quranm◉

Surah Ad-Dukhan transliteration

◉ Sura · ∞

44:1

حمٓ ﴿1﴾

Transliteration: Hameem

Translation: Ḥ. M̃.

44:2

وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ ﴿2﴾

Transliteration: Waalkitabi almubeeni

Translation: Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.

44:3

إِنَّآ أَنزَلۡنَٰهُ فِي لَيۡلَةٖ مُّبَٰرَكَةٍۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ ﴿3﴾

Transliteration: Inna anzalnahu fee laylatin mubarakatin inna kunna munthireena

Translation: Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.

44:4

فِيهَا يُفۡرَقُ كُلُّ أَمۡرٍ حَكِيمٍ ﴿4﴾

Transliteration: Feeha yufraqu kullu amrin hakeemin

Translation: A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.

44:5

أَمۡرٗا مِّنۡ عِندِنَآۚ إِنَّا كُنَّا مُرۡسِلِينَ ﴿5﴾

Transliteration: Amran min AAindina inna kunna mursileena

Translation: Umurni na daga wurin Mu. Lalle Mũ ne Muka kasance Mãsu aikãwã.

44:6

رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ ﴿6﴾

Transliteration: Rahmatan min rabbika innahu huwa alssameeAAu alAAaleemu

Translation: Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.

44:7

رَبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَآۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ ﴿7﴾

Transliteration: Rabbi alssamawati waalardi wama baynahuma in kuntum mooqineena

Translation: (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).

44:8

لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ رَبُّكُمۡ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ ﴿8﴾

Transliteration: La ilaha illa huwa yuhyee wayumeetu rabbukum warabbu abaikumu alawwaleena

Translation: Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.

44:9

بَلۡ هُمۡ فِي شَكّٖ يَلۡعَبُونَ ﴿9﴾

Transliteration: Bal hum fee shakkin yalAAaboona

Translation: A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.

44:10

فَٱرۡتَقِبۡ يَوۡمَ تَأۡتِي ٱلسَّمَآءُ بِدُخَانٖ مُّبِينٖ ﴿10﴾

Transliteration: Fairtaqib yawma tatee alssamao bidukhanin mubeenin

Translation: Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.

44:11

يَغۡشَى ٱلنَّاسَۖ هَٰذَا عَذَابٌ أَلِيمٞ ﴿11﴾

Transliteration: Yaghsha alnnasa hatha AAathabun aleemun

Translation: Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.

44:12

رَّبَّنَا ٱكۡشِفۡ عَنَّا ٱلۡعَذَابَ إِنَّا مُؤۡمِنُونَ ﴿12﴾

Transliteration: Rabbana ikshif AAanna alAAathaba inna muminoona

Translation: Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.

44:13

أَنَّىٰ لَهُمُ ٱلذِّكۡرَىٰ وَقَدۡ جَآءَهُمۡ رَسُولٞ مُّبِينٞ ﴿13﴾

Transliteration: Anna lahumu alththikra waqad jaahum rasoolun mubeenun

Translation: Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?

44:14

ثُمَّ تَوَلَّوۡاْ عَنۡهُ وَقَالُواْ مُعَلَّمٞ مَّجۡنُونٌ ﴿14﴾

Transliteration: Thumma tawallaw AAanhu waqaloo muAAallamun majnoonun

Translation: Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci."

44:15

إِنَّا كَاشِفُواْ ٱلۡعَذَابِ قَلِيلًاۚ إِنَّكُمۡ عَآئِدُونَ ﴿15﴾

Transliteration: Inna kashifoo alAAathabi qaleelan innakum AAaidoona

Translation: Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).

44:16

يَوۡمَ نَبۡطِشُ ٱلۡبَطۡشَةَ ٱلۡكُبۡرَىٰٓ إِنَّا مُنتَقِمُونَ ﴿16﴾

Transliteration: Yawma nabtishu albatshata alkubra inna muntaqimoona

Translation: Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.

44:17

وَلَقَدۡ فَتَنَّا قَبۡلَهُمۡ قَوۡمَ فِرۡعَوۡنَ وَجَآءَهُمۡ رَسُولٞ كَرِيمٌ ﴿17﴾

Transliteration: Walaqad fatanna qablahum qawma firAAawna wajaahum rasoolun kareemun

Translation: Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.

44:18

أَنۡ أَدُّوٓاْ إِلَيَّ عِبَادَ ٱللَّهِۖ إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ ﴿18﴾

Transliteration: An addoo ilayya AAibada Allahi innee lakum rasoolun ameenun

Translation: (Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."

44:19

وَأَن لَّا تَعۡلُواْ عَلَى ٱللَّهِۖ إِنِّيٓ ءَاتِيكُم بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ ﴿19﴾

Transliteration: Waan la taAAloo AAala Allahi innee ateekum bisultanin mubeenin

Translation: "Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne."

