quranm◉

Surah An-Najm transliteration

◉ Sura · ∞

53:1

وَٱلنَّجۡمِ إِذَا هَوَىٰ ﴿1﴾

Transliteration: Waalnnajmi itha hawa

Translation: Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.

53:2

مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمۡ وَمَا غَوَىٰ ﴿2﴾

Transliteration: Ma dalla sahibukum wama ghawa

Translation: Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.

53:3

وَمَا يَنطِقُ عَنِ ٱلۡهَوَىٰٓ ﴿3﴾

Transliteration: Wama yantiqu AAani alhawa

Translation: Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.

53:4

إِنۡ هُوَ إِلَّا وَحۡيٞ يُوحَىٰ ﴿4﴾

Transliteration: In huwa illa wahyun yooha

Translation: (Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.

53:5

عَلَّمَهُۥ شَدِيدُ ٱلۡقُوَىٰ ﴿5﴾

Transliteration: AAallamahu shadeedu alquwa

Translation: (Malã'ika) mai tsananin ƙarfi ya sanar da shi.

53:6

ذُو مِرَّةٖ فَٱسۡتَوَىٰ ﴿6﴾

Transliteration: Thoo mirratin faistawa

Translation: Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.

53:7

وَهُوَ بِٱلۡأُفُقِ ٱلۡأَعۡلَىٰ ﴿7﴾

Transliteration: Wahuwa bialofuqi alaAAla

Translation: Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi daukaka.

53:8

ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّىٰ ﴿8﴾

Transliteration: Thumma dana fatadalla

Translation: Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.

53:9

فَكَانَ قَابَ قَوۡسَيۡنِ أَوۡ أَدۡنَىٰ ﴿9﴾

Transliteration: Fakana qaba qawsayni aw adna

Translation: Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.

53:10

فَأَوۡحَىٰٓ إِلَىٰ عَبۡدِهِۦ مَآ أَوۡحَىٰ ﴿10﴾

Transliteration: Faawha ila AAabdihi ma awha

Translation: Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa).

53:11

مَا كَذَبَ ٱلۡفُؤَادُ مَا رَأَىٰٓ ﴿11﴾

Transliteration: Ma kathaba alfuadu ma raa

Translation: Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba.

53:12

أَفَتُمَٰرُونَهُۥ عَلَىٰ مَا يَرَىٰ ﴿12﴾

Transliteration: Afatumaroonahu AAala ma yara

Translation: Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani?

53:13

وَلَقَدۡ رَءَاهُ نَزۡلَةً أُخۡرَىٰ ﴿13﴾

Transliteration: Walaqad raahu nazlatan okhra

Translation: Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa.

53:14

عِندَ سِدۡرَةِ ٱلۡمُنتَهَىٰ ﴿14﴾

Transliteration: AAinda sidrati almuntaha

Translation: A wurin da magaryar tuƙẽwa take.

53:15

عِندَهَا جَنَّةُ ٱلۡمَأۡوَىٰٓ ﴿15﴾

Transliteration: AAindaha jannatu almawa

Translation: A inda taken, nan Aljannar makoma take.

53:16

إِذۡ يَغۡشَى ٱلسِّدۡرَةَ مَا يَغۡشَىٰ ﴿16﴾

Transliteration: Ith yaghsha alssidrata ma yaghsha

Translation: Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.

53:17

مَا زَاغَ ٱلۡبَصَرُ وَمَا طَغَىٰ ﴿17﴾

Transliteration: Ma zagha albasaru wama tagha

Translation: Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.

53:18

لَقَدۡ رَأَىٰ مِنۡ ءَايَٰتِ رَبِّهِ ٱلۡكُبۡرَىٰٓ ﴿18﴾

Transliteration: Laqad raa min ayati rabbihi alkubra

Translation: Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma daga ãyõyin Ubangijinsa.

