quranm◉

Surah Al-Ma'arij transliteration

◉ Sura · ∞

70:1

سَأَلَ سَآئِلُۢ بِعَذَابٖ وَاقِعٖ ﴿1﴾

Transliteration: Saala sailun biAAathabin waqiAAin

Translation: Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa.

70:2

لِّلۡكَٰفِرِينَ لَيۡسَ لَهُۥ دَافِعٞ ﴿2﴾

Transliteration: Lilkafireena laysa lahu dafiAAun

Translation: Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa.

70:3

مِّنَ ٱللَّهِ ذِي ٱلۡمَعَارِجِ ﴿3﴾

Transliteration: Mina Allahi thee almaAAariji

Translation: Daga Allah Mai matãkala.

70:4

تَعۡرُجُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ إِلَيۡهِ فِي يَوۡمٖ كَانَ مِقۡدَارُهُۥ خَمۡسِينَ أَلۡفَ سَنَةٖ ﴿4﴾

Transliteration: TaAAruju almalaikatu waalrroohu ilayhi fee yawmin kana miqdaruhu khamseena alfa sanatin

Translation: Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne.

70:5

فَٱصۡبِرۡ صَبۡرٗا جَمِيلًا ﴿5﴾

Transliteration: Faisbir sabran jameelan

Translation: Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo.

70:6

إِنَّهُمۡ يَرَوۡنَهُۥ بَعِيدٗا ﴿6﴾

Transliteration: Innahum yarawnahu baAAeedan

Translation: Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa.

70:7

وَنَرَىٰهُ قَرِيبٗا ﴿7﴾

Transliteration: Wanarahu qareeban

Translation: Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa.

70:8

يَوۡمَ تَكُونُ ٱلسَّمَآءُ كَٱلۡمُهۡلِ ﴿8﴾

Transliteration: Yawma takoonu alssamao kaalmuhli

Translation: Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa.

70:9

وَتَكُونُ ٱلۡجِبَالُ كَٱلۡعِهۡنِ ﴿9﴾

Transliteration: Watakoonu aljibalu kaalAAihni

Translation: Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi.

70:10

وَلَا يَسۡـَٔلُ حَمِيمٌ حَمِيمٗا ﴿10﴾

Transliteration: Wala yasalu hameemun hameeman

Translation: Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake.

70:11

يُبَصَّرُونَهُمۡۚ يَوَدُّ ٱلۡمُجۡرِمُ لَوۡ يَفۡتَدِي مِنۡ عَذَابِ يَوۡمِئِذِۭ بِبَنِيهِ ﴿11﴾

Transliteration: Yubassaroonahum yawaddu almujrimu law yaftadee min AAathabi yawmiithin bibaneehi

Translation: Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa,

70:12

وَصَٰحِبَتِهِۦ وَأَخِيهِ ﴿12﴾

Transliteration: Wasahibatihi waakheehi

Translation: Da matarsa da ɗan'uwansa.

70:13

وَفَصِيلَتِهِ ٱلَّتِي تُـٔۡوِيهِ ﴿13﴾

Transliteration: Wafaseelatihi allatee tuweehi

Translation: Da danginsa, mãsu tattarã shi.

70:14

وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا ثُمَّ يُنجِيهِ ﴿14﴾

Transliteration: Waman fee alardi jameeAAan thumma yunjeehi

Translation: Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi.

70:15

كَلَّآۖ إِنَّهَا لَظَىٰ ﴿15﴾

Transliteration: Kalla innaha latha

Translation: A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã,

70:16

نَزَّاعَةٗ لِّلشَّوَىٰ ﴿16﴾

Transliteration: NazzaAAatan lilshshawa

Translation: Mai twãle fãtar goshi.

70:17

تَدۡعُواْ مَنۡ أَدۡبَرَ وَتَوَلَّىٰ ﴿17﴾

Transliteration: TadAAoo man adbara watawalla

Translation: Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai.

70:18

وَجَمَعَ فَأَوۡعَىٰٓ ﴿18﴾

Transliteration: WajamaAAa faawAAa

Translation: Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka.

70:19

إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ خُلِقَ هَلُوعًا ﴿19﴾

Transliteration: Inna alinsana khuliqa halooAAan

Translation: Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi.

70:20

إِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ جَزُوعٗا ﴿20﴾

Transliteration: Itha massahu alshsharru jazooAAan

Translation: Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri.

70:21

وَإِذَا مَسَّهُ ٱلۡخَيۡرُ مَنُوعًا ﴿21﴾

Transliteration: Waitha massahu alkhayru manooAAan

Translation: Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa.

70:22

إِلَّا ٱلۡمُصَلِّينَ ﴿22﴾

Transliteration: Illa almusalleena

Translation: Sai mãsu yin salla,

70:23

ٱلَّذِينَ هُمۡ عَلَىٰ صَلَاتِهِمۡ دَآئِمُونَ ﴿23﴾

Transliteration: Allatheena hum AAala salatihim daimoona

Translation: Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne.

70:24

وَٱلَّذِينَ فِيٓ أَمۡوَٰلِهِمۡ حَقّٞ مَّعۡلُومٞ ﴿24﴾

Transliteration: Waallatheena fee amwalihim haqqun maAAloomun

Translation: Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne.

