quranm◉

Surah Al-Hijr transliteration

◉ Sura · ∞

15:1

الٓرۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ وَقُرۡءَانٖ مُّبِينٖ ﴿1﴾

Transliteration: Aliflamra tilka ayatu alkitabi waquranin mubeenin

Translation: A. L̃.R. Waɗan can ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa.

15:2

رُّبَمَا يَوَدُّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡ كَانُواْ مُسۡلِمِينَ ﴿2﴾

Transliteration: Rubama yawaddu allatheena kafaroo law kanoo muslimeena

Translation: Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi.

15:3

ذَرۡهُمۡ يَأۡكُلُواْ وَيَتَمَتَّعُواْ وَيُلۡهِهِمُ ٱلۡأَمَلُۖ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ ﴿3﴾

Transliteration: Tharhum yakuloo wayatamattaAAoo wayulhihimu alamalu fasawfa yaAAlamoona

Translation: Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani.

15:4

وَمَآ أَهۡلَكۡنَا مِن قَرۡيَةٍ إِلَّا وَلَهَا كِتَابٞ مَّعۡلُومٞ ﴿4﴾

Transliteration: Wama ahlakna min qaryatin illa walaha kitabun maAAloomun

Translation: Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne.

15:5

مَّا تَسۡبِقُ مِنۡ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ ﴿5﴾

Transliteration: Ma tasbiqu min ommatin ajalaha wama yastakhiroona

Translation: Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba.

15:6

وَقَالُواْ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِي نُزِّلَ عَلَيۡهِ ٱلذِّكۡرُ إِنَّكَ لَمَجۡنُونٞ ﴿6﴾

Transliteration: Waqaloo ya ayyuha allathee nuzzila AAalayhi alththikru innaka lamajnoonun

Translation: Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne."

15:7

لَّوۡمَا تَأۡتِينَا بِٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ ﴿7﴾

Transliteration: Law ma tateena bialmalaikati in kunta mina alssadiqeena

Translation: "Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?"

15:8

مَا نُنَزِّلُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَمَا كَانُوٓاْ إِذٗا مُّنظَرِينَ ﴿8﴾

Transliteration: Ma nunazzilu almalaikata illa bialhaqqi wama kanoo ithan munthareena

Translation: Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya, bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba.

15:9

إِنَّا نَحۡنُ نَزَّلۡنَا ٱلذِّكۡرَ وَإِنَّا لَهُۥ لَحَٰفِظُونَ ﴿9﴾

Transliteration: Inna nahnu nazzalna alththikra wainna lahu lahafithoona

Translation: Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lale Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi.

15:10

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ فِي شِيَعِ ٱلۡأَوَّلِينَ ﴿10﴾

Transliteration: Walaqad arsalna min qablika fee shiyaAAi alawwaleena

Translation: Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãnin ka.

15:11

وَمَا يَأۡتِيهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ ﴿11﴾

Transliteration: Wama yateehim min rasoolin illa kanoo bihi yastahzioona

Translation: Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi.

15:12

كَذَٰلِكَ نَسۡلُكُهُۥ فِي قُلُوبِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ ﴿12﴾

Transliteration: Kathalika naslukuhu fee quloobi almujrimeena

Translation: Kamar wancan ne Muke shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi.

15:13

لَا يُؤۡمِنُونَ بِهِۦ وَقَدۡ خَلَتۡ سُنَّةُ ٱلۡأَوَّلِينَ ﴿13﴾

Transliteration: La yuminoona bihi waqad khalat sunnatu alawwaleena

Translation: Bã su yin ĩmãni da shi,( kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige.

15:14

وَلَوۡ فَتَحۡنَا عَلَيۡهِم بَابٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ فَظَلُّواْ فِيهِ يَعۡرُجُونَ ﴿14﴾

Transliteration: Walaw fatahna AAalayhim baban mina alssamai fathalloo feehi yaAArujoona

Translation: Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa.

