quranm◉

Surah Al-Waqi'ah transliteration

◉ Sura · ∞

56:1

إِذَا وَقَعَتِ ٱلۡوَاقِعَةُ ﴿1﴾

Transliteration: Itha waqaAAati alwaqiAAatu

Translation: Idan mai aukuwa ta auku.

56:2

لَيۡسَ لِوَقۡعَتِهَا كَاذِبَةٌ ﴿2﴾

Transliteration: Laysa liwaqAAatiha kathibatun

Translation: Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.

56:3

خَافِضَةٞ رَّافِعَةٌ ﴿3﴾

Transliteration: Khafidatun rafiAAatun

Translation: (Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.

56:4

إِذَا رُجَّتِ ٱلۡأَرۡضُ رَجّٗا ﴿4﴾

Transliteration: Itha rujjati alardu rajjan

Translation: Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.

56:5

وَبُسَّتِ ٱلۡجِبَالُ بَسّٗا ﴿5﴾

Transliteration: Wabussati aljibalu bassan

Translation: Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.

56:6

فَكَانَتۡ هَبَآءٗ مُّنۢبَثّٗا ﴿6﴾

Transliteration: Fakanat habaan munbaththan

Translation: Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.

56:7

وَكُنتُمۡ أَزۡوَٰجٗا ثَلَٰثَةٗ ﴿7﴾

Transliteration: Wakuntum azwajan thalathatan

Translation: Kuma kun kasance nau'i uku.

56:8

فَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ ﴿8﴾

Transliteration: Faashabu almaymanati ma ashabu almaymanati

Translation: Watau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?

56:9

وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ ﴿9﴾

Transliteration: Waashabu almashamati ma ashabu almashamati

Translation: Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?

56:10

وَٱلسَّـٰبِقُونَ ٱلسَّـٰبِقُونَ ﴿10﴾

Transliteration: Waalssabiqoona alssabiqoona

Translation: Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,

56:11

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلۡمُقَرَّبُونَ ﴿11﴾

Transliteration: Olaika almuqarraboona

Translation: Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.

56:12

فِي جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ ﴿12﴾

Transliteration: Fee jannati alnnaAAeemi

Translation: A ckin Aljannar ni'ima.

56:13

ثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ ﴿13﴾

Transliteration: Thullatun mina alawwaleena

Translation: Jama'a ne daga mutãnen farko.

56:14

وَقَلِيلٞ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ ﴿14﴾

Transliteration: Waqaleelun mina alakhireena

Translation: Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.

56:15

عَلَىٰ سُرُرٖ مَّوۡضُونَةٖ ﴿15﴾

Transliteration: AAala sururin mawdoonatin

Translation: (Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙu.

56:16

مُّتَّكِـِٔينَ عَلَيۡهَا مُتَقَٰبِلِينَ ﴿16﴾

Transliteration: Muttakieena AAalayha mutaqabileena

Translation: Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.

56:17

يَطُوفُ عَلَيۡهِمۡ وِلۡدَٰنٞ مُّخَلَّدُونَ ﴿17﴾

Transliteration: Yatoofu AAalayhim wildanun mukhalladoona

Translation: Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.

56:18

بِأَكۡوَابٖ وَأَبَارِيقَ وَكَأۡسٖ مِّن مَّعِينٖ ﴿18﴾

Transliteration: Biakwabin waabareeqa wakasin min maAAeenin

Translation: Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.

56:19

لَّا يُصَدَّعُونَ عَنۡهَا وَلَا يُنزِفُونَ ﴿19﴾

Transliteration: La yusaddaAAoona AAanha wala yunzifoona

Translation: Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.

56:20

وَفَٰكِهَةٖ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَ ﴿20﴾

Transliteration: Wafakihatin mimma yatakhayyaroona

Translation: Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.

56:21

وَلَحۡمِ طَيۡرٖ مِّمَّا يَشۡتَهُونَ ﴿21﴾

Transliteration: Walahmi tayrin mimma yashtahoona

Translation: Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa.

56:22

وَحُورٌ عِينٞ ﴿22﴾

Transliteration: Wahoorun AAeenun

Translation: Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.

56:23

كَأَمۡثَٰلِ ٱللُّؤۡلُوِٕ ٱلۡمَكۡنُونِ ﴿23﴾

Transliteration: Kaamthali allului almaknooni

Translation: Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye.

56:24

جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ ﴿24﴾

Transliteration: Jazaan bima kanoo yaAAmaloona

Translation: A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.

56:25

لَا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوٗا وَلَا تَأۡثِيمًا ﴿25﴾

Transliteration: La yasmaAAoona feeha laghwan wala tatheeman

Translation: Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.

