quranm◉

Surah An-Nazi'at transliteration

◉ Sura · ∞

79:1

وَٱلنَّـٰزِعَٰتِ غَرۡقٗا ﴿1﴾

Transliteration: WaalnnaziAAati gharqan

Translation: Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.

79:2

وَٱلنَّـٰشِطَٰتِ نَشۡطٗا ﴿2﴾

Transliteration: Waalnnashitati nashtan

Translation: Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.

79:3

وَٱلسَّـٰبِحَٰتِ سَبۡحٗا ﴿3﴾

Transliteration: Waalssabihati sabhan

Translation: Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.

79:4

فَٱلسَّـٰبِقَٰتِ سَبۡقٗا ﴿4﴾

Transliteration: Faalssabiqati sabqan

Translation: Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umarnin Allah) kamar suna tsẽre.

79:5

فَٱلۡمُدَبِّرَٰتِ أَمۡرٗا ﴿5﴾

Transliteration: Faalmudabbirati amran

Translation: Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umarni.

79:6

يَوۡمَ تَرۡجُفُ ٱلرَّاجِفَةُ ﴿6﴾

Transliteration: Yawma tarjufu alrrajifatu

Translation: Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.

79:7

تَتۡبَعُهَا ٱلرَّادِفَةُ ﴿7﴾

Transliteration: TatbaAAuha alrradifatu

Translation: Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.

79:8

قُلُوبٞ يَوۡمَئِذٖ وَاجِفَةٌ ﴿8﴾

Transliteration: Quloobun yawmaithin wajifatun

Translation: Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.

79:9

أَبۡصَٰرُهَا خَٰشِعَةٞ ﴿9﴾

Transliteration: Absaruha khashiAAatun

Translation: Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.

79:10

يَقُولُونَ أَءِنَّا لَمَرۡدُودُونَ فِي ٱلۡحَافِرَةِ ﴿10﴾

Transliteration: Yaqooloona ainna lamardoodoona fee alhafirati

Translation: Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?

79:11

أَءِذَا كُنَّا عِظَٰمٗا نَّخِرَةٗ ﴿11﴾

Transliteration: Aitha kunna AAithaman nakhiratan

Translation: "Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"

79:12

قَالُواْ تِلۡكَ إِذٗا كَرَّةٌ خَاسِرَةٞ ﴿12﴾

Transliteration: Qaloo tilka ithan karratun khasiratun

Translation: Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"

79:13

فَإِنَّمَا هِيَ زَجۡرَةٞ وَٰحِدَةٞ ﴿13﴾

Transliteration: Fainnama hiya zajratun wahidatun

Translation: To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.

79:14

فَإِذَا هُم بِٱلسَّاهِرَةِ ﴿14﴾

Transliteration: Faitha hum bialssahirati

Translation: Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.

79:15

هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ ﴿15﴾

Transliteration: Hal ataka hadeethu moosa

Translation: Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?

79:16

إِذۡ نَادَىٰهُ رَبُّهُۥ بِٱلۡوَادِ ٱلۡمُقَدَّسِ طُوًى ﴿16﴾

Transliteration: Ith nadahu rabbuhu bialwadi almuqaddasi tuwan

Translation: A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?

79:17

ٱذۡهَبۡ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ ﴿17﴾

Transliteration: Ithhab ila firAAawna innahu tagha

Translation: Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi.

79:18

فَقُلۡ هَل لَّكَ إِلَىٰٓ أَن تَزَكَّىٰ ﴿18﴾

Transliteration: Faqul hal laka ila an tazakka

Translation: "Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka.

79:19

وَأَهۡدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخۡشَىٰ ﴿19﴾

Transliteration: Waahdiyaka ila rabbika fatakhsha

Translation: "Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoron Sa?"

79:20

فَأَرَىٰهُ ٱلۡأٓيَةَ ٱلۡكُبۡرَىٰ ﴿20﴾

Transliteration: Faarahu alayata alkubra

Translation: Sai ya nũna masa ãyar nan mafi girma.

79:21

فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ ﴿21﴾

Transliteration: Fakaththaba waAAasa

Translation: Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni),

79:22

ثُمَّ أَدۡبَرَ يَسۡعَىٰ ﴿22﴾

Transliteration: Thumma adbara yasAAa

Translation: Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri.

79:23

فَحَشَرَ فَنَادَىٰ ﴿23﴾

Transliteration: Fahashara fanada

Translation: Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.

79:24

فَقَالَ أَنَا۠ رَبُّكُمُ ٱلۡأَعۡلَىٰ ﴿24﴾

Transliteration: Faqala ana rabbukumu alaAAla

Translation: Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka."

