quranm◉

Surah Al-Qiyamah transliteration

◉ Sura · ∞

75:1

لَآ أُقۡسِمُ بِيَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ ﴿1﴾

Transliteration: La oqsimu biyawmi alqiyamati

Translation: Bã sai Nã yi rantsuwa da Rãnar ¡iyãma ba.

75:2

وَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلنَّفۡسِ ٱللَّوَّامَةِ ﴿2﴾

Transliteration: Wala oqsimu bialnnafsi allawwamati

Translation: Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa ba.

75:3

أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَلَّن نَّجۡمَعَ عِظَامَهُۥ ﴿3﴾

Transliteration: Ayahsabu alinsanu allan najmaAAa AAithamahu

Translation: Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?

75:4

بَلَىٰ قَٰدِرِينَ عَلَىٰٓ أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُۥ ﴿4﴾

Transliteration: Bala qadireena AAala an nusawwiya bananahu

Translation: Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.

75:5

بَلۡ يُرِيدُ ٱلۡإِنسَٰنُ لِيَفۡجُرَ أَمَامَهُۥ ﴿5﴾

Transliteration: Bal yureedu alinsanu liyafjura amamahu

Translation: Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.

75:6

يَسۡـَٔلُ أَيَّانَ يَوۡمُ ٱلۡقِيَٰمَةِ ﴿6﴾

Transliteration: Yasalu ayyana yawmu alqiyamati

Translation: Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?"

75:7

فَإِذَا بَرِقَ ٱلۡبَصَرُ ﴿7﴾

Transliteration: Faitha bariqa albasaru

Translation: To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).

75:8

وَخَسَفَ ٱلۡقَمَرُ ﴿8﴾

Transliteration: Wakhasafa alqamaru

Translation: Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).

75:9

وَجُمِعَ ٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ ﴿9﴾

Transliteration: WajumiAAa alshshamsu waalqamaru

Translation: Aka tãra rãnã da watã

75:10

يَقُولُ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذٍ أَيۡنَ ٱلۡمَفَرُّ ﴿10﴾

Transliteration: Yaqoolu alinsanu yawmaithin ayna almafarru

Translation: Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?"

75:11

كَلَّا لَا وَزَرَ ﴿11﴾

Transliteration: Kalla la wazara

Translation: A'aha! bãbu mafaka.

75:12

إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمُسۡتَقَرُّ ﴿12﴾

Transliteration: Ila rabbika yawmaithin almustaqarru

Translation: zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.

75:13

يُنَبَّؤُاْ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذِۭ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ ﴿13﴾

Transliteration: Yunabbao alinsanu yawmaithin bima qaddama waakhkhara

Translation: Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.

75:14

بَلِ ٱلۡإِنسَٰنُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦ بَصِيرَةٞ ﴿14﴾

Transliteration: Bali alinsanu AAala nafsihi baseeratun

Translation: Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.

75:15

وَلَوۡ أَلۡقَىٰ مَعَاذِيرَهُۥ ﴿15﴾

Transliteration: Walaw alqa maAAatheerahu

Translation: Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).

75:16

لَا تُحَرِّكۡ بِهِۦ لِسَانَكَ لِتَعۡجَلَ بِهِۦٓ ﴿16﴾

Transliteration: La tuharrik bihi lisanaka litaAAjala bihi

Translation: Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).

75:17

إِنَّ عَلَيۡنَا جَمۡعَهُۥ وَقُرۡءَانَهُۥ ﴿17﴾

Transliteration: Inna AAalayna jamAAahu waquranahu

Translation: Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.

75:18

فَإِذَا قَرَأۡنَٰهُ فَٱتَّبِعۡ قُرۡءَانَهُۥ ﴿18﴾

Transliteration: Faitha qaranahu faittabiAA quranahu

Translation: To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.

75:19

ثُمَّ إِنَّ عَلَيۡنَا بَيَانَهُۥ ﴿19﴾

Transliteration: Thumma inna AAalayna bayanahu

Translation: sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.

75:20

كَلَّا بَلۡ تُحِبُّونَ ٱلۡعَاجِلَةَ ﴿20﴾

Transliteration: Kalla bal tuhibboona alAAajilata

Translation: A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.

75:21

وَتَذَرُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ ﴿21﴾

Transliteration: Watatharoona alakhirata

Translation: Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).

75:22

وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ نَّاضِرَةٌ ﴿22﴾

Transliteration: Wujoohun yawmaithin nadiratun

Translation: Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.

75:23

إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٞ ﴿23﴾

Transliteration: Ila rabbiha nathiratun

Translation: Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.

75:24

وَوُجُوهٞ يَوۡمَئِذِۭ بَاسِرَةٞ ﴿24﴾

Transliteration: Wawujoohun yawmaithin basiratun

Translation: Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.

75:25

تَظُنُّ أَن يُفۡعَلَ بِهَا فَاقِرَةٞ ﴿25﴾

Transliteration: Tathunnu an yufAAala biha faqiratun

Translation: Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.

75:26

كَلَّآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلتَّرَاقِيَ ﴿26﴾

Transliteration: Kalla itha balaghati alttaraqiya

Translation: A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.

75:27

وَقِيلَ مَنۡۜ رَاقٖ ﴿27﴾

Transliteration: Waqeela man raqin

Translation: kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"

75:28

وَظَنَّ أَنَّهُ ٱلۡفِرَاقُ ﴿28﴾

Transliteration: Wathanna annahu alfiraqu

Translation: Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.

75:29

وَٱلۡتَفَّتِ ٱلسَّاقُ بِٱلسَّاقِ ﴿29﴾

Transliteration: Wailtaffati alssaqu bialssaqi

Translation: Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.

75:30

إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمَسَاقُ ﴿30﴾

Transliteration: Ila rabbika yawmaithin almasaqu

Translation: Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa take.

75:31

فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ ﴿31﴾

Transliteration: Fala saddaqa wala salla

Translation: To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!

75:32

وَلَٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ ﴿32﴾

Transliteration: Walakin kaththaba watawalla

Translation: Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!

75:33

ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ يَتَمَطَّىٰٓ ﴿33﴾

Transliteration: Thumma thahaba ila ahlihi yatamatta

Translation: Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.

75:34

أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰ ﴿34﴾

Transliteration: Awla laka faawla

Translation: Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.

75:35

ثُمَّ أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰٓ ﴿35﴾

Transliteration: Thumma awla laka faawla

Translation: Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.

75:36

أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَن يُتۡرَكَ سُدًى ﴿36﴾

Transliteration: Ayahsabu alinsanu an yutraka sudan

Translation: Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?

75:37

أَلَمۡ يَكُ نُطۡفَةٗ مِّن مَّنِيّٖ يُمۡنَىٰ ﴿37﴾

Transliteration: Alam yaku nutfatan min manayyin yumna

Translation: Bai kasance ɗigo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)

75:38

ثُمَّ كَانَ عَلَقَةٗ فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ ﴿38﴾

Transliteration: Thumma kana AAalaqatan fakhalaqa fasawwa

Translation: Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;

75:39

فَجَعَلَ مِنۡهُ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰٓ ﴿39﴾

Transliteration: FajaAAala minhu alzzawjayni alththakara waalontha

Translation: Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?

75:40

أَلَيۡسَ ذَٰلِكَ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحۡـِۧيَ ٱلۡمَوۡتَىٰ ﴿40﴾

Transliteration: Alaysa thalika biqadirin AAala an yuhyiya almawta

Translation: Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download