quranm◉

Surah Adh-Dhariyat transliteration

◉ Sura · ∞

51:1

وَٱلذَّـٰرِيَٰتِ ذَرۡوٗا ﴿1﴾

Transliteration: Waalththariyati tharwan

Translation: Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa.

51:2

فَٱلۡحَٰمِلَٰتِ وِقۡرٗا ﴿2﴾

Transliteration: Faalhamilati wiqran

Translation: Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa).

51:3

فَٱلۡجَٰرِيَٰتِ يُسۡرٗا ﴿3﴾

Transliteration: Faaljariyati yusran

Translation: Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi.

51:4

فَٱلۡمُقَسِّمَٰتِ أَمۡرًا ﴿4﴾

Transliteration: Faalmuqassimati amran

Translation: Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah).

51:5

إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَصَادِقٞ ﴿5﴾

Transliteration: Innama tooAAadoona lasadiqun

Translation: Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne.

51:6

وَإِنَّ ٱلدِّينَ لَوَٰقِعٞ ﴿6﴾

Transliteration: Wainna alddeena lawaqiAAun

Translation: Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne

51:7

وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلۡحُبُكِ ﴿7﴾

Transliteration: Waalssamai thati alhubuki

Translation: Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo).

51:8

إِنَّكُمۡ لَفِي قَوۡلٖ مُّخۡتَلِفٖ ﴿8﴾

Transliteration: Innakum lafee qawlin mukhtalifin

Translation: Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani).

51:9

يُؤۡفَكُ عَنۡهُ مَنۡ أُفِكَ ﴿9﴾

Transliteration: Yufaku AAanhu man ofika

Translation: Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya).

51:10

قُتِلَ ٱلۡخَرَّـٰصُونَ ﴿10﴾

Transliteration: Qutila alkharrasoona

Translation: An la'ani mãsu ƙiri-faɗi.

51:11

ٱلَّذِينَ هُمۡ فِي غَمۡرَةٖ سَاهُونَ ﴿11﴾

Transliteration: Allatheena hum fee ghamratin sahoona

Translation: Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci.

51:12

يَسۡـَٔلُونَ أَيَّانَ يَوۡمُ ٱلدِّينِ ﴿12﴾

Transliteration: Yasaloona ayyana yawmu alddeeni

Translation: Sunã tambaya: "Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?"

51:13

يَوۡمَ هُمۡ عَلَى ٱلنَّارِ يُفۡتَنُونَ ﴿13﴾

Transliteration: Yawma hum AAala alnnari yuftanoona

Translation: Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su.

51:14

ذُوقُواْ فِتۡنَتَكُمۡ هَٰذَا ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تَسۡتَعۡجِلُونَ ﴿14﴾

Transliteration: Thooqoo fitnatakum hatha allathee kuntum bihi tastaAAjiloona

Translation: (A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa."

51:15

إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّـٰتٖ وَعُيُونٍ ﴿15﴾

Transliteration: Inna almuttaqeena fee jannatin waAAuyoonin

Translation: Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari.

51:16

ءَاخِذِينَ مَآ ءَاتَىٰهُمۡ رَبُّهُمۡۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَبۡلَ ذَٰلِكَ مُحۡسِنِينَ ﴿16﴾

Transliteration: Akhitheena ma atahum rabbuhum innahum kanoo qabla thalika muhsineena

Translation: Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya).

51:17

كَانُواْ قَلِيلٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِ مَا يَهۡجَعُونَ ﴿17﴾

Transliteration: Kanoo qaleelan mina allayli ma yahjaAAoona

Translation: Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci.

51:18

وَبِٱلۡأَسۡحَارِ هُمۡ يَسۡتَغۡفِرُونَ ﴿18﴾

Transliteration: Wabialashari hum yastaghfiroona

Translation: Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri.

