quranm◉

Surah As-Saffat transliteration

◉ Sura · ∞

37:1

وَٱلصَّـٰٓفَّـٰتِ صَفّٗا ﴿1﴾

Transliteration: Waalssaffati saffan

Translation: Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi).

37:2

فَٱلزَّـٰجِرَٰتِ زَجۡرٗا ﴿2﴾

Transliteration: Faalzzajirati zajran

Translation: Sa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi.

37:3

فَٱلتَّـٰلِيَٰتِ ذِكۡرًا ﴿3﴾

Transliteration: Faalttaliyati thikran

Translation: Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa.

37:4

إِنَّ إِلَٰهَكُمۡ لَوَٰحِدٞ ﴿4﴾

Transliteration: Inna ilahakum lawahidun

Translation: Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne.

37:5

رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا وَرَبُّ ٱلۡمَشَٰرِقِ ﴿5﴾

Transliteration: Rabbu alssamawati waalardi wama baynahuma warabbu almashariqi

Translation: Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã.

37:6

إِنَّا زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنۡيَا بِزِينَةٍ ٱلۡكَوَاكِبِ ﴿6﴾

Transliteration: Inna zayyanna alssamaa alddunya bizeenatin alkawakibi

Translation: Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri.

37:7

وَحِفۡظٗا مِّن كُلِّ شَيۡطَٰنٖ مَّارِدٖ ﴿7﴾

Transliteration: Wahifthan min kulli shaytanin maridin

Translation: Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai.

37:8

لَّا يَسَّمَّعُونَ إِلَى ٱلۡمَلَإِ ٱلۡأَعۡلَىٰ وَيُقۡذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٖ ﴿8﴾

Transliteration: La yassammaAAoona ila almalai alaAAla wayuqthafoona min kulli janibin

Translation: Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe.

37:9

دُحُورٗاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٞ وَاصِبٌ ﴿9﴾

Transliteration: Duhooran walahum AAathabun wasibun

Translation: Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya.

37:10

إِلَّا مَنۡ خَطِفَ ٱلۡخَطۡفَةَ فَأَتۡبَعَهُۥ شِهَابٞ ثَاقِبٞ ﴿10﴾

Transliteration: Illa man khatifa alkhatfata faatbaAAahu shihabun thaqibun

Translation: Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi.

37:11

فَٱسۡتَفۡتِهِمۡ أَهُمۡ أَشَدُّ خَلۡقًا أَم مَّنۡ خَلَقۡنَآۚ إِنَّا خَلَقۡنَٰهُم مِّن طِينٖ لَّازِبِۭ ﴿11﴾

Transliteration: Faistaftihim ahum ashaddu khalqan am man khalaqna inna khalaqnahum min teenin lazibin

Translation: Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri.

37:12

بَلۡ عَجِبۡتَ وَيَسۡخَرُونَ ﴿12﴾

Transliteration: Bal AAajibta wayaskharoona

Translation: Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili.

37:13

وَإِذَا ذُكِّرُواْ لَا يَذۡكُرُونَ ﴿13﴾

Transliteration: Waitha thukkiroo la yathkuroona

Translation: Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa.

37:14

وَإِذَا رَأَوۡاْ ءَايَةٗ يَسۡتَسۡخِرُونَ ﴿14﴾

Transliteration: Waitha raaw ayatan yastaskhiroona

Translation: Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili.

37:15

وَقَالُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٌ ﴿15﴾

Transliteration: Waqaloo in hatha illa sihrun mubeenun

Translation: Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne."

37:16

أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ ﴿16﴾

Transliteration: Aitha mitna wakunna turaban waAAithaman ainna lamabAAoothoona

Translation: "Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne?

37:17

أَوَءَابَآؤُنَا ٱلۡأَوَّلُونَ ﴿17﴾

Transliteration: Awaabaona alawwaloona

Translation: "Ashe kõ da ubanninmu na farko?"

37:18

قُلۡ نَعَمۡ وَأَنتُمۡ دَٰخِرُونَ ﴿18﴾

Transliteration: Qul naAAam waantum dakhiroona

Translation: Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu."

37:19

فَإِنَّمَا هِيَ زَجۡرَةٞ وَٰحِدَةٞ فَإِذَا هُمۡ يَنظُرُونَ ﴿19﴾

Transliteration: Fainnama hiya zajratun wahidatun faitha hum yanthuroona

Translation: Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi.

37:20

وَقَالُواْ يَٰوَيۡلَنَا هَٰذَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ ﴿20﴾

Transliteration: Waqaloo ya waylana hatha yawmu alddeeni

Translation: Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako."

37:21

هَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ ﴿21﴾

Transliteration: Hatha yawmu alfasli allathee kuntum bihi tukaththiboona

Translation: Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa.

37:22

ٱحۡشُرُواْ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ وَأَزۡوَٰجَهُمۡ وَمَا كَانُواْ يَعۡبُدُونَ ﴿22﴾

Transliteration: Ohshuroo allatheena thalamoo waazwajahum wama kanoo yaAAbudoona

Translation: Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa.