15:15

لَقَالُوٓاْ إِنَّمَا سُكِّرَتۡ أَبۡصَٰرُنَا بَلۡ نَحۡنُ قَوۡمٞ مَّسۡحُورُونَ ﴿15﴾

Transliteration: Laqaloo innama sukkirat absaruna bal nahnu qawmun mashooroona

Translation: Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce."

15:16

وَلَقَدۡ جَعَلۡنَا فِي ٱلسَّمَآءِ بُرُوجٗا وَزَيَّنَّـٰهَا لِلنَّـٰظِرِينَ ﴿16﴾

Transliteration: Walaqad jaAAalna fee alssamai buroojan wazayyannaha lilnnathireena

Translation: Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo.

15:17

وَحَفِظۡنَٰهَا مِن كُلِّ شَيۡطَٰنٖ رَّجِيمٍ ﴿17﴾

Transliteration: Wahafithnaha min kulli shaytanin rajeemin

Translation: Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa.

15:18

إِلَّا مَنِ ٱسۡتَرَقَ ٱلسَّمۡعَ فَأَتۡبَعَهُۥ شِهَابٞ مُّبِينٞ ﴿18﴾

Transliteration: Illa mani istaraqa alssamAAa faatbaAAahu shihabun mubeenun

Translation: Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi.

15:19

وَٱلۡأَرۡضَ مَدَدۡنَٰهَا وَأَلۡقَيۡنَا فِيهَا رَوَٰسِيَ وَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ شَيۡءٖ مَّوۡزُونٖ ﴿19﴾

Transliteration: Waalarda madadnaha waalqayna feeha rawasiya waanbatna feeha min kulli shayin mawzoonin

Translation: Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli.

15:20

وَجَعَلۡنَا لَكُمۡ فِيهَا مَعَٰيِشَ وَمَن لَّسۡتُمۡ لَهُۥ بِرَٰزِقِينَ ﴿20﴾

Transliteration: WajaAAalna lakum feeha maAAayisha waman lastum lahu biraziqeena

Translation: Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba.

15:21

وَإِن مِّن شَيۡءٍ إِلَّا عِندَنَا خَزَآئِنُهُۥ وَمَا نُنَزِّلُهُۥٓ إِلَّا بِقَدَرٖ مَّعۡلُومٖ ﴿21﴾

Transliteration: Wain min shayin illa AAindana khazainuhu wama nunazziluhu illa biqadarin maAAloomin

Translation: Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne.

15:22

وَأَرۡسَلۡنَا ٱلرِّيَٰحَ لَوَٰقِحَ فَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَسۡقَيۡنَٰكُمُوهُ وَمَآ أَنتُمۡ لَهُۥ بِخَٰزِنِينَ ﴿22﴾

Transliteration: Waarsalna alrriyaha lawaqiha faanzalna mina alssamai maan faasqaynakumoohu wama antum lahu bikhazineena

Translation: Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba.

15:23

وَإِنَّا لَنَحۡنُ نُحۡيِۦ وَنُمِيتُ وَنَحۡنُ ٱلۡوَٰرِثُونَ ﴿23﴾

Transliteration: Wainna lanahnu nuhyee wanumeetu wanahnu alwarithoona

Translation: Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada.

15:24

وَلَقَدۡ عَلِمۡنَا ٱلۡمُسۡتَقۡدِمِينَ مِنكُمۡ وَلَقَدۡ عَلِمۡنَا ٱلۡمُسۡتَـٔۡخِرِينَ ﴿24﴾

Transliteration: Walaqad AAalimna almustaqdimeena minkum walaqad AAalimna almustakhireena

Translation: Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri.

15:25

وَإِنَّ رَبَّكَ هُوَ يَحۡشُرُهُمۡۚ إِنَّهُۥ حَكِيمٌ عَلِيمٞ ﴿25﴾

Transliteration: Wainna rabbaka huwa yahshuruhum innahu hakeemun AAaleemun

Translation: Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani.

15:26

وَلَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِن صَلۡصَٰلٖ مِّنۡ حَمَإٖ مَّسۡنُونٖ ﴿26﴾

Transliteration: Walaqad khalaqna alinsana min salsalin min hamain masnoonin

Translation: Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja.