51:19

وَفِيٓ أَمۡوَٰلِهِمۡ حَقّٞ لِّلسَّآئِلِ وَٱلۡمَحۡرُومِ ﴿19﴾

Transliteration: Wafee amwalihim haqqun lilssaili waalmahroomi

Translation: Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo.

51:20

وَفِي ٱلۡأَرۡضِ ءَايَٰتٞ لِّلۡمُوقِنِينَ ﴿20﴾

Transliteration: Wafee alardi ayatun lilmooqineena

Translation: Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni.

51:21

وَفِيٓ أَنفُسِكُمۡۚ أَفَلَا تُبۡصِرُونَ ﴿21﴾

Transliteration: Wafee anfusikum afala tubsiroona

Translation: Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba?

51:22

وَفِي ٱلسَّمَآءِ رِزۡقُكُمۡ وَمَا تُوعَدُونَ ﴿22﴾

Transliteration: Wafee alssamai rizqukum wama tooAAadoona

Translation: Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari.

51:23

فَوَرَبِّ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ إِنَّهُۥ لَحَقّٞ مِّثۡلَ مَآ أَنَّكُمۡ تَنطِقُونَ ﴿23﴾

Transliteration: Fawarabbi alssamai waalardi innahu lahaqqun mithla ma annakum tantiqoona

Translation: To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana,

51:24

هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ضَيۡفِ إِبۡرَٰهِيمَ ٱلۡمُكۡرَمِينَ ﴿24﴾

Transliteration: Hal ataka hadeethu dayfi ibraheema almukrameena

Translation: Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka?

51:25

إِذۡ دَخَلُواْ عَلَيۡهِ فَقَالُواْ سَلَٰمٗاۖ قَالَ سَلَٰمٞ قَوۡمٞ مُّنكَرُونَ ﴿25﴾

Transliteration: Ith dakhaloo AAalayhi faqaloo salaman qala salamun qawmun munkaroona

Translation: A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!"

51:26

فَرَاغَ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ فَجَآءَ بِعِجۡلٖ سَمِينٖ ﴿26﴾

Transliteration: Faragha ila ahlihi fajaa biAAijlin sameenin

Translation: Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna,

51:27

فَقَرَّبَهُۥٓ إِلَيۡهِمۡ قَالَ أَلَا تَأۡكُلُونَ ﴿27﴾

Transliteration: Faqarrabahu ilayhim qala ala takuloona

Translation: Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bã zã ku ci ba?"

51:28

فَأَوۡجَسَ مِنۡهُمۡ خِيفَةٗۖ قَالُواْ لَا تَخَفۡۖ وَبَشَّرُوهُ بِغُلَٰمٍ عَلِيمٖ ﴿28﴾

Transliteration: Faawjasa minhum kheefatan qaloo la takhaf wabashsharoohu bighulamin AAaleemin

Translation: Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro." Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi.

51:29

فَأَقۡبَلَتِ ٱمۡرَأَتُهُۥ فِي صَرَّةٖ فَصَكَّتۡ وَجۡهَهَا وَقَالَتۡ عَجُوزٌ عَقِيمٞ ﴿29﴾

Transliteration: Faaqbalati imraatuhu fee sarratin fasakkat wajhaha waqalat AAajoozun AAaqeemun

Translation: Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!"

51:30

قَالُواْ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡعَلِيمُ ﴿30﴾

Transliteration: Qaloo kathaliki qala rabbuki innahu huwa alhakeemu alAAaleemu

Translation: Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi."

51:31

قَالَ فَمَا خَطۡبُكُمۡ أَيُّهَا ٱلۡمُرۡسَلُونَ ﴿31﴾

Transliteration: Qala fama khatbukum ayyuha almursaloona

Translation: (Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!"

51:32

قَالُوٓاْ إِنَّآ أُرۡسِلۡنَآ إِلَىٰ قَوۡمٖ مُّجۡرِمِينَ ﴿32﴾

Transliteration: Qaloo inna orsilna ila qawmin mujrimeena

Translation: Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi.

