quranm◉

Surah Al-Mutaffifin transliteration

◉ Sura · ∞

83:1

وَيۡلٞ لِّلۡمُطَفِّفِينَ ﴿1﴾

Transliteration: Waylun lilmutaffifeena

Translation: Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.

83:2

ٱلَّذِينَ إِذَا ٱكۡتَالُواْ عَلَى ٱلنَّاسِ يَسۡتَوۡفُونَ ﴿2﴾

Transliteration: Allatheena itha iktaloo AAala alnnasi yastawfoona

Translation: Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.

83:3

وَإِذَا كَالُوهُمۡ أَو وَّزَنُوهُمۡ يُخۡسِرُونَ ﴿3﴾

Transliteration: Waitha kaloohum aw wazanoohum yukhsiroona

Translation: Kuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa

83:4

أَلَا يَظُنُّ أُوْلَـٰٓئِكَ أَنَّهُم مَّبۡعُوثُونَ ﴿4﴾

Transliteration: Ala yathunnu olaika annahum mabAAoothoona

Translation: Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?

83:5

لِيَوۡمٍ عَظِيمٖ ﴿5﴾

Transliteration: Liyawmin AAatheemin

Translation: Domin yini mai girma.

83:6

يَوۡمَ يَقُومُ ٱلنَّاسُ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ﴿6﴾

Transliteration: Yawma yaqoomu alnnasu lirabbi alAAalameena

Translation: Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?

83:7

كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلۡفُجَّارِ لَفِي سِجِّينٖ ﴿7﴾

Transliteration: Kalla inna kitaba alfujjari lafee sijjeenin

Translation: Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn.

83:8

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا سِجِّينٞ ﴿8﴾

Transliteration: Wama adraka ma sijjeenun

Translation: Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn?

83:9

كِتَٰبٞ مَّرۡقُومٞ ﴿9﴾

Transliteration: Kitabun marqoomun

Translation: Wani ittãfi ne rubũtacce.

83:10

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ﴿10﴾

Transliteration: Waylun yawmaithin lilmukaththibeena

Translation: Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa.

83:11

ٱلَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ ﴿11﴾

Transliteration: Allatheena yukaththiboona biyawmi alddeeni

Translation: Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako.

83:12

وَمَا يُكَذِّبُ بِهِۦٓ إِلَّا كُلُّ مُعۡتَدٍ أَثِيمٍ ﴿12﴾

Transliteration: Wama yukaththibu bihi illa kullu muAAtadin atheemin

Translation: Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi.

83:13

إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِ ءَايَٰتُنَا قَالَ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ ﴿13﴾

Transliteration: Itha tutla AAalayhi ayatuna qala asateeru alawwaleena

Translation: Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne.

83:14

كَلَّاۖ بَلۡۜ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ ﴿14﴾

Transliteration: Kalla bal rana AAala quloobihim ma kanoo yaksiboona

Translation: A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu.

83:15

كَلَّآ إِنَّهُمۡ عَن رَّبِّهِمۡ يَوۡمَئِذٖ لَّمَحۡجُوبُونَ ﴿15﴾

Transliteration: Kalla innahum AAan rabbihim yawmaithin lamahjooboona

Translation: A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne.

83:16

ثُمَّ إِنَّهُمۡ لَصَالُواْ ٱلۡجَحِيمِ ﴿16﴾

Transliteration: Thumma innahum lasaloo aljaheemi

Translation: Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne.

83:17

ثُمَّ يُقَالُ هَٰذَا ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ ﴿17﴾

Transliteration: Thumma yuqalu hatha allathee kuntum bihi tukaththiboona

Translation: Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi."

83:18

كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلۡأَبۡرَارِ لَفِي عِلِّيِّينَ ﴿18﴾

Transliteration: Kalla inna kitaba alabrari lafee AAilliyyeena

Translation: A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna?

83:19

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا عِلِّيُّونَ ﴿19﴾

Transliteration: Wama adraka ma AAilliyyoona

Translation: Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna?