56:26

إِلَّا قِيلٗا سَلَٰمٗا سَلَٰمٗا ﴿26﴾

Transliteration: Illa qeelan salaman salaman

Translation: Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.

56:27

وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ ﴿27﴾

Transliteration: Waashabu alyameeni ma ashabu alyameeni

Translation: Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?

56:28

فِي سِدۡرٖ مَّخۡضُودٖ ﴿28﴾

Transliteration: Fee sidrin makhdoodin

Translation: (Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.

56:29

وَطَلۡحٖ مَّنضُودٖ ﴿29﴾

Transliteration: Watalhin mandoodin

Translation: Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya.

56:30

وَظِلّٖ مَّمۡدُودٖ ﴿30﴾

Transliteration: Wathillin mamdoodin

Translation: Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.

56:31

وَمَآءٖ مَّسۡكُوبٖ ﴿31﴾

Transliteration: Wamain maskoobin

Translation: Da wani ruwa mai gudãna.

56:32

وَفَٰكِهَةٖ كَثِيرَةٖ ﴿32﴾

Transliteration: Wafakihatin katheeratin

Translation: Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa.

56:33

لَّا مَقۡطُوعَةٖ وَلَا مَمۡنُوعَةٖ ﴿33﴾

Transliteration: La maqtooAAatin wala mamnooAAatin

Translation: Bã su yankẽwa kuma bã a hana su.

56:34

وَفُرُشٖ مَّرۡفُوعَةٍ ﴿34﴾

Transliteration: Wafurushin marfooAAatin

Translation: Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.

56:35

إِنَّآ أَنشَأۡنَٰهُنَّ إِنشَآءٗ ﴿35﴾

Transliteration: Inna anshanahunna inshaan

Translation: Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.

56:36

فَجَعَلۡنَٰهُنَّ أَبۡكَارًا ﴿36﴾

Transliteration: FajaAAalnahunna abkaran

Translation: Sa'an nan Muka sanya su budurwai.

56:37

عُرُبًا أَتۡرَابٗا ﴿37﴾

Transliteration: AAuruban atraban

Translation: Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.

56:38

لِّأَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ ﴿38﴾

Transliteration: Liashabi alyameeni

Translation: Ga mazõwa dãma.

56:39

ثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ ﴿39﴾

Transliteration: Thullatun mina alawwaleena

Translation: Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.

56:40

وَثُلَّةٞ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ ﴿40﴾

Transliteration: Wathullatun mina alakhireena

Translation: Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.

56:41

وَأَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ ﴿41﴾

Transliteration: Waashabu alshshimali ma ashabu alshshimali

Translation: Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?

56:42

فِي سَمُومٖ وَحَمِيمٖ ﴿42﴾

Transliteration: Fee samoomin wahameemin

Translation: Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.

56:43

وَظِلّٖ مِّن يَحۡمُومٖ ﴿43﴾

Transliteration: Wathillin min yahmoomin

Translation: Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.

56:44

لَّا بَارِدٖ وَلَا كَرِيمٍ ﴿44﴾

Transliteration: La baridin wala kareemin

Translation: Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba.

56:45

إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَبۡلَ ذَٰلِكَ مُتۡرَفِينَ ﴿45﴾

Transliteration: Innahum kanoo qabla thalika mutrafeena

Translation: Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.

56:46

وَكَانُواْ يُصِرُّونَ عَلَى ٱلۡحِنثِ ٱلۡعَظِيمِ ﴿46﴾

Transliteration: Wakanoo yusirroona AAala alhinthi alAAatheemi

Translation: Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.

56:47

وَكَانُواْ يَقُولُونَ أَئِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ ﴿47﴾

Transliteration: Wakanoo yaqooloona aitha mitna wakunna turaban waAAithaman ainna lamabAAoothoona

Translation: Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?"

56:48

أَوَءَابَآؤُنَا ٱلۡأَوَّلُونَ ﴿48﴾

Transliteration: Awa abaona alawwaloona

Translation: "Shin, kuma da ubanninmu na farko?"

56:49

قُلۡ إِنَّ ٱلۡأَوَّلِينَ وَٱلۡأٓخِرِينَ ﴿49﴾

Transliteration: Qul inna alawwaleena waalakhireena

Translation: Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe."

56:50

لَمَجۡمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَٰتِ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ ﴿50﴾

Transliteration: LamajmooAAoona ila meeqati yawmin maAAloomin

Translation: "Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne."

56:51

ثُمَّ إِنَّكُمۡ أَيُّهَا ٱلضَّآلُّونَ ٱلۡمُكَذِّبُونَ ﴿51﴾

Transliteration: Thumma innakum ayyuha alddalloona almukaththiboona

Translation: "Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"

56:52

لَأٓكِلُونَ مِن شَجَرٖ مِّن زَقُّومٖ ﴿52﴾

Transliteration: Laakiloona min shajarin min zaqqoomin

Translation: "Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."