53:19

أَفَرَءَيۡتُمُ ٱللَّـٰتَ وَٱلۡعُزَّىٰ ﴿19﴾

Transliteration: Afaraaytumu allata waalAAuzza

Translation: Shin, kun ga Lãta da uzza?

53:20

وَمَنَوٰةَ ٱلثَّالِثَةَ ٱلۡأُخۡرَىٰٓ ﴿20﴾

Transliteration: Wamanata alththalithata alokhra

Translation: Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu?

53:21

أَلَكُمُ ٱلذَّكَرُ وَلَهُ ٱلۡأُنثَىٰ ﴿21﴾

Transliteration: Alakumu alththakaru walahu alontha

Translation: Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace?

53:22

تِلۡكَ إِذٗا قِسۡمَةٞ ضِيزَىٰٓ ﴿22﴾

Transliteration: Tilka ithan qismatun deeza

Translation: Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe.

53:23

إِنۡ هِيَ إِلَّآ أَسۡمَآءٞ سَمَّيۡتُمُوهَآ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلۡطَٰنٍۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَمَا تَهۡوَى ٱلۡأَنفُسُۖ وَلَقَدۡ جَآءَهُم مِّن رَّبِّهِمُ ٱلۡهُدَىٰٓ ﴿23﴾

Transliteration: In hiya illa asmaon sammaytumooha antum waabaokum ma anzala Allahu biha min sultanin in yattabiAAoona illa alththanna wama tahwa alanfusu walaqad jaahum min rabbihimu alhuda

Translation: Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton).

53:24

أَمۡ لِلۡإِنسَٰنِ مَا تَمَنَّىٰ ﴿24﴾

Transliteration: Am lilinsani ma tamanna

Translation: Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri?

53:25

فَلِلَّهِ ٱلۡأٓخِرَةُ وَٱلۡأُولَىٰ ﴿25﴾

Transliteration: Falillahi alakhiratu waaloola

Translation: To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure).

53:26

وَكَم مِّن مَّلَكٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ لَا تُغۡنِي شَفَٰعَتُهُمۡ شَيۡـًٔا إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ أَن يَأۡذَنَ ٱللَّهُ لِمَن يَشَآءُ وَيَرۡضَىٰٓ ﴿26﴾

Transliteration: Wakam min malakin fee alssamawati la tughnee shafaAAatuhum shayan illa min baAAdi an yathana Allahu liman yashao wayarda

Translation: Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda.

53:27

إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ لَيُسَمُّونَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةَ تَسۡمِيَةَ ٱلۡأُنثَىٰ ﴿27﴾

Transliteration: Inna allatheena la yuminoona bialakhirati layusammoona almalaikata tasmiyata alontha

Translation: Lalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace.

53:28

وَمَا لَهُم بِهِۦ مِنۡ عِلۡمٍۖ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّۖ وَإِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغۡنِي مِنَ ٱلۡحَقِّ شَيۡـٔٗا ﴿28﴾

Transliteration: Wama lahum bihi min AAilmin in yattabiAAoona illa alththanna wainna alththanna la yughnee mina alhaqqi shayan

Translation: Kuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya.

53:29

فَأَعۡرِضۡ عَن مَّن تَوَلَّىٰ عَن ذِكۡرِنَا وَلَمۡ يُرِدۡ إِلَّا ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا ﴿29﴾

Transliteration: FaaAArid AAan man tawalla AAan thikrina walam yurid illa alhayata alddunya

Translation: Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambaton Mu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya).

53:30

ذَٰلِكَ مَبۡلَغُهُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِمَنِ ٱهۡتَدَىٰ ﴿30﴾

Transliteration: Thalika mablaghuhum mina alAAilmi inna rabbaka huwa aAAlamu biman dalla AAan sabeelihi wahuwa aAAlamu bimani ihtada

Translation: Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyar Sa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya.

