quranm◉

Surah Al-Mursalat transliteration

◉ Sura · ∞

77:1

وَٱلۡمُرۡسَلَٰتِ عُرۡفٗا ﴿1﴾

Transliteration: Waalmursalati AAurfan

Translation: Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.

77:2

فَٱلۡعَٰصِفَٰتِ عَصۡفٗا ﴿2﴾

Transliteration: FaalAAasifati AAasfan

Translation: Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.

77:3

وَٱلنَّـٰشِرَٰتِ نَشۡرٗا ﴿3﴾

Transliteration: Waalnnashirati nashran

Translation: Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.

77:4

فَٱلۡفَٰرِقَٰتِ فَرۡقٗا ﴿4﴾

Transliteration: Faalfariqati farqan

Translation: sa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.

77:5

فَٱلۡمُلۡقِيَٰتِ ذِكۡرًا ﴿5﴾

Transliteration: Faalmulqiyati thikran

Translation: Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.

77:6

عُذۡرًا أَوۡ نُذۡرًا ﴿6﴾

Transliteration: AAuthran aw nuthran

Translation: Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.

77:7

إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَٰقِعٞ ﴿7﴾

Transliteration: Innama tooAAadoona lawaqiAAun

Translation: Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne

77:8

فَإِذَا ٱلنُّجُومُ طُمِسَتۡ ﴿8﴾

Transliteration: Faitha alnnujoomu tumisat

Translation: To, idan taurãri aka shãfe haskensu.

77:9

وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ فُرِجَتۡ ﴿9﴾

Transliteration: Waitha alssamao furijat

Translation: Kuma, idan sama aka tsãge ta.

77:10

وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ نُسِفَتۡ ﴿10﴾

Transliteration: Waitha aljibalu nusifat

Translation: Kuma, idan duwãtsu aka nike su.

77:11

وَإِذَا ٱلرُّسُلُ أُقِّتَتۡ ﴿11﴾

Transliteration: Waitha alrrusulu oqqitat

Translation: Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.

77:12

لِأَيِّ يَوۡمٍ أُجِّلَتۡ ﴿12﴾

Transliteration: Liayyi yawmin ojjilat

Translation: Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.

77:13

لِيَوۡمِ ٱلۡفَصۡلِ ﴿13﴾

Transliteration: Liyawmi alfasli

Translation: Domin rãnar rarrabẽwa.

77:14

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ ﴿14﴾

Transliteration: Wama adraka ma yawmu alfasli

Translation: Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?

77:15

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ﴿15﴾

Transliteration: Waylun yawmaithin lilmukaththibeena

Translation: Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

77:16

أَلَمۡ نُهۡلِكِ ٱلۡأَوَّلِينَ ﴿16﴾

Transliteration: Alam nuhliki alawwaleena

Translation: Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.

77:17

ثُمَّ نُتۡبِعُهُمُ ٱلۡأٓخِرِينَ ﴿17﴾

Transliteration: Thumma nutbiAAuhumu alakhireena

Translation: Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?

77:18

كَذَٰلِكَ نَفۡعَلُ بِٱلۡمُجۡرِمِينَ ﴿18﴾

Transliteration: Kathalika nafAAalu bialmujrimeena

Translation: Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.

77:19

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ﴿19﴾

Transliteration: Waylun yawmaithin lilmukaththibeena

Translation: Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!

77:20

أَلَمۡ نَخۡلُقكُّم مِّن مَّآءٖ مَّهِينٖ ﴿20﴾

Transliteration: Alam nakhluqkum min main maheenin

Translation: Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.

77:21

فَجَعَلۡنَٰهُ فِي قَرَارٖ مَّكِينٍ ﴿21﴾

Transliteration: FajaAAalnahu fee qararin makeenin

Translation: Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.

77:22

إِلَىٰ قَدَرٖ مَّعۡلُومٖ ﴿22﴾

Transliteration: Ila qadarin maAAloomin

Translation: Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.

77:23

فَقَدَرۡنَا فَنِعۡمَ ٱلۡقَٰدِرُونَ ﴿23﴾

Transliteration: Faqadarna faniAAma alqadiroona

Translation: Sa'an nan, Muka nũna iyãwar Mu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.

77:24

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ﴿24﴾

Transliteration: Waylun yawmaithin lilmukaththibeena

Translation: Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!

77:25

أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ كِفَاتًا ﴿25﴾

Transliteration: Alam najAAali alarda kifatan

Translation: Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.