79:25

فَأَخَذَهُ ٱللَّهُ نَكَالَ ٱلۡأٓخِرَةِ وَٱلۡأُولَىٰٓ ﴿25﴾

Transliteration: Faakhathahu Allahu nakala alakhirati waaloola

Translation: Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko.

79:26

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبۡرَةٗ لِّمَن يَخۡشَىٰٓ ﴿26﴾

Transliteration: Inna fee thalika laAAibratan liman yakhsha

Translation: Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah.

79:27

ءَأَنتُمۡ أَشَدُّ خَلۡقًا أَمِ ٱلسَّمَآءُۚ بَنَىٰهَا ﴿27﴾

Transliteration: Aantum ashaddu khalqan ami alssamao banaha

Translation: Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.

79:28

رَفَعَ سَمۡكَهَا فَسَوَّىٰهَا ﴿28﴾

Transliteration: RafaAAa samkaha fasawwaha

Translation: Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.

79:29

وَأَغۡطَشَ لَيۡلَهَا وَأَخۡرَجَ ضُحَىٰهَا ﴿29﴾

Transliteration: Waaghtasha laylaha waakhraja duhaha

Translation: Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.

79:30

وَٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ ذَٰلِكَ دَحَىٰهَآ ﴿30﴾

Transliteration: Waalarda baAAda thalika dahaha

Translation: Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta.

79:31

أَخۡرَجَ مِنۡهَا مَآءَهَا وَمَرۡعَىٰهَا ﴿31﴾

Transliteration: Akhraja minha maaha wamarAAaha

Translation: Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta.

79:32

وَٱلۡجِبَالَ أَرۡسَىٰهَا ﴿32﴾

Transliteration: Waaljibala arsaha

Translation: Da duwatsu, Yã kafe ta.

79:33

مَتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ ﴿33﴾

Transliteration: MataAAan lakum walianAAamikum

Translation: Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku.

79:34

فَإِذَا جَآءَتِ ٱلطَّآمَّةُ ٱلۡكُبۡرَىٰ ﴿34﴾

Transliteration: Faitha jaati alttammatu alkubra

Translation: To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo.

79:35

يَوۡمَ يَتَذَكَّرُ ٱلۡإِنسَٰنُ مَا سَعَىٰ ﴿35﴾

Transliteration: Yawma yatathakkaru alinsanu ma saAAa

Translation: Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata.

79:36

وَبُرِّزَتِ ٱلۡجَحِيمُ لِمَن يَرَىٰ ﴿36﴾

Transliteration: Waburrizati aljaheemu liman yara

Translation: Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani.

79:37

فَأَمَّا مَن طَغَىٰ ﴿37﴾

Transliteration: Faamma man tagha

Translation: To, amma wanda ya yi girman kai.

79:38

وَءَاثَرَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا ﴿38﴾

Transliteration: Waathara alhayata alddunya

Translation: Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya).

79:39

فَإِنَّ ٱلۡجَحِيمَ هِيَ ٱلۡمَأۡوَىٰ ﴿39﴾

Transliteration: Fainna aljaheema hiya almawa

Translation: To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma.

79:40

وَأَمَّا مَنۡ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ وَنَهَى ٱلنَّفۡسَ عَنِ ٱلۡهَوَىٰ ﴿40﴾

Transliteration: Waama man khafa maqama rabbihi wanaha alnnafsa AAani alhawa

Translation: Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.

79:41

فَإِنَّ ٱلۡجَنَّةَ هِيَ ٱلۡمَأۡوَىٰ ﴿41﴾

Transliteration: Fainna aljannata hiya almawa

Translation: To, lalle ne Aljanna ita ce makõma.

79:42

يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَيَّانَ مُرۡسَىٰهَا ﴿42﴾

Transliteration: Yasaloonaka AAani alssaAAati ayyana mursaha

Translation: Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta?

79:43

فِيمَ أَنتَ مِن ذِكۡرَىٰهَآ ﴿43﴾

Transliteration: Feema anta min thikraha

Translation: Me ya haɗã ka da ambatonta?

79:44

إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَىٰهَآ ﴿44﴾

Transliteration: Ila rabbika muntahaha

Translation: Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake.

79:45

إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخۡشَىٰهَا ﴿45﴾

Transliteration: Innama anta munthiru man yakhshaha

Translation: Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta.

79:46

كَأَنَّهُمۡ يَوۡمَ يَرَوۡنَهَا لَمۡ يَلۡبَثُوٓاْ إِلَّا عَشِيَّةً أَوۡ ضُحَىٰهَا ﴿46﴾

Transliteration: Kaannahum yawma yarawnaha lam yalbathoo illa AAashiyyatan aw duhaha

Translation: Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa.

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download