53:31

وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ لِيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ أَسَـٰٓـُٔواْ بِمَا عَمِلُواْ وَيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ أَحۡسَنُواْ بِٱلۡحُسۡنَى ﴿31﴾

Transliteration: Walillahi ma fee alssamawati wama fee alardi liyajziya allatheena asaoo bima AAamiloo wayajziya allatheena ahsanoo bialhusna

Translation: Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau.

53:32

ٱلَّذِينَ يَجۡتَنِبُونَ كَبَـٰٓئِرَ ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡفَوَٰحِشَ إِلَّا ٱللَّمَمَۚ إِنَّ رَبَّكَ وَٰسِعُ ٱلۡمَغۡفِرَةِۚ هُوَ أَعۡلَمُ بِكُمۡ إِذۡ أَنشَأَكُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ وَإِذۡ أَنتُمۡ أَجِنَّةٞ فِي بُطُونِ أُمَّهَٰتِكُمۡۖ فَلَا تُزَكُّوٓاْ أَنفُسَكُمۡۖ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَنِ ٱتَّقَىٰٓ ﴿32﴾

Transliteration: Allatheena yajtaniboona kabaira alithmi waalfawahisha illa allamama inna rabbaka wasiAAu almaghfirati huwa aAAlamu bikum ith anshaakum mina alardi waith antum ajinnatun fee butooni ommahatikum fala tuzakkoo anfusakum huwa aAAlamu bimani ittaqa

Translation: Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa.

53:33

أَفَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي تَوَلَّىٰ ﴿33﴾

Transliteration: Afaraayta allathee tawalla

Translation: Shin, ka ga wannan da ya jũya baya?

53:34

وَأَعۡطَىٰ قَلِيلٗا وَأَكۡدَىٰٓ ﴿34﴾

Transliteration: WaaAAta qaleelan waakda

Translation: Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa?

53:35

أَعِندَهُۥ عِلۡمُ ٱلۡغَيۡبِ فَهُوَ يَرَىٰٓ ﴿35﴾

Transliteration: aAAindahu AAilmu alghaybi fahuwa yara

Translation: Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin?

53:36

أَمۡ لَمۡ يُنَبَّأۡ بِمَا فِي صُحُفِ مُوسَىٰ ﴿36﴾

Transliteration: Am lam yunabba bima fee suhufi moosa

Translation: Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã?

53:37

وَإِبۡرَٰهِيمَ ٱلَّذِي وَفَّىٰٓ ﴿37﴾

Transliteration: Waibraheema allathee waffa

Translation: Da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari?

53:38

أَلَّا تَزِرُ وَازِرَةٞ وِزۡرَ أُخۡرَىٰ ﴿38﴾

Transliteration: Alla taziru waziratun wizra okhra

Translation: Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani.

53:39

وَأَن لَّيۡسَ لِلۡإِنسَٰنِ إِلَّا مَا سَعَىٰ ﴿39﴾

Transliteration: Waan laysa lilinsani illa ma saAAa

Translation: Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata.

53:40

وَأَنَّ سَعۡيَهُۥ سَوۡفَ يُرَىٰ ﴿40﴾

Transliteration: Waanna saAAyahu sawfa yura

Translation: Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi.

53:41

ثُمَّ يُجۡزَىٰهُ ٱلۡجَزَآءَ ٱلۡأَوۡفَىٰ ﴿41﴾

Transliteration: Thumma yujzahu aljazaa alawfa

Translation: Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni?

53:42

وَأَنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلۡمُنتَهَىٰ ﴿42﴾

Transliteration: Waanna ila rabbika almuntaha

Translation: Kuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take?

53:43

وَأَنَّهُۥ هُوَ أَضۡحَكَ وَأَبۡكَىٰ ﴿43﴾

Transliteration: Waannahu huwa adhaka waabka

Translation: Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka.

53:44

وَأَنَّهُۥ هُوَ أَمَاتَ وَأَحۡيَا ﴿44﴾

Transliteration: Waannahu huwa amata waahya

Translation: Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar.

