quranm◉

Surah Al-Qamar transliteration

◉ Sura · ∞

54:1

ٱقۡتَرَبَتِ ٱلسَّاعَةُ وَٱنشَقَّ ٱلۡقَمَرُ ﴿1﴾

Transliteration: Iqtarabati alssaAAatu wainshaqqa alqamaru

Translation: Sã'a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge.

54:2

وَإِن يَرَوۡاْ ءَايَةٗ يُعۡرِضُواْ وَيَقُولُواْ سِحۡرٞ مُّسۡتَمِرّٞ ﴿2﴾

Transliteration: Wain yaraw ayatan yuAAridoo wayaqooloo sihrun mustamirrun

Translation: Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"

54:3

وَكَذَّبُواْ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَهۡوَآءَهُمۡۚ وَكُلُّ أَمۡرٖ مُّسۡتَقِرّٞ ﴿3﴾

Transliteration: Wakaththaboo waittabaAAoo ahwaahum wakullu amrin mustaqirrun

Translation: Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.

54:4

وَلَقَدۡ جَآءَهُم مِّنَ ٱلۡأَنۢبَآءِ مَا فِيهِ مُزۡدَجَرٌ ﴿4﴾

Transliteration: Walaqad jaahum mina alanbai ma feehi muzdajarun

Translation: Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.

54:5

حِكۡمَةُۢ بَٰلِغَةٞۖ فَمَا تُغۡنِ ٱلنُّذُرُ ﴿5﴾

Transliteration: Hikmatun balighatun fama tughnee alnnuthuru

Translation: Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.

54:6

فَتَوَلَّ عَنۡهُمۡۘ يَوۡمَ يَدۡعُ ٱلدَّاعِ إِلَىٰ شَيۡءٖ نُّكُرٍ ﴿6﴾

Transliteration: Fatawalla AAanhum yawma yadAAu alddaAAi ila shayin nukurin

Translation: Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.

54:7

خُشَّعًا أَبۡصَٰرُهُمۡ يَخۡرُجُونَ مِنَ ٱلۡأَجۡدَاثِ كَأَنَّهُمۡ جَرَادٞ مُّنتَشِرٞ ﴿7﴾

Transliteration: KhushshaAAan absaruhum yakhrujoona mina alajdathi kaannahum jaradun muntashirun

Translation: ¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse.

54:8

مُّهۡطِعِينَ إِلَى ٱلدَّاعِۖ يَقُولُ ٱلۡكَٰفِرُونَ هَٰذَا يَوۡمٌ عَسِرٞ ﴿8﴾

Transliteration: MuhtiAAeena ila alddaAAi yaqoolu alkafiroona hatha yawmun AAasirun

Translation: Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!"

54:9

كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ فَكَذَّبُواْ عَبۡدَنَا وَقَالُواْ مَجۡنُونٞ وَٱزۡدُجِرَ ﴿9﴾

Transliteration: Kaththabat qablahum qawmu noohin fakaththaboo AAabdana waqaloo majnoonun waizdujira

Translation: Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata Bawan Mu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi.

54:10

فَدَعَا رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَغۡلُوبٞ فَٱنتَصِرۡ ﴿10﴾

Transliteration: FadaAAa rabbahu annee maghloobun faintasir

Translation: Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako."

54:11

فَفَتَحۡنَآ أَبۡوَٰبَ ٱلسَّمَآءِ بِمَآءٖ مُّنۡهَمِرٖ ﴿11﴾

Transliteration: Fafatahna abwaba alssamai bimain munhamirin

Translation: Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba.

54:12

وَفَجَّرۡنَا ٱلۡأَرۡضَ عُيُونٗا فَٱلۡتَقَى ٱلۡمَآءُ عَلَىٰٓ أَمۡرٖ قَدۡ قُدِرَ ﴿12﴾

Transliteration: Wafajjarna alarda AAuyoonan failtaqa almao AAala amrin qad qudira

Translation: Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umarni da aka riga aka ƙaddara shi.

54:13

وَحَمَلۡنَٰهُ عَلَىٰ ذَاتِ أَلۡوَٰحٖ وَدُسُرٖ ﴿13﴾

Transliteration: Wahamalnahu AAala thati alwahin wadusurin

Translation: Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi.

54:14

تَجۡرِي بِأَعۡيُنِنَا جَزَآءٗ لِّمَن كَانَ كُفِرَ ﴿14﴾

Transliteration: Tajree biaAAyunina jazaan liman kana kufira

Translation: Tanã gudãna, a kan idãnun Mu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin.

54:15

وَلَقَد تَّرَكۡنَٰهَآ ءَايَةٗ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ ﴿15﴾

Transliteration: Walaqad taraknaha ayatan fahal min muddakirin

Translation: Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni

54:16

فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ ﴿16﴾

Transliteration: Fakayfa kana AAathabee wanuthuri

Translation: To, yãyã azãbã Ta take da gargaɗi Na?