15:27

وَٱلۡجَآنَّ خَلَقۡنَٰهُ مِن قَبۡلُ مِن نَّارِ ٱلسَّمُومِ ﴿27﴾

Transliteration: Waaljanna khalaqnahu min qablu min nari alssamoomi

Translation: Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar iskar zafi.

15:28

وَإِذۡ قَالَ رَبُّكَ لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ إِنِّي خَٰلِقُۢ بَشَرٗا مِّن صَلۡصَٰلٖ مِّنۡ حَمَإٖ مَّسۡنُونٖ ﴿28﴾

Transliteration: Waith qala rabbuka lilmalaikati innee khaliqun basharan min salsalin min hamain masnoonin

Translation: Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã'iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja."

15:29

فَإِذَا سَوَّيۡتُهُۥ وَنَفَخۡتُ فِيهِ مِن رُّوحِي فَقَعُواْ لَهُۥ سَٰجِدِينَ ﴿29﴾

Transliteration: Faitha sawwaytuhu wanafakhtu feehi min roohee faqaAAoo lahu sajideena

Translation: "To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada."

15:30

فَسَجَدَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ كُلُّهُمۡ أَجۡمَعُونَ ﴿30﴾

Transliteration: Fasajada almalaikatu kulluhum ajmaAAoona

Translation: Sai malã'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya.

15:31

إِلَّآ إِبۡلِيسَ أَبَىٰٓ أَن يَكُونَ مَعَ ٱلسَّـٰجِدِينَ ﴿31﴾

Transliteration: Illa ibleesa aba an yakoona maAAa alssajideena

Translation: Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar.

15:32

قَالَ يَـٰٓإِبۡلِيسُ مَا لَكَ أَلَّا تَكُونَ مَعَ ٱلسَّـٰجِدِينَ ﴿32﴾

Transliteration: Qala ya ibleesu ma laka alla takoona maAAa alssajideena

Translation: Ya ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?"

15:33

قَالَ لَمۡ أَكُن لِّأَسۡجُدَ لِبَشَرٍ خَلَقۡتَهُۥ مِن صَلۡصَٰلٖ مِّنۡ حَمَإٖ مَّسۡنُونٖ ﴿33﴾

Transliteration: Qala lam akun liasjuda libasharin khalaqtahu min salsalin min hamain masnoonin

Translation: Ya ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja."

15:34

قَالَ فَٱخۡرُجۡ مِنۡهَا فَإِنَّكَ رَجِيمٞ ﴿34﴾

Transliteration: Qala faokhruj minha fainnaka rajeemun

Translation: Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne."

15:35

وَإِنَّ عَلَيۡكَ ٱللَّعۡنَةَ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلدِّينِ ﴿35﴾

Transliteration: Wainna AAalayka allaAAnata ila yawmi alddeeni

Translation: "Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako."

15:36

قَالَ رَبِّ فَأَنظِرۡنِيٓ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ ﴿36﴾

Transliteration: Qala rabbi faanthirnee ila yawmi yubAAathoona

Translation: Ya ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su."

15:37

قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ ٱلۡمُنظَرِينَ ﴿37﴾

Transliteration: Qala fainnaka mina almunthareena

Translation: Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri."

15:38

إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡوَقۡتِ ٱلۡمَعۡلُومِ ﴿38﴾

Transliteration: Ila yawmi alwaqti almaAAloomi

Translation: "Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sanan ne."

15:39

قَالَ رَبِّ بِمَآ أَغۡوَيۡتَنِي لَأُزَيِّنَنَّ لَهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَأُغۡوِيَنَّهُمۡ أَجۡمَعِينَ ﴿39﴾

Transliteration: Qala rabbi bima aghwaytanee laozayyinanna lahum fee alardi walaoghwiyannahum ajmaAAeena

Translation: Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya."

15:40

إِلَّا عِبَادَكَ مِنۡهُمُ ٱلۡمُخۡلَصِينَ ﴿40﴾

Transliteration: Illa AAibadaka minhumu almukhlaseena

Translation: "Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake."

