quranm◉

Surah 'Abasa transliteration

◉ Sura · ∞

80:1

عَبَسَ وَتَوَلَّىٰٓ ﴿1﴾

Transliteration: AAabasa watawalla

Translation: Yã game huska kuma ya jũya bãya.

80:2

أَن جَآءَهُ ٱلۡأَعۡمَىٰ ﴿2﴾

Transliteration: An jaahu alaAAma

Translation: Sabõda makãho yã je masa.

80:3

وَمَا يُدۡرِيكَ لَعَلَّهُۥ يَزَّكَّىٰٓ ﴿3﴾

Transliteration: Wama yudreeka laAAallahu yazzakka

Translation: To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka.

80:4

أَوۡ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ ٱلذِّكۡرَىٰٓ ﴿4﴾

Transliteration: Aw yaththakkaru fatanfaAAahu alththikra

Translation: Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?

80:5

أَمَّا مَنِ ٱسۡتَغۡنَىٰ ﴿5﴾

Transliteration: Amma mani istaghna

Translation: Amma wanda ya wadãtu da dũkiya.

80:6

فَأَنتَ لَهُۥ تَصَدَّىٰ ﴿6﴾

Transliteration: Faanta lahu tasadda

Translation: Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!

80:7

وَمَا عَلَيۡكَ أَلَّا يَزَّكَّىٰ ﴿7﴾

Transliteration: Wama AAalayka alla yazzakka

Translation: To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?

80:8

وَأَمَّا مَن جَآءَكَ يَسۡعَىٰ ﴿8﴾

Transliteration: Waamma man jaaka yasAAa

Translation: Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.

80:9

وَهُوَ يَخۡشَىٰ ﴿9﴾

Transliteration: Wahuwa yakhsha

Translation: Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.

80:10

فَأَنتَ عَنۡهُ تَلَهَّىٰ ﴿10﴾

Transliteration: Faanta AAanhu talahha

Translation: Kai kuma kã shagala ga barinsa!

80:11

كَلَّآ إِنَّهَا تَذۡكِرَةٞ ﴿11﴾

Transliteration: Kalla innaha tathkiratun

Translation: A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.

80:12

فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ ﴿12﴾

Transliteration: Faman shaa thakarahu

Translation: Sabõda wanda ya so ya tuna Shi (Allah).

80:13

فِي صُحُفٖ مُّكَرَّمَةٖ ﴿13﴾

Transliteration: Fee suhufin mukarramatin

Translation: (Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,

80:14

مَّرۡفُوعَةٖ مُّطَهَّرَةِۭ ﴿14﴾

Transliteration: MarfooAAatin mutahharatin

Translation: Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa.

80:15

بِأَيۡدِي سَفَرَةٖ ﴿15﴾

Transliteration: Biaydee safaratin

Translation: A cikin hannãyen mala'iku marubũta.

80:16

كِرَامِۭ بَرَرَةٖ ﴿16﴾

Transliteration: Kiramin bararatin

Translation: Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah.

80:17

قُتِلَ ٱلۡإِنسَٰنُ مَآ أَكۡفَرَهُۥ ﴿17﴾

Transliteration: Qutila alinsanu ma akfarahu

Translation: An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa!

80:18

مِنۡ أَيِّ شَيۡءٍ خَلَقَهُۥ ﴿18﴾

Transliteration: Min ayyi shayin khalaqahu

Translation: Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?

80:19

مِن نُّطۡفَةٍ خَلَقَهُۥ فَقَدَّرَهُۥ ﴿19﴾

Transliteration: Min nutfatin khalaqahu faqaddarahu

Translation: Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).

80:20

ثُمَّ ٱلسَّبِيلَ يَسَّرَهُۥ ﴿20﴾

Transliteration: Thumma alssabeela yassarahu

Translation: Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.

80:21

ثُمَّ أَمَاتَهُۥ فَأَقۡبَرَهُۥ ﴿21﴾

Transliteration: Thumma amatahu faaqbarahu

Translation: Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.