37:23

مِن دُونِ ٱللَّهِ فَٱهۡدُوهُمۡ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡجَحِيمِ ﴿23﴾

Transliteration: Min dooni Allahi faihdoohum ila sirati aljaheemi

Translation: Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm.

37:24

وَقِفُوهُمۡۖ إِنَّهُم مَّسۡـُٔولُونَ ﴿24﴾

Transliteration: Waqifoohum innahum masooloona

Translation: Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne.

37:25

مَا لَكُمۡ لَا تَنَاصَرُونَ ﴿25﴾

Transliteration: Ma lakum la tanasaroona

Translation: Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?

37:26

بَلۡ هُمُ ٱلۡيَوۡمَ مُسۡتَسۡلِمُونَ ﴿26﴾

Transliteration: Bal humu alyawma mustaslimoona

Translation: Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.

37:27

وَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ يَتَسَآءَلُونَ ﴿27﴾

Transliteration: Waaqbala baAAduhum AAala baAAdin yatasaaloona

Translation: Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.

37:28

قَالُوٓاْ إِنَّكُمۡ كُنتُمۡ تَأۡتُونَنَا عَنِ ٱلۡيَمِينِ ﴿28﴾

Transliteration: Qaloo innakum kuntum tatoonana AAani alyameeni

Translation: Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)."

37:29

قَالُواْ بَل لَّمۡ تَكُونُواْ مُؤۡمِنِينَ ﴿29﴾

Transliteration: Qaloo bal lam takoonoo mumineena

Translation: Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba.

37:30

وَمَا كَانَ لَنَا عَلَيۡكُم مِّن سُلۡطَٰنِۭۖ بَلۡ كُنتُمۡ قَوۡمٗا طَٰغِينَ ﴿30﴾

Transliteration: Wama kana lana AAalaykum min sultanin bal kuntum qawman tagheena

Translation: "Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka."

37:31

فَحَقَّ عَلَيۡنَا قَوۡلُ رَبِّنَآۖ إِنَّا لَذَآئِقُونَ ﴿31﴾

Transliteration: Fahaqqa AAalayna qawlu rabbina inna lathaiqoona

Translation: "Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne."

37:32

فَأَغۡوَيۡنَٰكُمۡ إِنَّا كُنَّا غَٰوِينَ ﴿32﴾

Transliteration: Faaghwaynakum inna kunna ghaweena

Translation: "Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu."

37:33

فَإِنَّهُمۡ يَوۡمَئِذٖ فِي ٱلۡعَذَابِ مُشۡتَرِكُونَ ﴿33﴾

Transliteration: Fainnahum yawmaithin fee alAAathabi mushtarikoona

Translation: To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.

37:34

إِنَّا كَذَٰلِكَ نَفۡعَلُ بِٱلۡمُجۡرِمِينَ ﴿34﴾

Transliteration: Inna kathalika nafAAalu bialmujrimeena

Translation: Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.

37:35

إِنَّهُمۡ كَانُوٓاْ إِذَا قِيلَ لَهُمۡ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ يَسۡتَكۡبِرُونَ ﴿35﴾

Transliteration: Innahum kanoo itha qeela lahum la ilaha illa Allahu yastakbiroona

Translation: Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai.

37:36

وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُوٓاْ ءَالِهَتِنَا لِشَاعِرٖ مَّجۡنُونِۭ ﴿36﴾

Transliteration: Wayaqooloona ainna latarikoo alihatina lishaAAirin majnoonin

Translation: Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?

37:37

بَلۡ جَآءَ بِٱلۡحَقِّ وَصَدَّقَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ﴿37﴾

Transliteration: Bal jaa bialhaqqi wasaddaqa almursaleena

Translation: Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.

37:38

إِنَّكُمۡ لَذَآئِقُواْ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡأَلِيمِ ﴿38﴾

Transliteration: Innakum lathaiqoo alAAathabi alaleemi

Translation: Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.

37:39

وَمَا تُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ ﴿39﴾

Transliteration: Wama tujzawna illa ma kuntum taAAmaloona

Translation: Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.

37:40

إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ ﴿40﴾

Transliteration: Illa AAibada Allahi almukhlaseena

Translation: Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

37:41

أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ رِزۡقٞ مَّعۡلُومٞ ﴿41﴾

Transliteration: Olaika lahum rizqun maAAloomun

Translation: Waɗannan sunã da abinci sananne.

37:42

فَوَٰكِهُ وَهُم مُّكۡرَمُونَ ﴿42﴾

Transliteration: Fawakihu wahum mukramoona

Translation: Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.

37:43

فِي جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ ﴿43﴾

Transliteration: Fee jannati alnnaAAeemi

Translation: A cikin gidãjen Aljannar ni'ima.

37:44

عَلَىٰ سُرُرٖ مُّتَقَٰبِلِينَ ﴿44﴾

Transliteration: AAala sururin mutaqabileena

Translation: A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.