15:41

قَالَ هَٰذَا صِرَٰطٌ عَلَيَّ مُسۡتَقِيمٌ ﴿41﴾

Transliteration: Qala hatha siratun AAalayya mustaqeemun

Translation: Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici."

15:42

إِنَّ عِبَادِي لَيۡسَ لَكَ عَلَيۡهِمۡ سُلۡطَٰنٌ إِلَّا مَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلۡغَاوِينَ ﴿42﴾

Transliteration: Inna AAibadee laysa laka AAalayhim sultanun illa mani ittabaAAaka mina alghaweena

Translation: "Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu."

15:43

وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمَوۡعِدُهُمۡ أَجۡمَعِينَ ﴿43﴾

Transliteration: Wainna jahannama lamawAAiduhum ajmaAAeena

Translation: Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'akawartarsu gabã ɗaya.

15:44

لَهَا سَبۡعَةُ أَبۡوَٰبٖ لِّكُلِّ بَابٖ مِّنۡهُمۡ جُزۡءٞ مَّقۡسُومٌ ﴿44﴾

Transliteration: Laha sabAAatu abwabin likulli babin minhum juzon maqsoomun

Translation: Tanã da ƙõfõfi bakwai, ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe.

15:45

إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّـٰتٖ وَعُيُونٍ ﴿45﴾

Transliteration: Inna almuttaqeena fee jannatin waAAuyoonin

Translation: Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa.

15:46

ٱدۡخُلُوهَا بِسَلَٰمٍ ءَامِنِينَ ﴿46﴾

Transliteration: Odkhulooha bisalamin amineena

Translation: "Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu."

15:47

وَنَزَعۡنَا مَا فِي صُدُورِهِم مِّنۡ غِلٍّ إِخۡوَٰنًا عَلَىٰ سُرُرٖ مُّتَقَٰبِلِينَ ﴿47﴾

Transliteration: WanazaAAna ma fee sudoorihim min ghillin ikhwanan AAala sururin mutaqabileena

Translation: Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã.

15:48

لَا يَمَسُّهُمۡ فِيهَا نَصَبٞ وَمَا هُم مِّنۡهَا بِمُخۡرَجِينَ ﴿48﴾

Transliteration: La yamassuhum feeha nasabun wama hum minha bimukhrajeena

Translation: Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikin ta ba.

15:49

نَبِّئۡ عِبَادِيٓ أَنِّيٓ أَنَا ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ ﴿49﴾

Transliteration: Nabbi AAibadee annee ana alghafooru alrraheemu

Translation: Ka bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai.

15:50

وَأَنَّ عَذَابِي هُوَ ٱلۡعَذَابُ ٱلۡأَلِيمُ ﴿50﴾

Transliteration: Wa anna AAathabee huwa alAAathabu alaleemu

Translation: Kuma azãbãTa ita ce Azãba mai raɗaɗi.

15:51

وَنَبِّئۡهُمۡ عَن ضَيۡفِ إِبۡرَٰهِيمَ ﴿51﴾

Transliteration: Wanabbihum AAan dayfi ibraheema

Translation: Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm.

15:52

إِذۡ دَخَلُواْ عَلَيۡهِ فَقَالُواْ سَلَٰمٗا قَالَ إِنَّا مِنكُمۡ وَجِلُونَ ﴿52﴾

Transliteration: Ith dakhaloo AAalayhi faqaloo salaman qala inna minkum wajiloona

Translation: A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne."

15:53

قَالُواْ لَا تَوۡجَلۡ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَٰمٍ عَلِيمٖ ﴿53﴾

Transliteration: Qaloo la tawjal inna nubashshiruka bighulamin AAaleemin

Translation: Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani."

15:54

قَالَ أَبَشَّرۡتُمُونِي عَلَىٰٓ أَن مَّسَّنِيَ ٱلۡكِبَرُ فَبِمَ تُبَشِّرُونَ ﴿54﴾

Transliteration: Qala abashshartumoonee AAala an massaniya alkibaru fabima tubashshirooni

Translation: Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?"