77:26

أَحۡيَآءٗ وَأَمۡوَٰتٗا ﴿26﴾

Transliteration: Ahyaan waamwatan

Translation: Ga rãyayyu da matattu,

77:27

وَجَعَلۡنَا فِيهَا رَوَٰسِيَ شَٰمِخَٰتٖ وَأَسۡقَيۡنَٰكُم مَّآءٗ فُرَاتٗا ﴿27﴾

Transliteration: WajaAAalna feeha rawasiya shamikhatin waasqaynakum maan furatan

Translation: Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?

77:28

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ﴿28﴾

Transliteration: Waylun yawmaithin lilmukaththibeena

Translation: Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

77:29

ٱنطَلِقُوٓاْ إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ ﴿29﴾

Transliteration: Intaliqoo ila ma kuntum bihi tukaththiboona

Translation: Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!

77:30

ٱنطَلِقُوٓاْ إِلَىٰ ظِلّٖ ذِي ثَلَٰثِ شُعَبٖ ﴿30﴾

Transliteration: Intaliqoo ila thillin thee thalathi shuAAabin

Translation: Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.

77:31

لَّا ظَلِيلٖ وَلَا يُغۡنِي مِنَ ٱللَّهَبِ ﴿31﴾

Transliteration: La thaleelin wala yughnee mina allahabi

Translation: Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.

77:32

إِنَّهَا تَرۡمِي بِشَرَرٖ كَٱلۡقَصۡرِ ﴿32﴾

Transliteration: Innaha tarmee bishararin kaalqasri

Translation: Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.

77:33

كَأَنَّهُۥ جِمَٰلَتٞ صُفۡرٞ ﴿33﴾

Transliteration: Kaannahu jimalatun sufrun

Translation: Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.

77:34

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ﴿34﴾

Transliteration: Waylun yawmaithin lilmukaththibeena

Translation: Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

77:35

هَٰذَا يَوۡمُ لَا يَنطِقُونَ ﴿35﴾

Transliteration: Hatha yawmu la yantiqoona

Translation: Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.

77:36

وَلَا يُؤۡذَنُ لَهُمۡ فَيَعۡتَذِرُونَ ﴿36﴾

Transliteration: Wala yuthanu lahum fayaAAtathiroona

Translation: Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.

77:37

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ﴿37﴾

Transliteration: Waylun yawmaithin lilmukaththibeena

Translation: Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

77:38

هَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِۖ جَمَعۡنَٰكُمۡ وَٱلۡأَوَّلِينَ ﴿38﴾

Transliteration: Hatha yawmu alfasli jamaAAnakum waalawwaleena

Translation: Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.

77:39

فَإِن كَانَ لَكُمۡ كَيۡدٞ فَكِيدُونِ ﴿39﴾

Transliteration: Fain kana lakum kaydun fakeedooni

Translation: To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.

77:40

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ﴿40﴾

Transliteration: Waylun yawmaithin lilmukaththibeena

Translation: Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

77:41

إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي ظِلَٰلٖ وَعُيُونٖ ﴿41﴾

Transliteration: Inna almuttaqeena fee thilalin waAAuyoonin

Translation: Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.

77:42

وَفَوَٰكِهَ مِمَّا يَشۡتَهُونَ ﴿42﴾

Transliteration: Wafawakiha mimma yashtahoona

Translation: Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari.

77:43

كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِيٓـَٔۢا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ ﴿43﴾

Transliteration: Kuloo waishraboo haneean bima kuntum taAAmaloona

Translation: (A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."

77:44

إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ ﴿44﴾

Transliteration: Inna kathalika najzee almuhsineena

Translation: Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

77:45

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ﴿45﴾

Transliteration: Waylun yawmaithin lilmukaththibeena

Translation: Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

77:46

كُلُواْ وَتَمَتَّعُواْ قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجۡرِمُونَ ﴿46﴾

Transliteration: Kuloo watamattaAAoo qaleelan innakum mujrimoona

Translation: (Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne."

77:47

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ﴿47﴾

Transliteration: Waylun yawmaithin lilmukaththibeena

Translation: Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

77:48

وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱرۡكَعُواْ لَا يَرۡكَعُونَ ﴿48﴾

Transliteration: Waitha qeela lahumu irkaAAoo la yarkaAAoona

Translation: Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba."

77:49

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ﴿49﴾

Transliteration: Waylun yawmaithin lilmukaththibeena

Translation: Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!

77:50

فَبِأَيِّ حَدِيثِۭ بَعۡدَهُۥ يُؤۡمِنُونَ ﴿50﴾

Transliteration: Fabiayyi hadeethin baAAdahu yuminoona

Translation: To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download