37:45

يُطَافُ عَلَيۡهِم بِكَأۡسٖ مِّن مَّعِينِۭ ﴿45﴾

Transliteration: Yutafu AAalayhim bikasin min maAAeenin

Translation: Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.

37:46

بَيۡضَآءَ لَذَّةٖ لِّلشَّـٰرِبِينَ ﴿46﴾

Transliteration: Baydaa laththatin lilshsharibeena

Translation: Farã mai dãɗi ga mashãyan.

37:47

لَا فِيهَا غَوۡلٞ وَلَا هُمۡ عَنۡهَا يُنزَفُونَ ﴿47﴾

Transliteration: La feeha ghawlun wala hum AAanha yunzafoona

Translation: A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,

37:48

وَعِندَهُمۡ قَٰصِرَٰتُ ٱلطَّرۡفِ عِينٞ ﴿48﴾

Transliteration: WaAAindahum qasiratu alttarfi AAeenun

Translation: Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.

37:49

كَأَنَّهُنَّ بَيۡضٞ مَّكۡنُونٞ ﴿49﴾

Transliteration: Kaannahunna baydun maknoonun

Translation: Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.

37:50

فَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ يَتَسَآءَلُونَ ﴿50﴾

Transliteration: Faaqbala baAAduhum AAala baAAdin yatasaaloona

Translation: Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.

37:51

قَالَ قَآئِلٞ مِّنۡهُمۡ إِنِّي كَانَ لِي قَرِينٞ ﴿51﴾

Transliteration: Qala qailun minhum innee kana lee qareenun

Translation: Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)."

37:52

يَقُولُ أَءِنَّكَ لَمِنَ ٱلۡمُصَدِّقِينَ ﴿52﴾

Transliteration: Yaqoolu ainnaka lamina almusaddiqeena

Translation: Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?"

37:53

أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَدِينُونَ ﴿53﴾

Transliteration: Aitha mitna wakunna turaban waAAithaman ainna lamadeenoona

Translation: "Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?"

37:54

قَالَ هَلۡ أَنتُم مُّطَّلِعُونَ ﴿54﴾

Transliteration: Qala hal antum muttaliAAoona

Translation: (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?"

37:55

فَٱطَّلَعَ فَرَءَاهُ فِي سَوَآءِ ٱلۡجَحِيمِ ﴿55﴾

Transliteration: FaittalaAAa faraahu fee sawai aljaheemi

Translation: Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim.

37:56

قَالَ تَٱللَّهِ إِن كِدتَّ لَتُرۡدِينِ ﴿56﴾

Transliteration: Qala taAllahi in kidta laturdeeni

Translation: Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni."

37:57

وَلَوۡلَا نِعۡمَةُ رَبِّي لَكُنتُ مِنَ ٱلۡمُحۡضَرِينَ ﴿57﴾

Transliteration: Walawla niAAmatu rabbee lakuntu mina almuhdareena

Translation: "Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)."

37:58

أَفَمَا نَحۡنُ بِمَيِّتِينَ ﴿58﴾

Transliteration: Afama nahnu bimayyiteena

Translation: "Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba."

37:59

إِلَّا مَوۡتَتَنَا ٱلۡأُولَىٰ وَمَا نَحۡنُ بِمُعَذَّبِينَ ﴿59﴾

Transliteration: Illa mawtatana aloola wama nahnu bimuAAaththabeena

Translation: "Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?"

37:60

إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ ﴿60﴾

Transliteration: Inna hatha lahuwa alfawzu alAAatheemu

Translation: Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma.

37:61

لِمِثۡلِ هَٰذَا فَلۡيَعۡمَلِ ٱلۡعَٰمِلُونَ ﴿61﴾

Transliteration: Limithli hatha falyaAAmali alAAamiloona

Translation: Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa.

37:62

أَذَٰلِكَ خَيۡرٞ نُّزُلًا أَمۡ شَجَرَةُ ٱلزَّقُّومِ ﴿62﴾

Transliteration: Athalika khayrun nuzulan am shajaratu alzzaqqoomi

Translation: Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm?

37:63

إِنَّا جَعَلۡنَٰهَا فِتۡنَةٗ لِّلظَّـٰلِمِينَ ﴿63﴾

Transliteration: Inna jaAAalnaha fitnatan lilththalimeena

Translation: Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai.

37:64

إِنَّهَا شَجَرَةٞ تَخۡرُجُ فِيٓ أَصۡلِ ٱلۡجَحِيمِ ﴿64﴾

Transliteration: Innaha shajaratun takhruju fee asli aljaheemi

Translation: Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm.

37:65

طَلۡعُهَا كَأَنَّهُۥ رُءُوسُ ٱلشَّيَٰطِينِ ﴿65﴾

Transliteration: TalAAuha kaannahu ruoosu alshshayateeni

Translation: Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne.