15:55

قَالُواْ بَشَّرۡنَٰكَ بِٱلۡحَقِّ فَلَا تَكُن مِّنَ ٱلۡقَٰنِطِينَ ﴿55﴾

Transliteration: Qaloo bashsharnaka bialhaqqi fala takun mina alqaniteena

Translation: Suka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni."

15:56

قَالَ وَمَن يَقۡنَطُ مِن رَّحۡمَةِ رَبِّهِۦٓ إِلَّا ٱلضَّآلُّونَ ﴿56﴾

Transliteration: Qala waman yaqnatu min rahmati rabbihi illa alddalloona

Translation: Ya ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijin sa, fãce ɓatattu?"

15:57

قَالَ فَمَا خَطۡبُكُمۡ أَيُّهَا ٱلۡمُرۡسَلُونَ ﴿57﴾

Transliteration: Qala fama khatbukum ayyuha almursaloona

Translation: Ya ce: "To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni!"

15:58

قَالُوٓاْ إِنَّآ أُرۡسِلۡنَآ إِلَىٰ قَوۡمٖ مُّجۡرِمِينَ ﴿58﴾

Transliteration: Qaloo inna orsilna ila qawmin mujrimeena

Translation: Suka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi."

15:59

إِلَّآ ءَالَ لُوطٍ إِنَّا لَمُنَجُّوهُمۡ أَجۡمَعِينَ ﴿59﴾

Transliteration: Illa ala lootin inna lamunajjoohum ajmaAAeena

Translation: "Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya."

15:60

إِلَّا ٱمۡرَأَتَهُۥ قَدَّرۡنَآ إِنَّهَا لَمِنَ ٱلۡغَٰبِرِينَ ﴿60﴾

Transliteration: Illa imraatahu qaddarna innaha lamina alghabireena

Translation: "Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka."

15:61

فَلَمَّا جَآءَ ءَالَ لُوطٍ ٱلۡمُرۡسَلُونَ ﴿61﴾

Transliteration: Falamma jaa ala lootin almursaloona

Translation: To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu,

15:62

قَالَ إِنَّكُمۡ قَوۡمٞ مُّنكَرُونَ ﴿62﴾

Transliteration: Qala innakum qawmun munkaroona

Translation: Ya ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba."

15:63

قَالُواْ بَلۡ جِئۡنَٰكَ بِمَا كَانُواْ فِيهِ يَمۡتَرُونَ ﴿63﴾

Transliteration: Qaloo bal jinaka bima kanoo feehi yamtaroona

Translation: Suka ce: "Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa."

15:64

وَأَتَيۡنَٰكَ بِٱلۡحَقِّ وَإِنَّا لَصَٰدِقُونَ ﴿64﴾

Transliteration: Waataynaka bialhaqqi wainna lasadiqoona

Translation: "Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne."

15:65

فَأَسۡرِ بِأَهۡلِكَ بِقِطۡعٖ مِّنَ ٱلَّيۡلِ وَٱتَّبِعۡ أَدۡبَٰرَهُمۡ وَلَا يَلۡتَفِتۡ مِنكُمۡ أَحَدٞ وَٱمۡضُواْ حَيۡثُ تُؤۡمَرُونَ ﴿65﴾

Transliteration: Faasri biahlika biqitAAin mina allayli waittabiAA adbarahum wala yaltafit minkum ahadun waimdoo haythu tumaroona

Translation: "Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku."

15:66

وَقَضَيۡنَآ إِلَيۡهِ ذَٰلِكَ ٱلۡأَمۡرَ أَنَّ دَابِرَ هَـٰٓؤُلَآءِ مَقۡطُوعٞ مُّصۡبِحِينَ ﴿66﴾

Transliteration: Waqadayna ilayhi thalika alamra anna dabira haolai maqtooAAun musbiheena

Translation: Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga Asuba.

15:67

وَجَآءَ أَهۡلُ ٱلۡمَدِينَةِ يَسۡتَبۡشِرُونَ ﴿67﴾

Transliteration: Wajaa ahlu almadeenati yastabshiroona

Translation: Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra.

