quranm◉

Surah Al-Fajr transliteration

◉ Sura · ∞

89:1

وَٱلۡفَجۡرِ ﴿1﴾

Transliteration: Waalfajri

Translation: Inã rantsuwa da alfijiri.

89:2

وَلَيَالٍ عَشۡرٖ ﴿2﴾

Transliteration: Walayalin AAashrin

Translation: Da darũruwa gõma.

89:3

وَٱلشَّفۡعِ وَٱلۡوَتۡرِ ﴿3﴾

Transliteration: WaalshshafAAi waalwatri

Translation: Da (adadi na) cikã da (na) mãrã.

89:4

وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَسۡرِ ﴿4﴾

Transliteration: Waallayli itha yasri

Translation: Da dare idan yana shũɗewa.

89:5

هَلۡ فِي ذَٰلِكَ قَسَمٞ لِّذِي حِجۡرٍ ﴿5﴾

Transliteration: Hal fee thalika qasamun lithee hijrin

Translation: Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?

89:6

أَلَمۡ تَرَ كَيۡفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَادٍ ﴿6﴾

Transliteration: Alam tara kayfa faAAala rabbuka biAAadin

Translation: Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba?

89:7

إِرَمَ ذَاتِ ٱلۡعِمَادِ ﴿7﴾

Transliteration: Irama thati alAAimadi

Translation: Iramawa mãsu sakon ƙĩrar jiki.

89:8

ٱلَّتِي لَمۡ يُخۡلَقۡ مِثۡلُهَا فِي ٱلۡبِلَٰدِ ﴿8﴾

Transliteration: Allatee lam yukhlaq mithluha fee albiladi

Translation: Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya).

89:9

وَثَمُودَ ٱلَّذِينَ جَابُواْ ٱلصَّخۡرَ بِٱلۡوَادِ ﴿9﴾

Transliteration: Wathamooda allatheena jaboo alssakhra bialwadi

Translation: Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi suka yi gidãje)?

89:10

وَفِرۡعَوۡنَ ذِي ٱلۡأَوۡتَادِ ﴿10﴾

Transliteration: WafirAAawna thee alawtadi

Translation: Da Fir'auna mai turãku.

89:11

ٱلَّذِينَ طَغَوۡاْ فِي ٱلۡبِلَٰدِ ﴿11﴾

Transliteration: Allatheena taghaw fee albiladi

Translation: Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa?

89:12

فَأَكۡثَرُواْ فِيهَا ٱلۡفَسَادَ ﴿12﴾

Transliteration: Faaktharoo feeha alfasada

Translation: Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu.

89:13

فَصَبَّ عَلَيۡهِمۡ رَبُّكَ سَوۡطَ عَذَابٍ ﴿13﴾

Transliteration: Fasabba AAalayhim rabbuka sawta AAathabin

Translation: Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba.

89:14

إِنَّ رَبَّكَ لَبِٱلۡمِرۡصَادِ ﴿14﴾

Transliteration: Inna rabbaka labialmirsadi

Translation: Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka.

89:15

فَأَمَّا ٱلۡإِنسَٰنُ إِذَا مَا ٱبۡتَلَىٰهُ رَبُّهُۥ فَأَكۡرَمَهُۥ وَنَعَّمَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّيٓ أَكۡرَمَنِ ﴿15﴾

Transliteration: Faamma alinsanu itha ma ibtalahu rabbuhu faakramahu wanaAAAAamahu fayaqoolu rabbee akramani

Translation: To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni."

89:16

وَأَمَّآ إِذَا مَا ٱبۡتَلَىٰهُ فَقَدَرَ عَلَيۡهِ رِزۡقَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّيٓ أَهَٰنَنِ ﴿16﴾

Transliteration: Waamma itha ma ibtalahu faqadara AAalayhi rizqahu fayaqoolu rabbee ahanani

Translation: Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni."

89:17

كَلَّاۖ بَل لَّا تُكۡرِمُونَ ٱلۡيَتِيمَ ﴿17﴾

Transliteration: Kalla bal la tukrimoona alyateema

Translation: A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya!

89:18

وَلَا تَحَـٰٓضُّونَ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلۡمِسۡكِينِ ﴿18﴾

Transliteration: Wala tahaddoona AAala taAAami almiskeeni

Translation: Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci!

89:19

وَتَأۡكُلُونَ ٱلتُّرَاثَ أَكۡلٗا لَّمّٗا ﴿19﴾

Transliteration: Watakuloona altturatha aklan lamman

Translation: Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa.

89:20

وَتُحِبُّونَ ٱلۡمَالَ حُبّٗا جَمّٗا ﴿20﴾

Transliteration: Watuhibboona almala hubban jamman

Translation: Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa.

89:21

كَلَّآۖ إِذَا دُكَّتِ ٱلۡأَرۡضُ دَكّٗا دَكّٗا ﴿21﴾

Transliteration: Kalla itha dukkati alardu dakkan dakkan

Translation: A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai.

89:22

وَجَآءَ رَبُّكَ وَٱلۡمَلَكُ صَفّٗا صَفّٗا ﴿22﴾

Transliteration: Wajaa rabbuka waalmalaku saffan saffan

Translation: Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, sahu- sahu.

89:23

وَجِاْيٓءَ يَوۡمَئِذِۭ بِجَهَنَّمَۚ يَوۡمَئِذٖ يَتَذَكَّرُ ٱلۡإِنسَٰنُ وَأَنَّىٰ لَهُ ٱلذِّكۡرَىٰ ﴿23﴾

Transliteration: Wajeea yawmaithin bijahannama yawmaithin yatathakkaru alinsanu waanna lahu alththikra

Translation: Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi!

89:24

يَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي قَدَّمۡتُ لِحَيَاتِي ﴿24﴾

Transliteration: Yaqoolu ya laytanee qaddamtu lihayatee

Translation: Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!"

89:25

فَيَوۡمَئِذٖ لَّا يُعَذِّبُ عَذَابَهُۥٓ أَحَدٞ ﴿25﴾

Transliteration: Fayawmaithin la yuAAaththibu AAathabahu ahadun

Translation: To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah.

89:26

وَلَا يُوثِقُ وَثَاقَهُۥٓ أَحَدٞ ﴿26﴾

Transliteration: Wala yoothiqu wathaqahu ahadun

Translation: Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurin Sa.

89:27

يَـٰٓأَيَّتُهَا ٱلنَّفۡسُ ٱلۡمُطۡمَئِنَّةُ ﴿27﴾

Transliteration: Ya ayyatuha alnnafsu almutmainnatu

Translation: Yã kai rai mai natsuwa!

89:28

ٱرۡجِعِيٓ إِلَىٰ رَبِّكِ رَاضِيَةٗ مَّرۡضِيَّةٗ ﴿28﴾

Transliteration: IrjiAAee ila rabbiki radiyatan mardiyyatan

Translation: Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira).

89:29

فَٱدۡخُلِي فِي عِبَٰدِي ﴿29﴾

Transliteration: Faodkhulee fee AAibadee

Translation: Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyi Na (mãsu bin umurui a dũniya).

89:30

وَٱدۡخُلِي جَنَّتِي ﴿30﴾

Transliteration: Waodkhulee jannatee

Translation: Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira).

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download