quranm◉

Surah An-Naba transliteration

◉ Sura · ∞

78:1

عَمَّ يَتَسَآءَلُونَ ﴿1﴾

Transliteration: AAamma yatasaaloona

Translation: A kan mẽ suke tambayar jũna?

78:2

عَنِ ٱلنَّبَإِ ٱلۡعَظِيمِ ﴿2﴾

Transliteration: AAani alnnabai alAAatheemi

Translation: A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)?

78:3

ٱلَّذِي هُمۡ فِيهِ مُخۡتَلِفُونَ ﴿3﴾

Transliteration: Allathee hum feehi mukhtalifoona

Translation: Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?

78:4

كَلَّا سَيَعۡلَمُونَ ﴿4﴾

Transliteration: Kalla sayaAAlamoona

Translation: A'aha! Zã su sani.

78:5

ثُمَّ كَلَّا سَيَعۡلَمُونَ ﴿5﴾

Transliteration: Thumma kalla sayaAAlamoona

Translation: Kuma, a'aha! Zã su sani.

78:6

أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ مِهَٰدٗا ﴿6﴾

Transliteration: Alam najAAali alarda mihadan

Translation: Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?

78:7

وَٱلۡجِبَالَ أَوۡتَادٗا ﴿7﴾

Transliteration: Waaljibala awtadan

Translation: Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?

78:8

وَخَلَقۡنَٰكُمۡ أَزۡوَٰجٗا ﴿8﴾

Transliteration: Wakhalaqnakum azwajan

Translation: Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?

78:9

وَجَعَلۡنَا نَوۡمَكُمۡ سُبَاتٗا ﴿9﴾

Transliteration: WajaAAalna nawmakum subatan

Translation: Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?

78:10

وَجَعَلۡنَا ٱلَّيۡلَ لِبَاسٗا ﴿10﴾

Transliteration: WajaAAalna allayla libasan

Translation: Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?

78:11

وَجَعَلۡنَا ٱلنَّهَارَ مَعَاشٗا ﴿11﴾

Transliteration: WajaAAalna alnnahara maAAashan

Translation: Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?

78:12

وَبَنَيۡنَا فَوۡقَكُمۡ سَبۡعٗا شِدَادٗا ﴿12﴾

Transliteration: Wabanayna fawqakum sabAAan shidadan

Translation: Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?

78:13

وَجَعَلۡنَا سِرَاجٗا وَهَّاجٗا ﴿13﴾

Transliteration: WajaAAalna sirajan wahhajan

Translation: Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?

78:14

وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلۡمُعۡصِرَٰتِ مَآءٗ ثَجَّاجٗا ﴿14﴾

Transliteration: Waanzalna mina almuAAsirati maan thajjajan

Translation: Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?

78:15

لِّنُخۡرِجَ بِهِۦ حَبّٗا وَنَبَاتٗا ﴿15﴾

Transliteration: Linukhrija bihi habban wanabatan

Translation: Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?

78:16

وَجَنَّـٰتٍ أَلۡفَافًا ﴿16﴾

Transliteration: Wajannatin alfafan

Translation: Da itãcen lambuna mãsu lillibniya?

78:17

إِنَّ يَوۡمَ ٱلۡفَصۡلِ كَانَ مِيقَٰتٗا ﴿17﴾

Transliteration: Inna yawma alfasli kana meeqatan

Translation: Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.

78:18

يَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِ فَتَأۡتُونَ أَفۡوَاجٗا ﴿18﴾

Transliteration: Yawma yunfakhu fee alssoori fatatoona afwajan

Translation: Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a.

78:19

وَفُتِحَتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتۡ أَبۡوَٰبٗا ﴿19﴾

Transliteration: Wafutihati alssamao fakanat abwaban

Translation: Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.

78:20

وَسُيِّرَتِ ٱلۡجِبَالُ فَكَانَتۡ سَرَابًا ﴿20﴾

Transliteration: Wasuyyirati aljibalu fakanat saraban

Translation: Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.

78:21

إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتۡ مِرۡصَادٗا ﴿21﴾

Transliteration: Inna jahannama kanat mirsadan

Translation: Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.

78:22

لِّلطَّـٰغِينَ مَـَٔابٗا ﴿22﴾

Transliteration: Lilttagheena maaban

Translation: Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma.