15:68

قَالَ إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ ضَيۡفِي فَلَا تَفۡضَحُونِ ﴿68﴾

Transliteration: Qala inna haolai dayfee fala tafdahooni

Translation: Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni."

15:69

وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَلَا تُخۡزُونِ ﴿69﴾

Transliteration: Waittaqoo Allaha wala tukhzooni

Translation: "Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki."

15:70

قَالُوٓاْ أَوَلَمۡ نَنۡهَكَ عَنِ ٱلۡعَٰلَمِينَ ﴿70﴾

Transliteration: Qaloo awalam nanhaka AAani alAAalameena

Translation: Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?"

15:71

قَالَ هَـٰٓؤُلَآءِ بَنَاتِيٓ إِن كُنتُمۡ فَٰعِلِينَ ﴿71﴾

Transliteration: Qala haolai banatee in kuntum faAAileena

Translation: Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."

15:72

لَعَمۡرُكَ إِنَّهُمۡ لَفِي سَكۡرَتِهِمۡ يَعۡمَهُونَ ﴿72﴾

Transliteration: LaAAamruka innahum lafee sakratihim yaAAmahoona

Translation: Rantsuwa da rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa.

15:73

فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّيۡحَةُ مُشۡرِقِينَ ﴿73﴾

Transliteration: Faakhathathumu alssayhatu mushriqeena

Translation: Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã.

15:74

فَجَعَلۡنَا عَٰلِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِمۡ حِجَارَةٗ مِّن سِجِّيلٍ ﴿74﴾

Transliteration: FajaAAalna AAaliyaha safilaha waamtarna AAalayhim hijaratan min sijjeelin

Translation: Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu.

15:75

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّلۡمُتَوَسِّمِينَ ﴿75﴾

Transliteration: Inna fee thalika laayatin lilmutawassimeena

Translation: Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali.

15:76

وَإِنَّهَا لَبِسَبِيلٖ مُّقِيمٍ ﴿76﴾

Transliteration: Wainnaha labisabeelin muqeemin

Translation: Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya.

15:77

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ ﴿77﴾

Transliteration: Inna fee thalika laayatan lilmumineena

Translation: Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni.

15:78

وَإِن كَانَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡأَيۡكَةِ لَظَٰلِمِينَ ﴿78﴾

Transliteration: Wain kana ashabu alaykati lathalimeena

Translation: Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci!

15:79

فَٱنتَقَمۡنَا مِنۡهُمۡ وَإِنَّهُمَا لَبِإِمَامٖ مُّبِينٖ ﴿79﴾

Transliteration: Faintaqamna minhum wainnahuma labiimamin mubeenin

Translation: Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani.

15:80

وَلَقَدۡ كَذَّبَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡحِجۡرِ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ﴿80﴾

Transliteration: Walaqad kaththaba ashabu alhijri almursaleena

Translation: Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri sun ƙaryata Manzanni.

15:81

وَءَاتَيۡنَٰهُمۡ ءَايَٰتِنَا فَكَانُواْ عَنۡهَا مُعۡرِضِينَ ﴿81﴾

Transliteration: Waataynahum ayatina fakanoo AAanha muAArideena

Translation: Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su.

15:82

وَكَانُواْ يَنۡحِتُونَ مِنَ ٱلۡجِبَالِ بُيُوتًا ءَامِنِينَ ﴿82﴾

Transliteration: Wakanoo yanhitoona mina aljibali buyootan amineena

Translation: Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu.

15:83

فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّيۡحَةُ مُصۡبِحِينَ ﴿83﴾

Transliteration: Faakhathathumu alssayhatu musbiheena

Translation: Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga Asuba.

15:84

فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ ﴿84﴾

Transliteration: Fama aghna AAanhum ma kanoo yaksiboona

Translation: Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba.

15:85

وَمَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۗ وَإِنَّ ٱلسَّاعَةَ لَأٓتِيَةٞۖ فَٱصۡفَحِ ٱلصَّفۡحَ ٱلۡجَمِيلَ ﴿85﴾

Transliteration: Wama khalaqna alssamawati waalarda wama baynahuma illa bialhaqqi wainna alssaAAata laatiyatun faisfahi alssafha aljameela

Translation: Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau.

