴿18﴾

Transliteration: Fakiheena bima atahum rabbuhum wawaqahum rabbuhum AAathaba aljaheemi

Translation: Sunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm.

52:19

كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِيٓـَٔۢا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ ﴿19﴾

Transliteration: Kuloo waishraboo haneean bima kuntum taAAmaloona

Translation: (A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa."

52:20

مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ سُرُرٖ مَّصۡفُوفَةٖۖ وَزَوَّجۡنَٰهُم بِحُورٍ عِينٖ ﴿20﴾

Transliteration: Muttakieena AAala sururin masfoofatin wazawwajnahum bihoorin AAeenin

Translation: Sunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu.

52:21

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱتَّبَعَتۡهُمۡ ذُرِّيَّتُهُم بِإِيمَٰنٍ أَلۡحَقۡنَا بِهِمۡ ذُرِّيَّتَهُمۡ وَمَآ أَلَتۡنَٰهُم مِّنۡ عَمَلِهِم مِّن شَيۡءٖۚ كُلُّ ٱمۡرِيِٕۭ بِمَا كَسَبَ رَهِينٞ ﴿21﴾

Transliteration: Waallatheena amanoo waittabaAAathum thurriyyatuhum bieemanin alhaqna bihim thurriyyatahum wama alatnahum min AAamalihim min shayin kullu imriin bima kasaba raheenun

Translation: Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta.

52:22

وَأَمۡدَدۡنَٰهُم بِفَٰكِهَةٖ وَلَحۡمٖ مِّمَّا يَشۡتَهُونَ ﴿22﴾

Transliteration: Waamdadnahum bifakihatin walahmin mimma yashtahoona

Translation: Kuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari.

52:23

يَتَنَٰزَعُونَ فِيهَا كَأۡسٗا لَّا لَغۡوٞ فِيهَا وَلَا تَأۡثِيمٞ ﴿23﴾

Transliteration: YatanazaAAoona feeha kasan la laghwun feeha wala tatheemun

Translation: Sunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi.

52:24

وَيَطُوفُ عَلَيۡهِمۡ غِلۡمَانٞ لَّهُمۡ كَأَنَّهُمۡ لُؤۡلُؤٞ مَّكۡنُونٞ ﴿24﴾

Transliteration: Wayatoofu AAalayhim ghilmanun lahum kaannahum luluon maknoonun

Translation: Kuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle.

52:25

وَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ يَتَسَآءَلُونَ ﴿25﴾

Transliteration: Waaqbala baAAduhum AAala baAAdin yatasaaloona

Translation: Waɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna.

52:26

قَالُوٓاْ إِنَّا كُنَّا قَبۡلُ فِيٓ أَهۡلِنَا مُشۡفِقِينَ ﴿26﴾

Transliteration: Qaloo inna kunna qablu fee ahlina mushfiqeena

Translation: Suka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan (a dũniya) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro."

52:27

فَمَنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡنَا وَوَقَىٰنَا عَذَابَ ٱلسَّمُومِ ﴿27﴾

Transliteration: Famanna Allahu AAalayna wawaqana AAathaba alssamoomi

Translation: "To, Allah Yã yi mana kyautar falala, kuma Yã tsare mana azãbar iskar zãfi."

52:28

إِنَّا كُنَّا مِن قَبۡلُ نَدۡعُوهُۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡبَرُّ ٱلرَّحِيمُ ﴿28﴾

Transliteration: Inna kunna min qablu nadAAoohu innahu huwa albarru alrraheemu

Translation: "Lalle mũ mun kasance, a gãbanin haka, munã kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatãwa, Mai rahama."

52:29

فَذَكِّرۡ فَمَآ أَنتَ بِنِعۡمَتِ رَبِّكَ بِكَاهِنٖ وَلَا مَجۡنُونٍ ﴿29﴾

Transliteration: Fathakkir fama anta biniAAmati rabbika bikahin wala majnoonin

Translation: To, ka tunãtar kai fa sabõda ni'imar Ubangjinka, bã bõka kake ba, kuma bã mahaukaci ba.

52:30

أَمۡ يَقُولُونَ شَاعِرٞ نَّتَرَبَّصُ بِهِۦ رَيۡبَ ٱلۡمَنُونِ ﴿30﴾

Transliteration: Am yaqooloona shaAAirun natarabbasu bihi rayba almanooni

Translation: Shin zã su ce: "Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ"?

52:31

قُلۡ تَرَبَّصُواْ فَإِنِّي مَعَكُم مِّنَ ٱلۡمُتَرَبِّصِينَ ﴿31﴾

Transliteration: Qul tarabbasoo fainnee maAAakum mina almutarabbiseena

Translation: Ka ce: "Ku yi jira, domin nĩ ma lalle inã a cikin mãsu jira tãre da ku."

52:32

أَمۡ تَأۡمُرُهُمۡ أَحۡلَٰمُهُم بِهَٰذَآۚ أَمۡ هُمۡ قَوۡمٞ طَاغُونَ ﴿32﴾

Transliteration: Am tamuruhum ahlamuhum bihatha am hum qawmun taghoona

Translation: Shin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi?