54:17

وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ ﴿17﴾

Transliteration: Walaqad yassarna alqurana lilththikri fahal min muddakirin

Translation: Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

54:18

كَذَّبَتۡ عَادٞ فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ ﴿18﴾

Transliteration: Kaththabat AAadun fakayfa kana AAathabee wanuthuri

Translation: Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗi Na?

54:19

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ رِيحٗا صَرۡصَرٗا فِي يَوۡمِ نَحۡسٖ مُّسۡتَمِرّٖ ﴿19﴾

Transliteration: Inna arsalna AAalayhim reehan sarsaran fee yawmi nahsin mustamirrin

Translation: Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa.

54:20

تَنزِعُ ٱلنَّاسَ كَأَنَّهُمۡ أَعۡجَازُ نَخۡلٖ مُّنقَعِرٖ ﴿20﴾

Transliteration: TanziAAu alnnasa kaannahum aAAjazu nakhlin munqaAAirin

Translation: Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne.

54:21

فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ ﴿21﴾

Transliteration: Fakayfa kana AAathabee wanuthuri

Translation: To, yãya azãbã Ta take da gargaɗi Na?

54:22

وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ ﴿22﴾

Transliteration: Walaqad yassarna alqurana lilththikri fahal min muddakirin

Translation: Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

54:23

كَذَّبَتۡ ثَمُودُ بِٱلنُّذُرِ ﴿23﴾

Transliteration: Kaththabat thamoodu bialnnuthuri

Translation: Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin.

54:24

فَقَالُوٓاْ أَبَشَرٗا مِّنَّا وَٰحِدٗا نَّتَّبِعُهُۥٓ إِنَّآ إِذٗا لَّفِي ضَلَٰلٖ وَسُعُرٍ ﴿24﴾

Transliteration: Faqaloo abasharan minna wahidan nattabiAAuhu inna ithan lafee dalalin wasuAAurin

Translation: Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã.

54:25

أَءُلۡقِيَ ٱلذِّكۡرُ عَلَيۡهِ مِنۢ بَيۡنِنَا بَلۡ هُوَ كَذَّابٌ أَشِرٞ ﴿25﴾

Transliteration: Aolqiya alththikru AAalayhi min baynina bal huwa kaththabun ashirun

Translation: "Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!"

54:26

سَيَعۡلَمُونَ غَدٗا مَّنِ ٱلۡكَذَّابُ ٱلۡأَشِرُ ﴿26﴾

Transliteration: SayaAAlamoona ghadan mani alkaththabu alashiru

Translation: Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan?

54:27

إِنَّا مُرۡسِلُواْ ٱلنَّاقَةِ فِتۡنَةٗ لَّهُمۡ فَٱرۡتَقِبۡهُمۡ وَٱصۡطَبِرۡ ﴿27﴾

Transliteration: Inna mursiloo alnnaqati fitnatan lahum fairtaqibhum waistabir

Translation: Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri.

54:28

وَنَبِّئۡهُمۡ أَنَّ ٱلۡمَآءَ قِسۡمَةُۢ بَيۡنَهُمۡۖ كُلُّ شِرۡبٖ مُّحۡتَضَرٞ ﴿28﴾

Transliteration: Wanabbihum anna almaa qismatun baynahum kullu shirbin muhtadarun

Translation: Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa.

54:29

فَنَادَوۡاْ صَاحِبَهُمۡ فَتَعَاطَىٰ فَعَقَرَ ﴿29﴾

Transliteration: Fanadaw sahibahum fataAAata faAAaqara

Translation: Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta,

54:30

فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ ﴿30﴾

Transliteration: Fakayfa kana AAathabee wanuthuri

Translation: To, yãya azãbaTa take da gargaɗi Na?

54:31

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ فَكَانُواْ كَهَشِيمِ ٱلۡمُحۡتَظِرِ ﴿31﴾

Transliteration: Inna arsalna AAalayhim sayhatan wahidatan fakanoo kahasheemi almuhtathiri

Translation: Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge.

54:32

وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ ﴿32﴾

Transliteration: Walaqad yassarna alqurana lilththikri fahal min muddakirin

Translation: Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

54:33

كَذَّبَتۡ قَوۡمُ لُوطِۭ بِٱلنُّذُرِ ﴿33﴾

Transliteration: Kaththabat qawmu lootin bialnnuthuri

Translation: Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi.

54:34

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ حَاصِبًا إِلَّآ ءَالَ لُوطٖۖ نَّجَّيۡنَٰهُم بِسَحَرٖ ﴿34﴾

Transliteration: Inna arsalna AAalayhim hasiban illa ala lootin najjaynahum bisaharin

Translation: Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba.

54:35

نِّعۡمَةٗ مِّنۡ عِندِنَاۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي مَن شَكَرَ ﴿35﴾

Transliteration: NiAAmatan min AAindina kathalika najzee man shakara

Translation: Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde.

54:36

وَلَقَدۡ أَنذَرَهُم بَطۡشَتَنَا فَتَمَارَوۡاْ بِٱلنُّذُرِ ﴿36﴾

Transliteration: Walaqad antharahum batshatana fatamaraw bialnnuthuri

Translation: Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙar Mu, sai suka yi musu game da gargaɗin.