78:23

لَّـٰبِثِينَ فِيهَآ أَحۡقَابٗا ﴿23﴾

Transliteration: Labitheena feeha ahqaban

Translation: Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.

78:24

لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرۡدٗا وَلَا شَرَابًا ﴿24﴾

Transliteration: La yathooqoona feeha bardan wala sharaban

Translation: Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.

78:25

إِلَّا حَمِيمٗا وَغَسَّاقٗا ﴿25﴾

Transliteration: Illa hameeman waghassaqan

Translation: Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.

78:26

جَزَآءٗ وِفَاقًا ﴿26﴾

Transliteration: Jazaan wifaqan

Translation: Sakamako mai dãcẽwa.

78:27

إِنَّهُمۡ كَانُواْ لَا يَرۡجُونَ حِسَابٗا ﴿27﴾

Transliteration: Innahum kanoo la yarjoona hisaban

Translation: Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.

78:28

وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا كِذَّابٗا ﴿28﴾

Transliteration: Wakaththaboo biayatina kiththaban

Translation: Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyin Mu, ƙaryatãwa!

78:29

وَكُلَّ شَيۡءٍ أَحۡصَيۡنَٰهُ كِتَٰبٗا ﴿29﴾

Transliteration: Wakulla shayin ahsaynahu kitaban

Translation: Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce.

78:30

فَذُوقُواْ فَلَن نَّزِيدَكُمۡ إِلَّا عَذَابًا ﴿30﴾

Transliteration: Fathooqoo falan nazeedakum illa AAathaban

Translation: Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.

78:31

إِنَّ لِلۡمُتَّقِينَ مَفَازًا ﴿31﴾

Transliteration: Inna lilmuttaqeena mafazan

Translation: Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.

78:32

حَدَآئِقَ وَأَعۡنَٰبٗا ﴿32﴾

Transliteration: Hadaiqa waaAAnaban

Translation: Lambuna da inabõbi.

78:33

وَكَوَاعِبَ أَتۡرَابٗا ﴿33﴾

Transliteration: WakawaAAiba atraban

Translation: Da yan Mata tsaraikun Juna

78:34

وَكَأۡسٗا دِهَاقٗا ﴿34﴾

Transliteration: Wakasan dihaqan

Translation: Da hinjãlan giya cikakku.

78:35

لَّا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوٗا وَلَا كِذَّـٰبٗا ﴿35﴾

Transliteration: La yasmaAAoona feeha laghwan wala kiththaban

Translation: Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.

78:36

جَزَآءٗ مِّن رَّبِّكَ عَطَآءً حِسَابٗا ﴿36﴾

Transliteration: Jazaan min rabbika AAataan hisaban

Translation: Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.

78:37

رَّبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا ٱلرَّحۡمَٰنِۖ لَا يَمۡلِكُونَ مِنۡهُ خِطَابٗا ﴿37﴾

Transliteration: Rabbi alssamawati waalardi wama baynahuma alrrahmani la yamlikoona minhu khitaban

Translation: Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.

78:38

يَوۡمَ يَقُومُ ٱلرُّوحُ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ صَفّٗاۖ لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنۡ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَقَالَ صَوَابٗا ﴿38﴾

Transliteration: Yawma yaqoomu alrroohu waalmalaikatu saffan la yatakallamoona illa man athina lahu alrrahmanu waqala sawaban

Translation: Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.

78:39

ذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمُ ٱلۡحَقُّۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ مَـَٔابًا ﴿39﴾

Transliteration: Thalika alyawmu alhaqqu faman shaa ittakhatha ila rabbihi maaban

Translation: Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.

78:40

إِنَّآ أَنذَرۡنَٰكُمۡ عَذَابٗا قَرِيبٗا يَوۡمَ يَنظُرُ ٱلۡمَرۡءُ مَا قَدَّمَتۡ يَدَاهُ وَيَقُولُ ٱلۡكَافِرُ يَٰلَيۡتَنِي كُنتُ تُرَٰبَۢا ﴿40﴾

Transliteration: Inna antharnakum AAathaban qareeban yawma yanthuru almaro ma qaddamat yadahu wayaqoolu alkafiru ya laytanee kuntu turaban

Translation: Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download