80:22

ثُمَّ إِذَا شَآءَ أَنشَرَهُۥ ﴿22﴾

Transliteration: Thumma itha shaa ansharahu

Translation: Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi.

80:23

كَلَّا لَمَّا يَقۡضِ مَآ أَمَرَهُۥ ﴿23﴾

Transliteration: Kalla lamma yaqdi ma amarahu

Translation: Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari).

80:24

فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ إِلَىٰ طَعَامِهِۦٓ ﴿24﴾

Transliteration: Falyanthuri alinsanu ila taAAamihi

Translation: To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa.

80:25

أَنَّا صَبَبۡنَا ٱلۡمَآءَ صَبّٗا ﴿25﴾

Transliteration: Anna sababna almaa sabban

Translation: Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa.

80:26

ثُمَّ شَقَقۡنَا ٱلۡأَرۡضَ شَقّٗا ﴿26﴾

Transliteration: Thumma shaqaqna alarda shaqqan

Translation: Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa.

80:27

فَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا حَبّٗا ﴿27﴾

Transliteration: Faanbatna feeha habban

Translation: Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta.

80:28

وَعِنَبٗا وَقَضۡبٗا ﴿28﴾

Transliteration: WaAAinaban waqadban

Translation: Da inabi da ciyãwa.

80:29

وَزَيۡتُونٗا وَنَخۡلٗا ﴿29﴾

Transliteration: Wazaytoonan wanakhlan

Translation: Da zaitũni da itãcen dabĩno.

80:30

وَحَدَآئِقَ غُلۡبٗا ﴿30﴾

Transliteration: Wahadaiqa ghulban

Translation: Da lambuna, mãsu yawan itãce.

80:31

وَفَٰكِهَةٗ وَأَبّٗا ﴿31﴾

Transliteration: Wafakihatan waabban

Translation: Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi.

80:32

مَّتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ ﴿32﴾

Transliteration: MataAAan lakum walianAAamikum

Translation: Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku.

80:33

فَإِذَا جَآءَتِ ٱلصَّآخَّةُ ﴿33﴾

Transliteration: Faitha jaati alssakhkhatu

Translation: To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo.

80:34

يَوۡمَ يَفِرُّ ٱلۡمَرۡءُ مِنۡ أَخِيهِ ﴿34﴾

Transliteration: Yawma yafirru almaro min akheehi

Translation: Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa.

80:35

وَأُمِّهِۦ وَأَبِيهِ ﴿35﴾

Transliteration: Waommihi waabeehi

Translation: Da uwarsa da ubansa.

80:36

وَصَٰحِبَتِهِۦ وَبَنِيهِ ﴿36﴾

Transliteration: Wasahibatihi wabaneehi

Translation: Da mãtarsa da ɗiyansa.

80:37

لِكُلِّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ يَوۡمَئِذٖ شَأۡنٞ يُغۡنِيهِ ﴿37﴾

Transliteration: Likulli imriin minhum yawmaithin shanun yughneehi

Translation: Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.

80:38

وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ مُّسۡفِرَةٞ ﴿38﴾

Transliteration: Wujoohun yawmaithin musfiratun

Translation: Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne.

80:39

ضَاحِكَةٞ مُّسۡتَبۡشِرَةٞ ﴿39﴾

Transliteration: Dahikatun mustabshiratun

Translation: Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra.

80:40

وَوُجُوهٞ يَوۡمَئِذٍ عَلَيۡهَا غَبَرَةٞ ﴿40﴾

Transliteration: Wawujoohun yawmaithin AAalayha ghabaratun

Translation: Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu.

80:41

تَرۡهَقُهَا قَتَرَةٌ ﴿41﴾

Transliteration: Tarhaquha qataratun

Translation: Baƙi zai rufe su.

80:42

أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَفَرَةُ ٱلۡفَجَرَةُ ﴿42﴾

Transliteration: Olaika humu alkafaratu alfajaratu

Translation: Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download