51:33

لِنُرۡسِلَ عَلَيۡهِمۡ حِجَارَةٗ مِّن طِينٖ ﴿33﴾

Transliteration: Linursila AAalayhim hijaratan min teenin

Translation: "Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom).

51:34

مُّسَوَّمَةً عِندَ رَبِّكَ لِلۡمُسۡرِفِينَ ﴿34﴾

Transliteration: Musawwamatan AAinda rabbika lilmusrifeena

Translation: "Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna."

51:35

فَأَخۡرَجۡنَا مَن كَانَ فِيهَا مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ﴿35﴾

Transliteration: Faakhrajna man kana feeha mina almumineena

Translation: Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai.

51:36

فَمَا وَجَدۡنَا فِيهَا غَيۡرَ بَيۡتٖ مِّنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ ﴿36﴾

Transliteration: Fama wajadna feeha ghayra baytin mina almuslimeena

Translation: Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi.

51:37

وَتَرَكۡنَا فِيهَآ ءَايَةٗ لِّلَّذِينَ يَخَافُونَ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَلِيمَ ﴿37﴾

Transliteration: Watarakna feeha ayatan lillatheena yakhafoona alAAathaba alaleema

Translation: Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi.

51:38

وَفِي مُوسَىٰٓ إِذۡ أَرۡسَلۡنَٰهُ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ ﴿38﴾

Transliteration: Wafee moosa ith arsalnahu ila firAAawna bisultanin mubeenin

Translation: Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne.

51:39

فَتَوَلَّىٰ بِرُكۡنِهِۦ وَقَالَ سَٰحِرٌ أَوۡ مَجۡنُونٞ ﴿39﴾

Transliteration: Fatawalla biruknihi waqala sahirun aw majnoonun

Translation: Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!"

51:40

فَأَخَذۡنَٰهُ وَجُنُودَهُۥ فَنَبَذۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡيَمِّ وَهُوَ مُلِيمٞ ﴿40﴾

Transliteration: Faakhathnahu wajunoodahu fanabathnahum fee alyammi wahuwa muleemun

Translation: Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.

51:41

وَفِي عَادٍ إِذۡ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلرِّيحَ ٱلۡعَقِيمَ ﴿41﴾

Transliteration: Wafee AAadin ith arsalna AAalayhimu alrreeha alAAaqeema

Translation: Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu.

51:42

مَا تَذَرُ مِن شَيۡءٍ أَتَتۡ عَلَيۡهِ إِلَّا جَعَلَتۡهُ كَٱلرَّمِيمِ ﴿42﴾

Transliteration: Ma tatharu min shayin atat AAalayhi illa jaAAalathu kaalrrameemi

Translation: Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa.

51:43

وَفِي ثَمُودَ إِذۡ قِيلَ لَهُمۡ تَمَتَّعُواْ حَتَّىٰ حِينٖ ﴿43﴾

Transliteration: Wafee thamooda ith qeela lahum tamattaAAoo hatta heenin

Translation: Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci,"

51:44

فَعَتَوۡاْ عَنۡ أَمۡرِ رَبِّهِمۡ فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّـٰعِقَةُ وَهُمۡ يَنظُرُونَ ﴿44﴾

Transliteration: FaAAataw AAan amri rabbihim faakhathathumu alssaAAiqatu wahum yanthuroona

Translation: Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo.

51:45

فَمَا ٱسۡتَطَٰعُواْ مِن قِيَامٖ وَمَا كَانُواْ مُنتَصِرِينَ ﴿45﴾

Transliteration: Fama istataAAoo min qiyamin wama kanoo muntasireena

Translation: Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba.

51:46

وَقَوۡمَ نُوحٖ مِّن قَبۡلُۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمٗا فَٰسِقِينَ ﴿46﴾

Transliteration: Waqawma noohin min qablu innahum kanoo qawman fasiqeena

Translation: Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.