56:53

فَمَالِـُٔونَ مِنۡهَا ٱلۡبُطُونَ ﴿53﴾

Transliteration: Famalioona minha albutoona

Translation: "Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."

56:54

فَشَٰرِبُونَ عَلَيۡهِ مِنَ ٱلۡحَمِيمِ ﴿54﴾

Transliteration: Fashariboona AAalayhi mina alhameemi

Translation: "Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."

56:55

فَشَٰرِبُونَ شُرۡبَ ٱلۡهِيمِ ﴿55﴾

Transliteration: Fashariboona shurba alheemi

Translation: "Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."

56:56

هَٰذَا نُزُلُهُمۡ يَوۡمَ ٱلدِّينِ ﴿56﴾

Transliteration: Hatha nuzuluhum yawma alddeeni

Translation: Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.

56:57

نَحۡنُ خَلَقۡنَٰكُمۡ فَلَوۡلَا تُصَدِّقُونَ ﴿57﴾

Transliteration: Nahnu khalaqnakum falawla tusaddiqoona

Translation: Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?

56:58

أَفَرَءَيۡتُم مَّا تُمۡنُونَ ﴿58﴾

Transliteration: Afaraaytum ma tumnoona

Translation: Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?

56:59

ءَأَنتُمۡ تَخۡلُقُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡخَٰلِقُونَ ﴿59﴾

Transliteration: Aantum takhluqoonahu am nahnu alkhaliqoona

Translation: Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?

56:60

نَحۡنُ قَدَّرۡنَا بَيۡنَكُمُ ٱلۡمَوۡتَ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ ﴿60﴾

Transliteration: Nahnu qaddarna baynakumu almawta wama nahnu bimasbooqeena

Translation: Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ba,

56:61

عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ أَمۡثَٰلَكُمۡ وَنُنشِئَكُمۡ فِي مَا لَا تَعۡلَمُونَ ﴿61﴾

Transliteration: AAala an nubaddila amthalakum wanunshiakum fee ma la taAAlamoona

Translation: A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.

56:62

وَلَقَدۡ عَلِمۡتُمُ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأُولَىٰ فَلَوۡلَا تَذَكَّرُونَ ﴿62﴾

Transliteration: Walaqad AAalimtumu alnnashata aloola falawla tathakkaroona

Translation: Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?

56:63

أَفَرَءَيۡتُم مَّا تَحۡرُثُونَ ﴿63﴾

Transliteration: Afaraaytum ma tahruthoona

Translation: Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?

56:64

ءَأَنتُمۡ تَزۡرَعُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلزَّـٰرِعُونَ ﴿64﴾

Transliteration: Aantum tazraAAoonahu am nahnu alzzariAAoona

Translation: Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?

56:65

لَوۡ نَشَآءُ لَجَعَلۡنَٰهُ حُطَٰمٗا فَظَلۡتُمۡ تَفَكَّهُونَ ﴿65﴾

Transliteration: Law nashao lajaAAalnahu hutaman fathaltum tafakkahoona

Translation: Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.

56:66

إِنَّا لَمُغۡرَمُونَ ﴿66﴾

Transliteration: Inna lamughramoona

Translation: (Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"

56:67

بَلۡ نَحۡنُ مَحۡرُومُونَ ﴿67﴾

Transliteration: Bal nahnu mahroomoona

Translation: "Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"

56:68

أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلۡمَآءَ ٱلَّذِي تَشۡرَبُونَ ﴿68﴾

Transliteration: Afaraaytumu almaa allathee tashraboona

Translation: Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?

56:69

ءَأَنتُمۡ أَنزَلۡتُمُوهُ مِنَ ٱلۡمُزۡنِ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنزِلُونَ ﴿69﴾

Transliteration: Aantum anzaltumoohu mina almuzni am nahnu almunziloona

Translation: Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?

56:70

لَوۡ نَشَآءُ جَعَلۡنَٰهُ أُجَاجٗا فَلَوۡلَا تَشۡكُرُونَ ﴿70﴾

Transliteration: Law nashao jaAAalnahu ojajan falawla tashkuroona

Translation: Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?

56:71

أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلنَّارَ ٱلَّتِي تُورُونَ ﴿71﴾

Transliteration: Afaraaytumu alnnara allatee tooroona

Translation: Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?

56:72

ءَأَنتُمۡ أَنشَأۡتُمۡ شَجَرَتَهَآ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنشِـُٔونَ ﴿72﴾

Transliteration: Aantum anshatum shajarataha am nahnu almunshioona

Translation: Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?

