quranm◉

Surah Al-Layl transliteration

◉ Sura · ∞

92:1

وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَغۡشَىٰ ﴿1﴾

Transliteration: Waallayli itha yaghsha

Translation: Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa.

92:2

وَٱلنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّىٰ ﴿2﴾

Transliteration: Waalnnahari itha tajalla

Translation: Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa.

92:3

وَمَا خَلَقَ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰٓ ﴿3﴾

Transliteration: Wama khalaqa alththakara waalontha

Translation: Da abin da ya halitta namiji da mace.

92:4

إِنَّ سَعۡيَكُمۡ لَشَتَّىٰ ﴿4﴾

Transliteration: Inna saAAyakum lashatta

Translation: Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke.

92:5

فَأَمَّا مَنۡ أَعۡطَىٰ وَٱتَّقَىٰ ﴿5﴾

Transliteration: Faamma man aAAta waittaqa

Translation: To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa.

92:6

وَصَدَّقَ بِٱلۡحُسۡنَىٰ ﴿6﴾

Transliteration: Wasaddaqa bialhusna

Translation: Kuma ya gaskata kalma mai kyãwo.

92:7

فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلۡيُسۡرَىٰ ﴿7﴾

Transliteration: Fasanuyassiruhu lilyusra

Translation: To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi.

92:8

وَأَمَّا مَنۢ بَخِلَ وَٱسۡتَغۡنَىٰ ﴿8﴾

Transliteration: Waamma man bakhila waistaghna

Translation: Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa.

92:9

وَكَذَّبَ بِٱلۡحُسۡنَىٰ ﴿9﴾

Transliteration: Wakaththaba bialhusna

Translation: Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo.

92:10

فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلۡعُسۡرَىٰ ﴿10﴾

Transliteration: Fasanuyassiruhu lilAAusra

Translation: To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani.

92:11

وَمَا يُغۡنِي عَنۡهُ مَالُهُۥٓ إِذَا تَرَدَّىٰٓ ﴿11﴾

Transliteration: Wama yughnee AAanhu maluhu itha taradda

Translation: Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta).

92:12

إِنَّ عَلَيۡنَا لَلۡهُدَىٰ ﴿12﴾

Transliteration: Inna AAalayna lalhuda

Translation: Lãlle aikin Mu ne, Mu bayyana shiriya.

92:13

وَإِنَّ لَنَا لَلۡأٓخِرَةَ وَٱلۡأُولَىٰ ﴿13﴾

Transliteration: Wainna lana lalakhirata waaloola

Translation: Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne.

92:14

فَأَنذَرۡتُكُمۡ نَارٗا تَلَظَّىٰ ﴿14﴾

Transliteration: Faanthartukum naran talaththa

Translation: Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka.

92:15

لَا يَصۡلَىٰهَآ إِلَّا ٱلۡأَشۡقَى ﴿15﴾

Transliteration: La yaslaha illa alashqa

Translation: Bãbu mai shigarta sai mafi Tabewa

92:16

ٱلَّذِي كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ ﴿16﴾

Transliteration: Allathee kaththaba watawalla

Translation: Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.

92:17

وَسَيُجَنَّبُهَا ٱلۡأَتۡقَى ﴿17﴾

Transliteration: Wasayujannabuha alatqa

Translation: Kuma mafi taƙawa zai nisance ta.

92:18

ٱلَّذِي يُؤۡتِي مَالَهُۥ يَتَزَكَّىٰ ﴿18﴾

Transliteration: Allathee yutee malahu yatazakka

Translation: Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka.

92:19

وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُۥ مِن نِّعۡمَةٖ تُجۡزَىٰٓ ﴿19﴾

Transliteration: Wama liahadin AAindahu min niAAmatin tujza

Translation: Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta.

92:20

إِلَّا ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ رَبِّهِ ٱلۡأَعۡلَىٰ ﴿20﴾

Transliteration: Illa ibtighaa wajhi rabbihi alaAAla

Translation: Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka.

92:21

وَلَسَوۡفَ يَرۡضَىٰ ﴿21﴾

Transliteration: Walasawfa yarda

Translation: To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi).

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download