83:20

كِتَٰبٞ مَّرۡقُومٞ ﴿20﴾

Transliteration: Kitabun marqoomun

Translation: Wani littãfi ne rubũtacce.

83:21

يَشۡهَدُهُ ٱلۡمُقَرَّبُونَ ﴿21﴾

Transliteration: Yashhaduhu almuqarraboona

Translation: Muƙarrabai suke halarta shi.

83:22

إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ لَفِي نَعِيمٍ ﴿22﴾

Transliteration: Inna alabrara lafee naAAeemin

Translation: Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima.

83:23

عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ ﴿23﴾

Transliteration: AAala alaraiki yanthuroona

Translation: A kan karagu, suna ta kallo.

83:24

تَعۡرِفُ فِي وُجُوهِهِمۡ نَضۡرَةَ ٱلنَّعِيمِ ﴿24﴾

Transliteration: TaAArifu fee wujoohihim nadrata alnnaAAeemi

Translation: Kana sani a cikin fuskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima.

83:25

يُسۡقَوۡنَ مِن رَّحِيقٖ مَّخۡتُومٍ ﴿25﴾

Transliteration: Yusqawna min raheeqin makhtoomin

Translation: Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta.

83:26

خِتَٰمُهُۥ مِسۡكٞۚ وَفِي ذَٰلِكَ فَلۡيَتَنَافَسِ ٱلۡمُتَنَٰفِسُونَ ﴿26﴾

Transliteration: Khitamuhu miskun wafee thalika falyatanafasi almutanafisoona

Translation: ¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma.

83:27

وَمِزَاجُهُۥ مِن تَسۡنِيمٍ ﴿27﴾

Transliteration: Wamizajuhu min tasneemin

Translation: Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake.

83:28

عَيۡنٗا يَشۡرَبُ بِهَا ٱلۡمُقَرَّبُونَ ﴿28﴾

Transliteration: AAaynan yashrabu biha almuqarraboona

Translation: (Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi.

83:29

إِنَّ ٱلَّذِينَ أَجۡرَمُواْ كَانُواْ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يَضۡحَكُونَ ﴿29﴾

Transliteration: Inna allatheena ajramoo kanoo mina allatheena amanoo yadhakoona

Translation: Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya.

83:30

وَإِذَا مَرُّواْ بِهِمۡ يَتَغَامَزُونَ ﴿30﴾

Transliteration: Waitha marroo bihim yataghamazoona

Translation: Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe.

83:31

وَإِذَا ٱنقَلَبُوٓاْ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِمُ ٱنقَلَبُواْ فَكِهِينَ ﴿31﴾

Transliteration: Waitha inqalaboo ila ahlihimu inqalaboo fakiheena

Translation: Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci.

83:32

وَإِذَا رَأَوۡهُمۡ قَالُوٓاْ إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ لَضَآلُّونَ ﴿32﴾

Transliteration: Waitha raawhum qaloo inna haolai ladalloona

Translation: Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne."

83:33

وَمَآ أُرۡسِلُواْ عَلَيۡهِمۡ حَٰفِظِينَ ﴿33﴾

Transliteration: Wama orsiloo AAalayhim hafitheena

Translation: Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu.

83:34

فَٱلۡيَوۡمَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنَ ٱلۡكُفَّارِ يَضۡحَكُونَ ﴿34﴾

Transliteration: Faalyawma allatheena amanoo mina alkuffari yadhakoona

Translation: To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya.

83:35

عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ ﴿35﴾

Transliteration: AAala alaraiki yanthuroona

Translation: A kan karagu, suna ta kallo.

83:36

هَلۡ ثُوِّبَ ٱلۡكُفَّارُ مَا كَانُواْ يَفۡعَلُونَ ﴿36﴾

Transliteration: Hal thuwwiba alkuffaru ma kanoo yafAAaloona

Translation: Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download