37:66

فَإِنَّهُمۡ لَأٓكِلُونَ مِنۡهَا فَمَالِـُٔونَ مِنۡهَا ٱلۡبُطُونَ ﴿66﴾

Transliteration: Fainnahum laakiloona minha famalioona minha albutoona

Translation: To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta.

37:67

ثُمَّ إِنَّ لَهُمۡ عَلَيۡهَا لَشَوۡبٗا مِّنۡ حَمِيمٖ ﴿67﴾

Transliteration: Thumma inna lahum AAalayha lashawban min hameemin

Translation: Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi.

37:68

ثُمَّ إِنَّ مَرۡجِعَهُمۡ لَإِلَى ٱلۡجَحِيمِ ﴿68﴾

Transliteration: Thumma inna marjiAAahum laila aljaheemi

Translation: Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take.

37:69

إِنَّهُمۡ أَلۡفَوۡاْ ءَابَآءَهُمۡ ضَآلِّينَ ﴿69﴾

Transliteration: Innahum alfaw abaahum dalleena

Translation: Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu.

37:70

فَهُمۡ عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِمۡ يُهۡرَعُونَ ﴿70﴾

Transliteration: Fahum AAala atharihim yuhraAAoona

Translation: Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa.

37:71

وَلَقَدۡ ضَلَّ قَبۡلَهُمۡ أَكۡثَرُ ٱلۡأَوَّلِينَ ﴿71﴾

Transliteration: Walaqad dalla qablahum aktharu alawwaleena

Translation: Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu.

37:72

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا فِيهِم مُّنذِرِينَ ﴿72﴾

Transliteration: Walaqad arsalna feehim munthireena

Translation: Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu.

37:73

فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُنذَرِينَ ﴿73﴾

Transliteration: Faonthur kayfa kana AAaqibatu almunthareena

Translation: Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance.

37:74

إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ ﴿74﴾

Transliteration: Illa AAibada Allahi almukhlaseena

Translation: Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

37:75

وَلَقَدۡ نَادَىٰنَا نُوحٞ فَلَنِعۡمَ ٱلۡمُجِيبُونَ ﴿75﴾

Transliteration: Walaqad nadana noohun falaniAAma almujeeboona

Translation: Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu.

37:76

وَنَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥ مِنَ ٱلۡكَرۡبِ ٱلۡعَظِيمِ ﴿76﴾

Transliteration: Wanajjaynahu waahlahu mina alkarbi alAAatheemi

Translation: Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba.

37:77

وَجَعَلۡنَا ذُرِّيَّتَهُۥ هُمُ ٱلۡبَاقِينَ ﴿77﴾

Transliteration: WajaAAalna thurriyyatahu humu albaqeena

Translation: Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.

37:78

وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ ﴿78﴾

Transliteration: Watarakna AAalayhi fee alakhireena

Translation: Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe.

37:79

سَلَٰمٌ عَلَىٰ نُوحٖ فِي ٱلۡعَٰلَمِينَ ﴿79﴾

Transliteration: Salamun AAala noohin fee alAAalameena

Translation: Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.

37:80

إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ ﴿80﴾

Transliteration: Inna kathalika najzee almuhsineena

Translation: Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

37:81

إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ﴿81﴾

Transliteration: Innahu min AAibadina almumineena

Translation: Lalle shi, yanã daga bãyin Mu mũminai.

37:82

ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ ﴿82﴾

Transliteration: Thumma aghraqna alakhareena

Translation: Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu.

37:83

وَإِنَّ مِن شِيعَتِهِۦ لَإِبۡرَٰهِيمَ ﴿83﴾

Transliteration: Wainna min sheeAAatihi laibraheema

Translation: Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.

37:84

إِذۡ جَآءَ رَبَّهُۥ بِقَلۡبٖ سَلِيمٍ ﴿84﴾

Transliteration: Ith jaa rabbahu biqalbin saleemin

Translation: A lõkacin da ya je wa ubangijinsa da zũciya kuɓutacciya.

37:85

إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦ مَاذَا تَعۡبُدُونَ ﴿85﴾

Transliteration: Ith qala liabeehi waqawmihi matha taAAbudoona

Translation: A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?"

37:86

أَئِفۡكًا ءَالِهَةٗ دُونَ ٱللَّهِ تُرِيدُونَ ﴿86﴾

Transliteration: Aifkan alihatan doona Allahi tureedoona

Translation: "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?"

37:87

فَمَا ظَنُّكُم بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ﴿87﴾

Transliteration: Fama thannukum birabbi alAAalameena

Translation: "To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?"

37:88

فَنَظَرَ نَظۡرَةٗ فِي ٱلنُّجُومِ ﴿88﴾

Transliteration: Fanathara nathratan fee alnnujoomi

Translation: Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.

37:89

فَقَالَ إِنِّي سَقِيمٞ ﴿89﴾

Transliteration: Faqala innee saqeemun

Translation: Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne."