52:33

أَمۡ يَقُولُونَ تَقَوَّلَهُۥۚ بَل لَّا يُؤۡمِنُونَ ﴿33﴾

Transliteration: Am yaqooloona taqawwalahu bal la yuminoona

Translation: Shin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙãga faɗarsa"? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba.

52:34

فَلۡيَأۡتُواْ بِحَدِيثٖ مِّثۡلِهِۦٓ إِن كَانُواْ صَٰدِقِينَ ﴿34﴾

Transliteration: Falyatoo bihadeethin mithlihi in kanoo sadiqeena

Translation: Sai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne.

52:35

أَمۡ خُلِقُواْ مِنۡ غَيۡرِ شَيۡءٍ أَمۡ هُمُ ٱلۡخَٰلِقُونَ ﴿35﴾

Transliteration: Am khuliqoo min ghayri shayin am humu alkhaliqoona

Translation: Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta?

52:36

أَمۡ خَلَقُواْ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۚ بَل لَّا يُوقِنُونَ ﴿36﴾

Transliteration: Am khalaqoo alssamawati waalarda bal la yooqinoona

Translation: Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba.

52:37

أَمۡ عِندَهُمۡ خَزَآئِنُ رَبِّكَ أَمۡ هُمُ ٱلۡمُصَۜيۡطِرُونَ ﴿37﴾

Transliteration: Am AAindahum khazainu rabbika am humu almusaytiroona

Translation: Shin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya?

52:38

أَمۡ لَهُمۡ سُلَّمٞ يَسۡتَمِعُونَ فِيهِۖ فَلۡيَأۡتِ مُسۡتَمِعُهُم بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٍ ﴿38﴾

Transliteration: Am lahum sullamun yastamiAAoona feehi falyati mustamiAAuhum bisultanin mubeenin

Translation: Shin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne.

52:39

أَمۡ لَهُ ٱلۡبَنَٰتُ وَلَكُمُ ٱلۡبَنُونَ ﴿39﴾

Transliteration: Am lahu albanatu walakumu albanoona

Translation: Shin, Yanã da 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne?

52:40

أَمۡ تَسۡـَٔلُهُمۡ أَجۡرٗا فَهُم مِّن مَّغۡرَمٖ مُّثۡقَلُونَ ﴿40﴾

Transliteration: Am tasaluhum ajran fahum min maghramin muthqaloona

Translation: Shin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar?

52:41

أَمۡ عِندَهُمُ ٱلۡغَيۡبُ فَهُمۡ يَكۡتُبُونَ ﴿41﴾

Transliteration: Am AAindahumu alghaybu fahum yaktuboona

Translation: Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa?

52:42

أَمۡ يُرِيدُونَ كَيۡدٗاۖ فَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ هُمُ ٱلۡمَكِيدُونَ ﴿42﴾

Transliteration: Am yureedoona kaydan faallatheena kafaroo humu almakeedoona

Translation: Shin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi.

52:43

أَمۡ لَهُمۡ إِلَٰهٌ غَيۡرُ ٱللَّهِۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشۡرِكُونَ ﴿43﴾

Transliteration: Am lahum ilahun ghayru Allahi subhana Allahi AAamma yushrikoona

Translation: Shin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki!

52:44

وَإِن يَرَوۡاْ كِسۡفٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ سَاقِطٗا يَقُولُواْ سَحَابٞ مَّرۡكُومٞ ﴿44﴾

Transliteration: Wain yaraw kisfan mina alssamai saqitan yaqooloo sahabun markoomun

Translation: Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna.

52:45

فَذَرۡهُمۡ حَتَّىٰ يُلَٰقُواْ يَوۡمَهُمُ ٱلَّذِي فِيهِ يُصۡعَقُونَ ﴿45﴾

Transliteration: Fatharhum hatta yulaqoo yawmahumu allathee feehi yusAAaqoona

Translation: To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa.

52:46

يَوۡمَ لَا يُغۡنِي عَنۡهُمۡ كَيۡدُهُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ ﴿46﴾

Transliteration: Yawma la yughnee AAanhum kayduhum shayan wala hum yunsaroona

Translation: Rãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su.

52:47

وَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ عَذَابٗا دُونَ ذَٰلِكَ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ ﴿47﴾

Transliteration: Wainna lillatheena thalamoo AAathaban doona thalika walakinna aktharahum la yaAAlamoona

Translation: Kuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba.

52:48

وَٱصۡبِرۡ لِحُكۡمِ رَبِّكَ فَإِنَّكَ بِأَعۡيُنِنَاۖ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ حِينَ تَقُومُ ﴿48﴾

Transliteration: Waisbir lihukmi rabbika fainnaka biaAAyunina wasabbih bihamdi rabbika heena taqoomu

Translation: Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnun Mu, kuma ka tsarkake Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu).

52:49

وَمِنَ ٱلَّيۡلِ فَسَبِّحۡهُ وَإِدۡبَٰرَ ٱلنُّجُومِ ﴿49﴾

Transliteration: Wamina allayli fasabbihhu waidbara alnnujoomi

Translation: Kuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) da lõkacin jũyãwar taurãri.

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download