44:20

وَإِنِّي عُذۡتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمۡ أَن تَرۡجُمُونِ ﴿20﴾

Transliteration: Wainnee AAuthtu birabbee warabbikum an tarjumooni

Translation: "Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni."

44:21

وَإِن لَّمۡ تُؤۡمِنُواْ لِي فَٱعۡتَزِلُونِ ﴿21﴾

Transliteration: Wain lam tuminoo lee faiAAtazilooni

Translation: "Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."

44:22

فَدَعَا رَبَّهُۥٓ أَنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ قَوۡمٞ مُّجۡرِمُونَ ﴿22﴾

Transliteration: FadaAAa rabbahu anna haolai qawmun mujrimoona

Translation: Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.

44:23

فَأَسۡرِ بِعِبَادِي لَيۡلًا إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ ﴿23﴾

Transliteration: Faasri biAAibadee laylan innakum muttabaAAoona

Translation: (Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)"

44:24

وَٱتۡرُكِ ٱلۡبَحۡرَ رَهۡوًاۖ إِنَّهُمۡ جُندٞ مُّغۡرَقُونَ ﴿24﴾

Transliteration: Waotruki albahra rahwan innahum jundun mughraqoona

Translation: "Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."

44:25

كَمۡ تَرَكُواْ مِن جَنَّـٰتٖ وَعُيُونٖ ﴿25﴾

Transliteration: Kam tarakoo min jannatin waAAuyoonin

Translation: Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari.

44:26

وَزُرُوعٖ وَمَقَامٖ كَرِيمٖ ﴿26﴾

Transliteration: WazurooAAin wamaqamin kareemin

Translation: Da shuke-shuke da matsayi mai kyau.

44:27

وَنَعۡمَةٖ كَانُواْ فِيهَا فَٰكِهِينَ ﴿27﴾

Transliteration: WanaAAmatin kanoo feeha fakiheena

Translation: Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.

44:28

كَذَٰلِكَۖ وَأَوۡرَثۡنَٰهَا قَوۡمًا ءَاخَرِينَ ﴿28﴾

Transliteration: Kathalika waawrathnaha qawman akhareena

Translation: Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.

44:29

فَمَا بَكَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلسَّمَآءُ وَٱلۡأَرۡضُ وَمَا كَانُواْ مُنظَرِينَ ﴿29﴾

Transliteration: Fama bakat AAalayhimu alssamao waalardu wama kanoo munthareena

Translation: Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.

44:30

وَلَقَدۡ نَجَّيۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ مِنَ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡمُهِينِ ﴿30﴾

Transliteration: Walaqad najjayna banee israeela mina alAAathabi almuheeni

Translation: Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.

44:31

مِن فِرۡعَوۡنَۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَالِيٗا مِّنَ ٱلۡمُسۡرِفِينَ ﴿31﴾

Transliteration: Min firAAawna innahu kana AAaliyan mina almusrifeena

Translation: Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.

44:32

وَلَقَدِ ٱخۡتَرۡنَٰهُمۡ عَلَىٰ عِلۡمٍ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ ﴿32﴾

Transliteration: Walaqadi ikhtarnahum AAala AAilmin AAala alAAalameena

Translation: Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne.

44:33

وَءَاتَيۡنَٰهُم مِّنَ ٱلۡأٓيَٰتِ مَا فِيهِ بَلَـٰٓؤٞاْ مُّبِينٌ ﴿33﴾

Transliteration: Waataynahum mina alayati ma feehi balaon mubeenun

Translation: Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna

44:34

إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ لَيَقُولُونَ ﴿34﴾

Transliteration: Inna haolai layaqooloona

Translation: Lalle waɗannan mutãne, haƙĩka, sunã cẽwa,

44:35

إِنۡ هِيَ إِلَّا مَوۡتَتُنَا ٱلۡأُولَىٰ وَمَا نَحۡنُ بِمُنشَرِينَ ﴿35﴾

Transliteration: In hiya illa mawtatuna aloola wama nahnu bimunshareena

Translation: "Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."

44:36

فَأۡتُواْ بِـَٔابَآئِنَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ ﴿36﴾

Transliteration: Fatoo biabaina in kuntum sadiqeena

Translation: "Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."

44:37

أَهُمۡ خَيۡرٌ أَمۡ قَوۡمُ تُبَّعٖ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ أَهۡلَكۡنَٰهُمۡۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ مُجۡرِمِينَ ﴿37﴾

Transliteration: Ahum khayrun am qawmu tubbaAAin waallatheena min qablihim ahlaknahum innahum kanoo mujrimeena

Translation: shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.

44:38

وَمَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَا لَٰعِبِينَ ﴿38﴾

Transliteration: Wama khalaqna alssamawati waalarda wama baynahuma laAAibeena

Translation: Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.