37:90

فَتَوَلَّوۡاْ عَنۡهُ مُدۡبِرِينَ ﴿90﴾

Transliteration: Fatawallaw AAanhu mudbireena

Translation: Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.

37:91

فَرَاغَ إِلَىٰٓ ءَالِهَتِهِمۡ فَقَالَ أَلَا تَأۡكُلُونَ ﴿91﴾

Transliteration: Faragha ila alihatihim faqala ala takuloona

Translation: Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba?

37:92

مَا لَكُمۡ لَا تَنطِقُونَ ﴿92﴾

Transliteration: Ma lakum la tantiqoona

Translation: "Me ya sãme ku, bã ku magana?"

37:93

فَرَاغَ عَلَيۡهِمۡ ضَرۡبَۢا بِٱلۡيَمِينِ ﴿93﴾

Transliteration: Faragha AAalayhim darban bialyameeni

Translation: Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.

37:94

فَأَقۡبَلُوٓاْ إِلَيۡهِ يَزِفُّونَ ﴿94﴾

Transliteration: Faaqbaloo ilayhi yaziffoona

Translation: Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.

37:95

قَالَ أَتَعۡبُدُونَ مَا تَنۡحِتُونَ ﴿95﴾

Transliteration: Qala ataAAbudoona ma tanhitoona

Translation: Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,

37:96

وَٱللَّهُ خَلَقَكُمۡ وَمَا تَعۡمَلُونَ ﴿96﴾

Transliteration: WaAllahu khalaqakum wama taAAmaloona

Translation: "Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"

37:97

قَالُواْ ٱبۡنُواْ لَهُۥ بُنۡيَٰنٗا فَأَلۡقُوهُ فِي ٱلۡجَحِيمِ ﴿97﴾

Transliteration: Qaloo ibnoo lahu bunyanan faalqoohu fee aljaheemi

Translation: Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm."

37:98

فَأَرَادُواْ بِهِۦ كَيۡدٗا فَجَعَلۡنَٰهُمُ ٱلۡأَسۡفَلِينَ ﴿98﴾

Transliteration: Faaradoo bihi kaydan fajaAAalnahumu alasfaleena

Translation: Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.

37:99

وَقَالَ إِنِّي ذَاهِبٌ إِلَىٰ رَبِّي سَيَهۡدِينِ ﴿99﴾

Transliteration: Waqala innee thahibun ila rabbee sayahdeeni

Translation: Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."

37:100

رَبِّ هَبۡ لِي مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ ﴿100﴾

Transliteration: Rabbi hab lee mina alssaliheena

Translation: "Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne."

37:101

فَبَشَّرۡنَٰهُ بِغُلَٰمٍ حَلِيمٖ ﴿101﴾

Transliteration: Fabashsharnahu bighulamin haleemin

Translation: Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri.

37:102

فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ ٱلسَّعۡيَ قَالَ يَٰبُنَيَّ إِنِّيٓ أَرَىٰ فِي ٱلۡمَنَامِ أَنِّيٓ أَذۡبَحُكَ فَٱنظُرۡ مَاذَا تَرَىٰۚ قَالَ يَـٰٓأَبَتِ ٱفۡعَلۡ مَا تُؤۡمَرُۖ سَتَجِدُنِيٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلصَّـٰبِرِينَ ﴿102﴾

Transliteration: Falamma balagha maAAahu alssaAAya qala ya bunayya innee ara fee almanami annee athbahuka faonthur matha tara qala ya abati ifAAal ma tumaru satajidunee in shaa Allahu mina alssabireena

Translation: To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri."

37:103

فَلَمَّآ أَسۡلَمَا وَتَلَّهُۥ لِلۡجَبِينِ ﴿103﴾

Transliteration: Falamma aslama watallahu liljabeeni

Translation: Yayin da suka mika wuya sai muka fansheshi da Rago

37:104

وَنَٰدَيۡنَٰهُ أَن يَـٰٓإِبۡرَٰهِيمُ ﴿104﴾

Transliteration: Wanadaynahu an ya ibraheemu

Translation: Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!"

37:105

قَدۡ صَدَّقۡتَ ٱلرُّءۡيَآۚ إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ ﴿105﴾

Transliteration: Qad saddaqta alrruya inna kathalika najzee almuhsineena

Translation: "Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

37:106

إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡبَلَـٰٓؤُاْ ٱلۡمُبِينُ ﴿106﴾

Transliteration: Inna hatha lahuwa albalao almubeenu

Translation: Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna.

37:107

وَفَدَيۡنَٰهُ بِذِبۡحٍ عَظِيمٖ ﴿107﴾

Transliteration: Wafadaynahu bithibhin AAatheemin

Translation: Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma.

37:108

وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ ﴿108﴾

Transliteration: Watarakna AAalayhi fee alakhireena

Translation: Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe.

37:109

سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ ﴿109﴾

Transliteration: Salamun AAala ibraheema

Translation: Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm.

37:110

كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ ﴿110﴾

Transliteration: Kathalika najzee almuhsineena

Translation: Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

37:111

إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ﴿111﴾

Transliteration: Innahu min AAibadina almumineena

Translation: Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai.