53:45

وَأَنَّهُۥ خَلَقَ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰ ﴿45﴾

Transliteration: Waannahu khalaqa alzzawjayni alththakara waalontha

Translation: Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.

53:46

مِن نُّطۡفَةٍ إِذَا تُمۡنَىٰ ﴿46﴾

Transliteration: Min nutfatin itha tumna

Translation: Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.

53:47

وَأَنَّ عَلَيۡهِ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأُخۡرَىٰ ﴿47﴾

Transliteration: Waanna AAalayhi alnnashata alokhra

Translation: Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take.

53:48

وَأَنَّهُۥ هُوَ أَغۡنَىٰ وَأَقۡنَىٰ ﴿48﴾

Transliteration: Waannahu huwa aghna waaqna

Translation: Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.

53:49

وَأَنَّهُۥ هُوَ رَبُّ ٱلشِّعۡرَىٰ ﴿49﴾

Transliteration: Waannahu huwa rabbu alshshiAAra

Translation: Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira.

53:50

وَأَنَّهُۥٓ أَهۡلَكَ عَادًا ٱلۡأُولَىٰ ﴿50﴾

Transliteration: Waannahu ahlaka AAadan aloola

Translation: Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko.

53:51

وَثَمُودَاْ فَمَآ أَبۡقَىٰ ﴿51﴾

Transliteration: Wathamooda fama abqa

Translation: Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba.

53:52

وَقَوۡمَ نُوحٖ مِّن قَبۡلُۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ هُمۡ أَظۡلَمَ وَأَطۡغَىٰ ﴿52﴾

Transliteration: Waqawma noohin min qablu innahum kanoo hum athlama waatgha

Translation: Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai.

53:53

وَٱلۡمُؤۡتَفِكَةَ أَهۡوَىٰ ﴿53﴾

Transliteration: Waalmutafikata ahwa

Translation: Da waɗanda aka birkice ƙasarsu, Ya kãyar da su.

53:54

فَغَشَّىٰهَا مَا غَشَّىٰ ﴿54﴾

Transliteration: Faghashshaha ma ghashsha

Translation: Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.

53:55

فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكَ تَتَمَارَىٰ ﴿55﴾

Transliteration: Fabiayyi alai rabbika tatamara

Translation: To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake yin shakka?

53:56

هَٰذَا نَذِيرٞ مِّنَ ٱلنُّذُرِ ٱلۡأُولَىٰٓ ﴿56﴾

Transliteration: Hatha natheerun mina alnnuthuri aloola

Translation: wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.

53:57

أَزِفَتِ ٱلۡأٓزِفَةُ ﴿57﴾

Transliteration: Azifati alazifatu

Translation: Makusanciya fa, tã yi kusa.

53:58

لَيۡسَ لَهَا مِن دُونِ ٱللَّهِ كَاشِفَةٌ ﴿58﴾

Transliteration: Laysa laha min dooni Allahi kashifatun

Translation: Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta.

53:59

أَفَمِنۡ هَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ تَعۡجَبُونَ ﴿59﴾

Transliteration: Afamin hatha alhadeethi taAAjaboona

Translation: Shin, kuma daga wannan lãbãri kuke mãmãki?

53:60

وَتَضۡحَكُونَ وَلَا تَبۡكُونَ ﴿60﴾

Transliteration: Watadhakoona wala tabkoona

Translation: Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?

53:61

وَأَنتُمۡ سَٰمِدُونَ ﴿61﴾

Transliteration: Waantum samidoona

Translation: Alhãli kunã mãsu wãsã?

53:62

فَٱسۡجُدُواْۤ لِلَّهِۤ وَٱعۡبُدُواْ۩ ﴿62﴾

Transliteration: Faosjudoo lillahi waoAAbudoo

Translation: To, ku yi tawãli'u ga Allah, kuma ku bauta (masa).

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download