70:25

لِّلسَّآئِلِ وَٱلۡمَحۡرُومِ ﴿25﴾

Transliteration: Lilssaili waalmahroomi

Translation: Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon.

70:26

وَٱلَّذِينَ يُصَدِّقُونَ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ ﴿26﴾

Transliteration: Waallatheena yusaddiqoona biyawmi alddeeni

Translation: Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako.

70:27

وَٱلَّذِينَ هُم مِّنۡ عَذَابِ رَبِّهِم مُّشۡفِقُونَ ﴿27﴾

Transliteration: Waallatheena hum min AAathabi rabbihim mushfiqoona

Translation: Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro.

70:28

إِنَّ عَذَابَ رَبِّهِمۡ غَيۡرُ مَأۡمُونٖ ﴿28﴾

Transliteration: Inna AAathaba rabbihim ghayru mamoonin

Translation: Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce.

70:29

وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِفُرُوجِهِمۡ حَٰفِظُونَ ﴿29﴾

Transliteration: Waallatheena hum lifuroojihim hafithoona

Translation: Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne.

70:30

إِلَّا عَلَىٰٓ أَزۡوَٰجِهِمۡ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ فَإِنَّهُمۡ غَيۡرُ مَلُومِينَ ﴿30﴾

Transliteration: Illa AAala azwajihim aw ma malakat aymanuhum fainnahum ghayru maloomeena

Translation: Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne.

70:31

فَمَنِ ٱبۡتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡعَادُونَ ﴿31﴾

Transliteration: Famani ibtagha waraa thalika faolaika humu alAAadoona

Translation: To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka.

70:32

وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِأَمَٰنَٰتِهِمۡ وَعَهۡدِهِمۡ رَٰعُونَ ﴿32﴾

Transliteration: Waallatheena hum liamanatihim waAAahdihim raAAoona

Translation: Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne.

70:33

وَٱلَّذِينَ هُم بِشَهَٰدَٰتِهِمۡ قَآئِمُونَ ﴿33﴾

Transliteration: Waallatheena hum bishahadatihim qaimoona

Translation: Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne.

70:34

وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَلَىٰ صَلَاتِهِمۡ يُحَافِظُونَ ﴿34﴾

Transliteration: Waallatheena hum AAala salatihim yuhafithoona

Translation: Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne.

70:35

أُوْلَـٰٓئِكَ فِي جَنَّـٰتٖ مُّكۡرَمُونَ ﴿35﴾

Transliteration: Olaika fee jannatin mukramoona

Translation: Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne

70:36

فَمَالِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ قِبَلَكَ مُهۡطِعِينَ ﴿36﴾

Transliteration: Famali allatheena kafaroo qibalaka muhtiAAeena

Translation: Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu).

70:37

عَنِ ٱلۡيَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ عِزِينَ ﴿37﴾

Transliteration: AAani alyameeni waAAani alshshimali AAizeena

Translation: Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a!

70:38

أَيَطۡمَعُ كُلُّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ أَن يُدۡخَلَ جَنَّةَ نَعِيمٖ ﴿38﴾

Transliteration: AyatmaAAu kullu imriin minhum an yudkhala jannata naAAeemin

Translation: Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)?

70:39

كَلَّآۖ إِنَّا خَلَقۡنَٰهُم مِّمَّا يَعۡلَمُونَ ﴿39﴾

Transliteration: Kalla inna khalaqnahum mimma yaAAlamoona

Translation: A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani.

70:40

فَلَآ أُقۡسِمُ بِرَبِّ ٱلۡمَشَٰرِقِ وَٱلۡمَغَٰرِبِ إِنَّا لَقَٰدِرُونَ ﴿40﴾

Transliteration: Fala oqsimu birabbi almashariqi waalmagharibi inna laqadiroona

Translation: Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne.

70:41

عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ خَيۡرٗا مِّنۡهُمۡ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ ﴿41﴾

Transliteration: AAala an nubaddila khayran minhum wama nahnu bimasbooqeena

Translation: Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba.

70:42

فَذَرۡهُمۡ يَخُوضُواْ وَيَلۡعَبُواْ حَتَّىٰ يُلَٰقُواْ يَوۡمَهُمُ ٱلَّذِي يُوعَدُونَ ﴿42﴾

Transliteration: Fatharhum yakhoodoo wayalAAaboo hatta yulaqoo yawmahumu allathee yooAAadoona

Translation: Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita).

70:43

يَوۡمَ يَخۡرُجُونَ مِنَ ٱلۡأَجۡدَاثِ سِرَاعٗا كَأَنَّهُمۡ إِلَىٰ نُصُبٖ يُوفِضُونَ ﴿43﴾

Transliteration: Yawma yakhrujoona mina alajdathi siraAAan kaannahum ila nusubin yoofidoona

Translation: Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa.

70:44

خَٰشِعَةً أَبۡصَٰرُهُمۡ تَرۡهَقُهُمۡ ذِلَّةٞۚ ذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمُ ٱلَّذِي كَانُواْ يُوعَدُونَ ﴿44﴾

Transliteration: KhashiAAatan absaruhum tarhaquhum thillatun thalika alyawmu allathee kanoo yooAAadoona

Translation: Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.)

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download