37:112

وَبَشَّرۡنَٰهُ بِإِسۡحَٰقَ نَبِيّٗا مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ ﴿112﴾

Transliteration: Wabashsharnahu biishaqa nabiyyan mina alssaliheena

Translation: Kuma Muka yi masa bushãra Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne.

37:113

وَبَٰرَكۡنَا عَلَيۡهِ وَعَلَىٰٓ إِسۡحَٰقَۚ وَمِن ذُرِّيَّتِهِمَا مُحۡسِنٞ وَظَالِمٞ لِّنَفۡسِهِۦ مُبِينٞ ﴿113﴾

Transliteration: Wabarakna AAalayhi waAAala ishaqa wamin thurriyyatihima muhsinun wathalimun linafsihi mubeenun

Translation: Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin).

37:114

وَلَقَدۡ مَنَنَّا عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ ﴿114﴾

Transliteration: Walaqad mananna AAala moosa waharoona

Translation: Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna.

37:115

وَنَجَّيۡنَٰهُمَا وَقَوۡمَهُمَا مِنَ ٱلۡكَرۡبِ ٱلۡعَظِيمِ ﴿115﴾

Transliteration: Wanajjaynahuma waqawmahuma mina alkarbi alAAatheemi

Translation: Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma.

37:116

وَنَصَرۡنَٰهُمۡ فَكَانُواْ هُمُ ٱلۡغَٰلِبِينَ ﴿116﴾

Transliteration: Wanasarnahum fakanoo humu alghalibeena

Translation: Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya.

37:117

وَءَاتَيۡنَٰهُمَا ٱلۡكِتَٰبَ ٱلۡمُسۡتَبِينَ ﴿117﴾

Transliteration: Waataynahuma alkitaba almustabeena

Translation: Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni.

37:118

وَهَدَيۡنَٰهُمَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ ﴿118﴾

Transliteration: Wahadaynahuma alssirata almustaqeema

Translation: Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya.

37:119

وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِمَا فِي ٱلۡأٓخِرِينَ ﴿119﴾

Transliteration: Watarakna AAalayhima fee alakhireena

Translation: Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe.

37:120

سَلَٰمٌ عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ ﴿120﴾

Transliteration: Salamun AAala moosa waharoona

Translation: Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna.

37:121

إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ ﴿121﴾

Transliteration: Inna kathalika najzee almuhsineena

Translation: Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

37:122

إِنَّهُمَا مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ﴿122﴾

Transliteration: Innahuma min AAibadina almumineena

Translation: Lalle, sunã daga bãyin Mu mũminai.

37:123

وَإِنَّ إِلۡيَاسَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ﴿123﴾

Transliteration: Wainna ilyasa lamina almursaleena

Translation: Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.

37:124

إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦٓ أَلَا تَتَّقُونَ ﴿124﴾

Transliteration: Ith qala liqawmihi ala tattaqoona

Translation: A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?"

37:125

أَتَدۡعُونَ بَعۡلٗا وَتَذَرُونَ أَحۡسَنَ ٱلۡخَٰلِقِينَ ﴿125﴾

Transliteration: AtadAAoona baAAlan watatharoona ahsana alkhaliqeena

Translation: "Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?"

37:126

ٱللَّهَ رَبَّكُمۡ وَرَبَّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ ﴿126﴾

Transliteration: Allaha rabbakum warabba abaikumu alawwaleena

Translation: "Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?"

37:127

فَكَذَّبُوهُ فَإِنَّهُمۡ لَمُحۡضَرُونَ ﴿127﴾

Transliteration: Fakaththaboohu fainnahum lamuhdaroona

Translation: Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã).

37:128

إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ ﴿128﴾

Transliteration: Illa AAibada Allahi almukhlaseena

Translation: Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

37:129

وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ ﴿129﴾

Transliteration: Watarakna AAalayhi fee alakhireena

Translation: Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe.

37:130

سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِلۡ يَاسِينَ ﴿130﴾

Transliteration: Salamun AAala il yaseena

Translation: Aminci ya tabbata ga Ilyãs.

37:131

إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ ﴿131﴾

Transliteration: Inna kathalika najzee almuhsineena

Translation: Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.

37:132

إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ﴿132﴾

Transliteration: Innahu min AAibadina almumineena

Translation: Lalle shĩ, yanã daga bãyin Mu mũminai.

37:133

وَإِنَّ لُوطٗا لَّمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ﴿133﴾

Transliteration: Wainna lootan lamina almursaleena

Translation: Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.

37:134

إِذۡ نَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ ﴿134﴾

Transliteration: Ith najjaynahu waahlahu ajmaAAeena

Translation: A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya.

37:135

إِلَّا عَجُوزٗا فِي ٱلۡغَٰبِرِينَ ﴿135﴾

Transliteration: Illa AAajoozan fee alghabireena

Translation: Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba).