15:86

إِنَّ رَبَّكَ هُوَ ٱلۡخَلَّـٰقُ ٱلۡعَلِيمُ ﴿86﴾

Transliteration: Inna rabbaka huwa alkhallaqu alAAaleemu

Translation: Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani.

15:87

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَٰكَ سَبۡعٗا مِّنَ ٱلۡمَثَانِي وَٱلۡقُرۡءَانَ ٱلۡعَظِيمَ ﴿87﴾

Transliteration: Walaqad ataynaka sabAAan mina almathanee waalqurana alAAatheema

Translation: Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗan da ake maimaita karatunsu da Alƙur'ãni mai girma.

15:88

لَا تَمُدَّنَّ عَيۡنَيۡكَ إِلَىٰ مَا مَتَّعۡنَا بِهِۦٓ أَزۡوَٰجٗا مِّنۡهُمۡ وَلَا تَحۡزَنۡ عَلَيۡهِمۡ وَٱخۡفِضۡ جَنَاحَكَ لِلۡمُؤۡمِنِينَ ﴿88﴾

Transliteration: La tamuddanna AAaynayka ila ma mattaAAna bihi azwajan minhum wala tahzan AAalayhim waikhfid janahaka lilmumineena

Translation: Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni.

15:89

وَقُلۡ إِنِّيٓ أَنَا ٱلنَّذِيرُ ٱلۡمُبِينُ ﴿89﴾

Transliteration: Waqul innee ana alnnatheeru almubeenu

Translation: Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyanan ne."

15:90

كَمَآ أَنزَلۡنَا عَلَى ٱلۡمُقۡتَسِمِينَ ﴿90﴾

Transliteration: Kama anzalna AAala almuqtasimeena

Translation: Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa,

15:91

ٱلَّذِينَ جَعَلُواْ ٱلۡقُرۡءَانَ عِضِينَ ﴿91﴾

Transliteration: Allatheena jaAAaloo alqurana AAideena

Translation: Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi.

15:92

فَوَرَبِّكَ لَنَسۡـَٔلَنَّهُمۡ أَجۡمَعِينَ ﴿92﴾

Transliteration: Fawarabbika lanasalannahum ajmaAAeena

Translation: To, rantsuwa da Ubangijinka! Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya.

15:93

عَمَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ ﴿93﴾

Transliteration: AAamma kanoo yaAAmaloona

Translation: Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa.

15:94

فَٱصۡدَعۡ بِمَا تُؤۡمَرُ وَأَعۡرِضۡ عَنِ ٱلۡمُشۡرِكِينَ ﴿94﴾

Transliteration: FaisdaAA bima tumaru waaAArid AAani almushrikeena

Translation: Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki.

15:95

إِنَّا كَفَيۡنَٰكَ ٱلۡمُسۡتَهۡزِءِينَ ﴿95﴾

Transliteration: Inna kafaynaka almustahzieena

Translation: Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu izgili.

15:96

ٱلَّذِينَ يَجۡعَلُونَ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۚ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ ﴿96﴾

Transliteration: Allatheena yajAAaloona maAAa Allahi ilahan akhara fasawfa yaAAlamoona

Translation: Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani.

15:97

وَلَقَدۡ نَعۡلَمُ أَنَّكَ يَضِيقُ صَدۡرُكَ بِمَا يَقُولُونَ ﴿97﴾

Transliteration: Walaqad naAAlamu annaka yadeequ sadruka bima yaqooloona

Translation: Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili).

15:98

فَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ وَكُن مِّنَ ٱلسَّـٰجِدِينَ ﴿98﴾

Transliteration: Fasabbih bihamdi rabbika wakun mina alssajideena

Translation: Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada.

15:99

وَٱعۡبُدۡ رَبَّكَ حَتَّىٰ يَأۡتِيَكَ ٱلۡيَقِينُ ﴿99﴾

Transliteration: WaoAAbud rabbaka hatta yatiyaka alyaqeenu

Translation: Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka.

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download