56:73

نَحۡنُ جَعَلۡنَٰهَا تَذۡكِرَةٗ وَمَتَٰعٗا لِّلۡمُقۡوِينَ ﴿73﴾

Transliteration: Nahnu jaAAalnaha tathkiratan wamataAAan lilmuqweena

Translation: Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.

56:74

فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ ﴿74﴾

Transliteration: Fasabbih biismi rabbika alAAatheemi

Translation: Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.

56:75

فَلَآ أُقۡسِمُ بِمَوَٰقِعِ ٱلنُّجُومِ ﴿75﴾

Transliteration: Fala oqsimu bimawaqiAAi alnnujoomi

Translation: To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.

56:76

وَإِنَّهُۥ لَقَسَمٞ لَّوۡ تَعۡلَمُونَ عَظِيمٌ ﴿76﴾

Transliteration: Wainnahu laqasamun law taAAlamoona AAatheemun

Translation: Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.

56:77

إِنَّهُۥ لَقُرۡءَانٞ كَرِيمٞ ﴿77﴾

Transliteration: Innahu laquranun kareemun

Translation: Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.

56:78

فِي كِتَٰبٖ مَّكۡنُونٖ ﴿78﴾

Transliteration: Fee kitabin maknoonin

Translation: A cikin wani littafi tsararre.

56:79

لَّا يَمَسُّهُۥٓ إِلَّا ٱلۡمُطَهَّرُونَ ﴿79﴾

Transliteration: La yamassuhu illa almutahharoona

Translation: Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.

56:80

تَنزِيلٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ﴿80﴾

Transliteration: Tanzeelun min rabbi alAAalameena

Translation: Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.

56:81

أَفَبِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ أَنتُم مُّدۡهِنُونَ ﴿81﴾

Transliteration: Afabihatha alhadeethi antum mudhinoona

Translation: Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?

56:82

وَتَجۡعَلُونَ رِزۡقَكُمۡ أَنَّكُمۡ تُكَذِّبُونَ ﴿82﴾

Transliteration: WatajAAaloona rizqakum annakum tukaththiboona

Translation: Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?

56:83

فَلَوۡلَآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلۡحُلۡقُومَ ﴿83﴾

Transliteration: Falawla itha balaghati alhulqooma

Translation: To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).

56:84

وَأَنتُمۡ حِينَئِذٖ تَنظُرُونَ ﴿84﴾

Transliteration: Waantum heenaithin tanthuroona

Translation: Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.

56:85

وَنَحۡنُ أَقۡرَبُ إِلَيۡهِ مِنكُمۡ وَلَٰكِن لَّا تُبۡصِرُونَ ﴿85﴾

Transliteration: Wanahnu aqrabu ilayhi minkum walakin la tubsiroona

Translation: Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.

56:86

فَلَوۡلَآ إِن كُنتُمۡ غَيۡرَ مَدِينِينَ ﴿86﴾

Transliteration: Falawla in kuntum ghayra madeeneena

Translation: To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?

56:87

تَرۡجِعُونَهَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ ﴿87﴾

Transliteration: TarjiAAoonaha in kuntum sadiqeena

Translation: Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.

56:88

فَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ ﴿88﴾

Transliteration: Faamma in kana mina almuqarrabeena

Translation: To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,

56:89

فَرَوۡحٞ وَرَيۡحَانٞ وَجَنَّتُ نَعِيمٖ ﴿89﴾

Transliteration: Farawhun warayhanun wajannatu naAAeemin

Translation: Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.

56:90

وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ ﴿90﴾

Transliteration: Waamma in kana min ashabi alyameeni

Translation: Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,

56:91

فَسَلَٰمٞ لَّكَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ ﴿91﴾

Transliteration: Fasalamun laka min ashabi alyameeni

Translation: Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.

56:92

وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُكَذِّبِينَ ٱلضَّآلِّينَ ﴿92﴾

Transliteration: Waamma in kana mina almukaththibeena alddalleena

Translation: Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,

56:93

فَنُزُلٞ مِّنۡ حَمِيمٖ ﴿93﴾

Transliteration: Fanuzulun min hameemin

Translation: Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.

56:94

وَتَصۡلِيَةُ جَحِيمٍ ﴿94﴾

Transliteration: Watasliyatu jaheemin

Translation: Da ƙõnuwa da Jahĩm,

56:95

إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ ٱلۡيَقِينِ ﴿95﴾

Transliteration: Inna hatha lahuwa haqqu alyaqeeni

Translation: Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.

56:96

فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ ﴿96﴾

Transliteration: Fasabbih biismi rabbika alAAatheemi

Translation: Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci.

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download