37:136

ثُمَّ دَمَّرۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ ﴿136﴾

Transliteration: Thumma dammarna alakhareena

Translation: Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen.

37:137

وَإِنَّكُمۡ لَتَمُرُّونَ عَلَيۡهِم مُّصۡبِحِينَ ﴿137﴾

Transliteration: Wainnakum latamurroona AAalayhim musbiheena

Translation: Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci.

37:138

وَبِٱلَّيۡلِۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ ﴿138﴾

Transliteration: Wabiallayli afala taAAqiloona

Translation: Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba?

37:139

وَإِنَّ يُونُسَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ﴿139﴾

Transliteration: Wainna yoonusa lamina almursaleena

Translation: Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni.

37:140

إِذۡ أَبَقَ إِلَى ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ ﴿140﴾

Transliteration: Ith abaqa ila alfulki almashhooni

Translation: A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi.

37:141

فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنَ ٱلۡمُدۡحَضِينَ ﴿141﴾

Transliteration: Fasahama fakana mina almudhadeena

Translation: Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya.

37:142

فَٱلۡتَقَمَهُ ٱلۡحُوتُ وَهُوَ مُلِيمٞ ﴿142﴾

Transliteration: Failtaqamahu alhootu wahuwa muleemun

Translation: Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi.

37:143

فَلَوۡلَآ أَنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلۡمُسَبِّحِينَ ﴿143﴾

Transliteration: Falawla annahu kana mina almusabbiheena

Translation: To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba,

37:144

لَلَبِثَ فِي بَطۡنِهِۦٓ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ ﴿144﴾

Transliteration: Lalabitha fee batnihi ila yawmi yubAAathoona

Translation: Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su.

37:145

فَنَبَذۡنَٰهُ بِٱلۡعَرَآءِ وَهُوَ سَقِيمٞ ﴿145﴾

Transliteration: Fanabathnahu bialAAarai wahuwa saqeemun

Translation: Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya.

37:146

وَأَنۢبَتۡنَا عَلَيۡهِ شَجَرَةٗ مِّن يَقۡطِينٖ ﴿146﴾

Transliteration: Waanbatna AAalayhi shajaratan min yaqteenin

Translation: Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi.

37:147

وَأَرۡسَلۡنَٰهُ إِلَىٰ مِاْئَةِ أَلۡفٍ أَوۡ يَزِيدُونَ ﴿147﴾

Transliteration: Waarsalnahu ila miati alfin aw yazeedoona

Translation: Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka).

37:148

فَـَٔامَنُواْ فَمَتَّعۡنَٰهُمۡ إِلَىٰ حِينٖ ﴿148﴾

Transliteration: Faamanoo famattaAAnahum ila heenin

Translation: Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci.

37:149

فَٱسۡتَفۡتِهِمۡ أَلِرَبِّكَ ٱلۡبَنَاتُ وَلَهُمُ ٱلۡبَنُونَ ﴿149﴾

Transliteration: Faistaftihim alirabbika albanatu walahumu albanoona

Translation: Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?"

37:150

أَمۡ خَلَقۡنَا ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ إِنَٰثٗا وَهُمۡ شَٰهِدُونَ ﴿150﴾

Transliteration: Am khalaqna almalaikata inathan wahum shahidoona

Translation: Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce?

37:151

أَلَآ إِنَّهُم مِّنۡ إِفۡكِهِمۡ لَيَقُولُونَ ﴿151﴾

Transliteration: Ala innahum min ifkihim layaqooloona

Translation: To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa.

37:152

وَلَدَ ٱللَّهُ وَإِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ ﴿152﴾

Transliteration: Walada Allahu wainnahum lakathiboona

Translation: "Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne.

37:153

أَصۡطَفَى ٱلۡبَنَاتِ عَلَى ٱلۡبَنِينَ ﴿153﴾

Transliteration: Astafa albanati AAala albaneena

Translation: Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza?

37:154

مَا لَكُمۡ كَيۡفَ تَحۡكُمُونَ ﴿154﴾

Transliteration: Ma lakum kayfa tahkumoona

Translation: Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannan hukunci)?

37:155

أَفَلَا تَذَكَّرُونَ ﴿155﴾

Transliteration: Afala tathakkaroona

Translation: Shin, bã ku tunãni?

37:156

أَمۡ لَكُمۡ سُلۡطَٰنٞ مُّبِينٞ ﴿156﴾

Transliteration: Am lakum sultanun mubeenun

Translation: Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?

37:157

فَأۡتُواْ بِكِتَٰبِكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ ﴿157﴾

Transliteration: Fatoo bikitabikum in kuntum sadiqeena

Translation: To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.