51:47

وَٱلسَّمَآءَ بَنَيۡنَٰهَا بِأَيۡيْدٖ وَإِنَّا لَمُوسِعُونَ ﴿47﴾

Transliteration: Waalssamaa banaynaha biaydin wainna lamoosiAAoona

Translation: Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa.

51:48

وَٱلۡأَرۡضَ فَرَشۡنَٰهَا فَنِعۡمَ ٱلۡمَٰهِدُونَ ﴿48﴾

Transliteration: Waalarda farashnaha faniAAma almahidoona

Translation: Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ,

51:49

وَمِن كُلِّ شَيۡءٍ خَلَقۡنَا زَوۡجَيۡنِ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ ﴿49﴾

Transliteration: Wamin kulli shayin khalaqna zawjayni laAAallakum tathakkaroona

Translation: Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni.

51:50

فَفِرُّوٓاْ إِلَى ٱللَّهِۖ إِنِّي لَكُم مِّنۡهُ نَذِيرٞ مُّبِينٞ ﴿50﴾

Transliteration: Fafirroo ila Allahi innee lakum minhu natheerun mubeenun

Translation: Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.

51:51

وَلَا تَجۡعَلُواْ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۖ إِنِّي لَكُم مِّنۡهُ نَذِيرٞ مُّبِينٞ ﴿51﴾

Transliteration: Wala tajAAaloo maAAa Allahi ilahan akhara innee lakum minhu natheerun mubeenun

Translation: Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi.

51:52

كَذَٰلِكَ مَآ أَتَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا قَالُواْ سَاحِرٌ أَوۡ مَجۡنُونٌ ﴿52﴾

Transliteration: Kathalika ma ata allatheena min qablihim min rasoolin illa qaloo sahirun aw majnoonun

Translation: Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci."

51:53

أَتَوَاصَوۡاْ بِهِۦۚ بَلۡ هُمۡ قَوۡمٞ طَاغُونَ ﴿53﴾

Transliteration: Atawasaw bihi bal hum qawmun taghoona

Translation: shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai.

51:54

فَتَوَلَّ عَنۡهُمۡ فَمَآ أَنتَ بِمَلُومٖ ﴿54﴾

Transliteration: Fatawalla AAanhum fama anta bimaloomin

Translation: Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne.

51:55

وَذَكِّرۡ فَإِنَّ ٱلذِّكۡرَىٰ تَنفَعُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ﴿55﴾

Transliteration: Wathakkir fainna alththikra tanfaAAu almumineena

Translation: Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.

51:56

وَمَا خَلَقۡتُ ٱلۡجِنَّ وَٱلۡإِنسَ إِلَّا لِيَعۡبُدُونِ ﴿56﴾

Transliteration: Wama khalaqtu aljinna waalinsa illa liyaAAbudooni

Translation: Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.

51:57

مَآ أُرِيدُ مِنۡهُم مِّن رِّزۡقٖ وَمَآ أُرِيدُ أَن يُطۡعِمُونِ ﴿57﴾

Transliteration: Ma oreedu minhum min rizqin wama oreedu an yutAAimooni

Translation: Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni.

51:58

إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلرَّزَّاقُ ذُو ٱلۡقُوَّةِ ٱلۡمَتِينُ ﴿58﴾

Transliteration: Inna Allaha huwa alrrazzaqu thoo alquwwati almateenu

Translation: Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi.

51:59

فَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ ذَنُوبٗا مِّثۡلَ ذَنُوبِ أَصۡحَٰبِهِمۡ فَلَا يَسۡتَعۡجِلُونِ ﴿59﴾

Transliteration: Fainna lillatheena thalamoo thanooban mithla thanoobi ashabihim fala yastaAAjiloona

Translation: To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa.

51:60

فَوَيۡلٞ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن يَوۡمِهِمُ ٱلَّذِي يُوعَدُونَ ﴿60﴾

Transliteration: Fawaylun lillatheena kafaroo min yawmihimu allathee yooAAadoona

Translation: Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari.

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download