54:37

وَلَقَدۡ رَٰوَدُوهُ عَن ضَيۡفِهِۦ فَطَمَسۡنَآ أَعۡيُنَهُمۡ فَذُوقُواْ عَذَابِي وَنُذُرِ ﴿37﴾

Transliteration: Walaqad rawadoohu AAan dayfihi fatamasna aAAyunahum fathooqoo AAathabee wanuthuri

Translation: Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩ Na."

54:38

وَلَقَدۡ صَبَّحَهُم بُكۡرَةً عَذَابٞ مُّسۡتَقِرّٞ ﴿38﴾

Transliteration: Walaqad sabbahahum bukratan AAathabun mustaqirrun

Translation: Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe.

54:39

فَذُوقُواْ عَذَابِي وَنُذُرِ ﴿39﴾

Transliteration: Fathooqoo AAathabee wanuthuri

Translation: To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩ Na.

54:40

وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ ﴿40﴾

Transliteration: Walaqad yassarna alqurana lilththikri fahal min muddakirin

Translation: Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa?

54:41

وَلَقَدۡ جَآءَ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ ٱلنُّذُرُ ﴿41﴾

Transliteration: Walaqad jaa ala firAAawna alnnuthuru

Translation: Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna.

54:42

كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا كُلِّهَا فَأَخَذۡنَٰهُمۡ أَخۡذَ عَزِيزٖ مُّقۡتَدِرٍ ﴿42﴾

Transliteration: Kaththaboo biayatina kulliha faakhathnahum akhtha AAazeezin muqtadirin

Translation: Sun ƙaryata game da ãyõyin Mu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi.

54:43

أَكُفَّارُكُمۡ خَيۡرٞ مِّنۡ أُوْلَـٰٓئِكُمۡ أَمۡ لَكُم بَرَآءَةٞ فِي ٱلزُّبُرِ ﴿43﴾

Transliteration: Akuffarukum khayrun min olaikum am lakum baraatun fee alzzuburi

Translation: Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai?

54:44

أَمۡ يَقُولُونَ نَحۡنُ جَمِيعٞ مُّنتَصِرٞ ﴿44﴾

Transliteration: Am yaqooloona nahnu jameeAAun muntasirun

Translation: Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?"

54:45

سَيُهۡزَمُ ٱلۡجَمۡعُ وَيُوَلُّونَ ٱلدُّبُرَ ﴿45﴾

Transliteration: Sayuhzamu aljamAAu wayuwalloona alddubura

Translation: Zã a karya tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu.

54:46

بَلِ ٱلسَّاعَةُ مَوۡعِدُهُمۡ وَٱلسَّاعَةُ أَدۡهَىٰ وَأَمَرُّ ﴿46﴾

Transliteration: Bali alssaAAatu mawAAiduhum waalssaAAatu adha waamarru

Translation: Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci.

54:47

إِنَّ ٱلۡمُجۡرِمِينَ فِي ضَلَٰلٖ وَسُعُرٖ ﴿47﴾

Transliteration: Inna almujrimeena fee dalalin wasuAAurin

Translation: Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka.

54:48

يَوۡمَ يُسۡحَبُونَ فِي ٱلنَّارِ عَلَىٰ وُجُوهِهِمۡ ذُوقُواْ مَسَّ سَقَرَ ﴿48﴾

Transliteration: Yawma yushaboona fee alnnari AAala wujoohihim thooqoo massa saqara

Translation: Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar."

54:49

إِنَّا كُلَّ شَيۡءٍ خَلَقۡنَٰهُ بِقَدَرٖ ﴿49﴾

Transliteration: Inna kulla shayin khalaqnahu biqadarin

Translation: Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri.

54:50

وَمَآ أَمۡرُنَآ إِلَّا وَٰحِدَةٞ كَلَمۡحِۭ بِٱلۡبَصَرِ ﴿50﴾

Transliteration: Wama amruna illa wahidatun kalamhin bialbasari

Translation: Kuma umurnin Mu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.

54:51

وَلَقَدۡ أَهۡلَكۡنَآ أَشۡيَاعَكُمۡ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ ﴿51﴾

Transliteration: Walaqad ahlakna ashyaAAakum fahal min muddakirin

Translation: Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?

54:52

وَكُلُّ شَيۡءٖ فَعَلُوهُ فِي ٱلزُّبُرِ ﴿52﴾

Transliteration: Wakullu shayin faAAaloohu fee alzzuburi

Translation: Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.

54:53

وَكُلُّ صَغِيرٖ وَكَبِيرٖ مُّسۡتَطَرٌ ﴿53﴾

Transliteration: Wakullu sagheerin wakabeerin mustatarun

Translation: Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.

54:54

إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّـٰتٖ وَنَهَرٖ ﴿54﴾

Transliteration: Inna almuttaqeena fee jannatin wanaharin

Translation: Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.

54:55

فِي مَقۡعَدِ صِدۡقٍ عِندَ مَلِيكٖ مُّقۡتَدِرِۭ ﴿55﴾

Transliteration: Fee maqAAadi sidqin AAinda maleekin muqtadirin

Translation: A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download