37:158

وَجَعَلُواْ بَيۡنَهُۥ وَبَيۡنَ ٱلۡجِنَّةِ نَسَبٗاۚ وَلَقَدۡ عَلِمَتِ ٱلۡجِنَّةُ إِنَّهُمۡ لَمُحۡضَرُونَ ﴿158﴾

Transliteration: WajaAAaloo baynahu wabayna aljinnati nasaban walaqad AAalimati aljinnatu innahum lamuhdaroona

Translation: Kuma suka sanya nasaba a tsakãnin Sa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)"

37:159

سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ ﴿159﴾

Transliteration: Subhana Allahi AAamma yasifoona

Translation: Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.

37:160

إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ ﴿160﴾

Transliteration: Illa AAibada Allahi almukhlaseena

Translation: Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.

37:161

فَإِنَّكُمۡ وَمَا تَعۡبُدُونَ ﴿161﴾

Transliteration: Fainnakum wama taAAbudoona

Translation: To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,

37:162

مَآ أَنتُمۡ عَلَيۡهِ بِفَٰتِنِينَ ﴿162﴾

Transliteration: Ma antum AAalayhi bifatineena

Translation: Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.

37:163

إِلَّا مَنۡ هُوَ صَالِ ٱلۡجَحِيمِ ﴿163﴾

Transliteration: Illa man huwa sali aljaheemi

Translation: Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.

37:164

وَمَامِنَّآ إِلَّا لَهُۥ مَقَامٞ مَّعۡلُومٞ ﴿164﴾

Transliteration: Wama minna illa lahu maqamun maAAloomun

Translation: "Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne."

37:165

وَإِنَّا لَنَحۡنُ ٱلصَّآفُّونَ ﴿165﴾

Transliteration: Wainna lanahnu alssaffoona

Translation: "Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)."

37:166

وَإِنَّا لَنَحۡنُ ٱلۡمُسَبِّحُونَ ﴿166﴾

Transliteration: Wainna lanahnu almusabbihoona

Translation: "Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi."

37:167

وَإِن كَانُواْ لَيَقُولُونَ ﴿167﴾

Transliteration: Wain kanoo layaqooloona

Translation: Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa,

37:168

لَوۡ أَنَّ عِندَنَا ذِكۡرٗا مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ ﴿168﴾

Transliteration: Law anna AAindana thikran mina alawwaleena

Translation: "Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko."

37:169

لَكُنَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ ﴿169﴾

Transliteration: Lakunna AAibada Allahi almukhlaseena

Translation: "Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."

37:170

فَكَفَرُواْ بِهِۦۖ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ ﴿170﴾

Transliteration: Fakafaroo bihi fasawfa yaAAlamoona

Translation: Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.

37:171

وَلَقَدۡ سَبَقَتۡ كَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا ٱلۡمُرۡسَلِينَ ﴿171﴾

Transliteration: Walaqad sabaqat kalimatuna liAAibadina almursaleena

Translation: Kuma lalle, haƙĩƙa kalmar Mu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.

37:172

إِنَّهُمۡ لَهُمُ ٱلۡمَنصُورُونَ ﴿172﴾

Transliteration: Innahum lahumu almansooroona

Translation: Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.

37:173

وَإِنَّ جُندَنَا لَهُمُ ٱلۡغَٰلِبُونَ ﴿173﴾

Transliteration: Wainna jundana lahumu alghaliboona

Translation: Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.

37:174

فَتَوَلَّ عَنۡهُمۡ حَتَّىٰ حِينٖ ﴿174﴾

Transliteration: Fatawalla AAanhum hatta heenin

Translation: Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.

37:175

وَأَبۡصِرۡهُمۡ فَسَوۡفَ يُبۡصِرُونَ ﴿175﴾

Transliteration: Waabsirhum fasawfa yubsiroona

Translation: Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.

37:176

أَفَبِعَذَابِنَا يَسۡتَعۡجِلُونَ ﴿176﴾

Transliteration: AfabiAAathabina yastaAAjiloona

Translation: Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?

37:177

فَإِذَا نَزَلَ بِسَاحَتِهِمۡ فَسَآءَ صَبَاحُ ٱلۡمُنذَرِينَ ﴿177﴾

Transliteration: Faitha nazala bisahatihim fasaa sabahu almunthareena

Translation: To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.

37:178

وَتَوَلَّ عَنۡهُمۡ حَتَّىٰ حِينٖ ﴿178﴾

Transliteration: Watawalla AAanhum hatta heenin

Translation: Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.

37:179

وَأَبۡصِرۡ فَسَوۡفَ يُبۡصِرُونَ ﴿179﴾

Transliteration: Waabsir fasawfa yubsiroona

Translation: Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.

37:180

سُبۡحَٰنَ رَبِّكَ رَبِّ ٱلۡعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ ﴿180﴾

Transliteration: Subhana rabbika rabbi alAAizzati AAamma yasifoona

Translation: Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.

37:181

وَسَلَٰمٌ عَلَى ٱلۡمُرۡسَلِينَ ﴿181﴾

Transliteration: Wasalamun AAala almursaleena

Translation: Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni.

37:182

وَٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ﴿182﴾

Transliteration: Waalhamdu lillahi rabbi alAAalameena

Translation: Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download