44:39

مَا خَلَقۡنَٰهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ ﴿39﴾

Transliteration: Ma khalaqnahuma illa bialhaqqi walakinna aktharahum la yaAAlamoona

Translation: Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.

44:40

إِنَّ يَوۡمَ ٱلۡفَصۡلِ مِيقَٰتُهُمۡ أَجۡمَعِينَ ﴿40﴾

Transliteration: Inna yawma alfasli meeqatuhum ajmaAAeena

Translation: Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya.

44:41

يَوۡمَ لَا يُغۡنِي مَوۡلًى عَن مَّوۡلٗى شَيۡـٔٗا وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ ﴿41﴾

Transliteration: Yawma la yughnee mawlan AAan mawlan shayan wala hum yunsaroona

Translation: Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.

44:42

إِلَّا مَن رَّحِمَ ٱللَّهُۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ ﴿42﴾

Transliteration: Illa man rahima Allahu innahu huwa alAAazeezu alrraheemu

Translation: fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.

44:43

إِنَّ شَجَرَتَ ٱلزَّقُّومِ ﴿43﴾

Transliteration: Inna shajarata alzzaqqoomi

Translation: Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),

44:44

طَعَامُ ٱلۡأَثِيمِ ﴿44﴾

Transliteration: TaAAamu alatheemi

Translation: Ita ce abincin mai laifi.

44:45

كَٱلۡمُهۡلِ يَغۡلِي فِي ٱلۡبُطُونِ ﴿45﴾

Transliteration: Kaalmuhli yaghlee fee albutooni

Translation: Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.

44:46

كَغَلۡيِ ٱلۡحَمِيمِ ﴿46﴾

Transliteration: Kaghalyi alhameemi

Translation: Kamar tafasar ruwan zãfi.

44:47

خُذُوهُ فَٱعۡتِلُوهُ إِلَىٰ سَوَآءِ ٱلۡجَحِيمِ ﴿47﴾

Transliteration: Khuthoohu faiAAtiloohu ila sawai aljaheemi

Translation: (A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm."

44:48

ثُمَّ صُبُّواْ فَوۡقَ رَأۡسِهِۦ مِنۡ عَذَابِ ٱلۡحَمِيمِ ﴿48﴾

Transliteration: Thumma subboo fawqa rasihi min AAathabi alhameemi

Translation: "Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi."

44:49

ذُقۡ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡكَرِيمُ ﴿49﴾

Transliteration: Thuq innaka anta alAAazeezu alkareemu

Translation: (A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!"

44:50

إِنَّ هَٰذَا مَا كُنتُم بِهِۦ تَمۡتَرُونَ ﴿50﴾

Transliteration: Inna hatha ma kuntum bihi tamtaroona

Translation: "Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi."

44:51

إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِينٖ ﴿51﴾

Transliteration: Inna almuttaqeena fee maqamin ameenin

Translation: Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.

44:52

فِي جَنَّـٰتٖ وَعُيُونٖ ﴿52﴾

Transliteration: Fee jannatin waAAuyoonin

Translation: A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari.

44:53

يَلۡبَسُونَ مِن سُندُسٖ وَإِسۡتَبۡرَقٖ مُّتَقَٰبِلِينَ ﴿53﴾

Transliteration: Yalbasoona min sundusin waistabraqin mutaqabileena

Translation: Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.

44:54

كَذَٰلِكَ وَزَوَّجۡنَٰهُم بِحُورٍ عِينٖ ﴿54﴾

Transliteration: Kathalika wazawwajnahum bihoorin AAeenin

Translation: Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyawun idãnu, mãsu girmansu.

44:55

يَدۡعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَٰكِهَةٍ ءَامِنِينَ ﴿55﴾

Transliteration: YadAAoona feeha bikulli fakihatin amineena

Translation: Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro).

44:56

لَا يَذُوقُونَ فِيهَا ٱلۡمَوۡتَ إِلَّا ٱلۡمَوۡتَةَ ٱلۡأُولَىٰۖ وَوَقَىٰهُمۡ عَذَابَ ٱلۡجَحِيمِ ﴿56﴾

Transliteration: La yathooqoona feeha almawta illa almawtata aloola wawaqahum AAathaba aljaheemi

Translation: Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm.

44:57

فَضۡلٗا مِّن رَّبِّكَۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ ﴿57﴾

Transliteration: Fadlan min rabbika thalika huwa alfawzu alAAatheemu

Translation: Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.

44:58

فَإِنَّمَا يَسَّرۡنَٰهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ ﴿58﴾

Transliteration: Fainnama yassarnahu bilisanika laAAallahum yatathakkaroona

Translation: Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.

44:59

فَٱرۡتَقِبۡ إِنَّهُم مُّرۡتَقِبُونَ ﴿59﴾

Transliteration: Fairtaqib innahum murtaqiboona

Translation: Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download