quranm◉

Surah Al-Muddaththir transliteration

◉ Sura · ∞

74:1

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمُدَّثِّرُ ﴿1﴾

Transliteration: Ya ayyuha almuddaththiru

Translation: Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi.

74:2

قُمۡ فَأَنذِرۡ ﴿2﴾

Transliteration: Qum faanthir

Translation: Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi

74:3

وَرَبَّكَ فَكَبِّرۡ ﴿3﴾

Transliteration: Warabbaka fakabbir

Translation: Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi,

74:4

وَثِيَابَكَ فَطَهِّرۡ ﴿4﴾

Transliteration: Wathiyabaka fatahhir

Translation: Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su,

74:5

وَٱلرُّجۡزَ فَٱهۡجُرۡ ﴿5﴾

Transliteration: Waalrrujza faohjur

Translation: Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu.

74:6

وَلَا تَمۡنُن تَسۡتَكۡثِرُ ﴿6﴾

Transliteration: Wala tamnun tastakthiru

Translation: Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri

74:7

وَلِرَبِّكَ فَٱصۡبِرۡ ﴿7﴾

Transliteration: Walirabbika faisbir

Translation: Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure

74:8

فَإِذَا نُقِرَ فِي ٱلنَّاقُورِ ﴿8﴾

Transliteration: Faitha nuqira fee alnnaqoori

Translation: To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho.

74:9

فَذَٰلِكَ يَوۡمَئِذٖ يَوۡمٌ عَسِيرٌ ﴿9﴾

Transliteration: Fathalika yawmaithin yawmun AAaseerun

Translation: To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya

74:10

عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ غَيۡرُ يَسِيرٖ ﴿10﴾

Transliteration: AAala alkafireena ghayru yaseerin

Translation: A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne.

74:11

ذَرۡنِي وَمَنۡ خَلَقۡتُ وَحِيدٗا ﴿11﴾

Transliteration: Tharnee waman khalaqtu waheedan

Translation: Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai,

74:12

وَجَعَلۡتُ لَهُۥ مَالٗا مَّمۡدُودٗا ﴿12﴾

Transliteration: WajaAAaltu lahu malan mamdoodan

Translation: Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya

74:13

وَبَنِينَ شُهُودٗا ﴿13﴾

Transliteration: Wabaneena shuhoodan

Translation: Da ɗiyã halartattu,

74:14

وَمَهَّدتُّ لَهُۥ تَمۡهِيدٗا ﴿14﴾

Transliteration: Wamahhadtu lahu tamheedan

Translation: Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa.

74:15

ثُمَّ يَطۡمَعُ أَنۡ أَزِيدَ ﴿15﴾

Transliteration: Thumma yatmaAAu an azeeda

Translation: Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri!

74:16

كَلَّآۖ إِنَّهُۥ كَانَ لِأٓيَٰتِنَا عَنِيدٗا ﴿16﴾

Transliteration: Kalla innahu kana liayatina AAaneedan

Translation: Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyin Mu, mai tsaurin kai.

74:17

سَأُرۡهِقُهُۥ صَعُودًا ﴿17﴾

Transliteration: Saorhiquhu saAAoodan

Translation: Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa.

74:18

إِنَّهُۥ فَكَّرَ وَقَدَّرَ ﴿18﴾

Transliteration: Innahu fakkara waqaddara

Translation: Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni)

74:19

فَقُتِلَ كَيۡفَ قَدَّرَ ﴿19﴾

Transliteration: Faqutila kayfa qaddara

Translation: Sabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara.

74:20

ثُمَّ قُتِلَ كَيۡفَ قَدَّرَ ﴿20﴾

Transliteration: Thumma qutila kayfa qaddara

Translation: Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara.

74:21

ثُمَّ نَظَرَ ﴿21﴾

Transliteration: Thumma nathara

Translation: Sa'an nan, ya yi tunãni

74:22

ثُمَّ عَبَسَ وَبَسَرَ ﴿22﴾

Transliteration: Thumma AAabasa wabasara

Translation: Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk.

74:23

ثُمَّ أَدۡبَرَ وَٱسۡتَكۡبَرَ ﴿23﴾

Transliteration: Thumma adbara waistakbara

Translation: Sa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa,

74:24

فَقَالَ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ يُؤۡثَرُ ﴿24﴾

Transliteration: Faqala in hatha illa sihrun yutharu

Translation: Sai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito."

74:25

إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا قَوۡلُ ٱلۡبَشَرِ ﴿25﴾

Transliteration: In hatha illa qawlu albashari

Translation: "Wannan maganar mutum dai ce."

74:26

سَأُصۡلِيهِ سَقَرَ ﴿26﴾

Transliteration: Saosleehi saqara

Translation: Zã Ni ƙõna shi da Saƙar.

74:27

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا سَقَرُ ﴿27﴾

Transliteration: Wama adraka ma saqaru

Translation: Kuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar!

74:28

لَا تُبۡقِي وَلَا تَذَرُ ﴿28﴾

Transliteration: La tubqee wala tatharu

Translation: Bã ta ragẽwa, kuma bã ta bari.

74:29

لَوَّاحَةٞ لِّلۡبَشَرِ ﴿29﴾

Transliteration: Lawwahatun lilbashari

Translation: Mai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna).

74:30

عَلَيۡهَا تِسۡعَةَ عَشَرَ ﴿30﴾

Transliteration: AAalayha tisAAata AAashara

Translation: A kanta akwai (matsara) gõma shã tara.

74:31

وَمَا جَعَلۡنَآ أَصۡحَٰبَ ٱلنَّارِ إِلَّا مَلَـٰٓئِكَةٗۖ وَمَا جَعَلۡنَا عِدَّتَهُمۡ إِلَّا فِتۡنَةٗ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ لِيَسۡتَيۡقِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَيَزۡدَادَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِيمَٰنٗا وَلَا يَرۡتَابَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَلِيَقُولَ ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ وَٱلۡكَٰفِرُونَ مَاذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِهَٰذَا مَثَلٗاۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَمَا يَعۡلَمُ جُنُودَ رَبِّكَ إِلَّا هُوَۚ وَمَا هِيَ إِلَّا ذِكۡرَىٰ لِلۡبَشَرِ ﴿31﴾

Transliteration: Wama jaAAalna ashaba alnnari illa malaikatan wama jaAAalna AAiddatahum illa fitnatan lillatheena kafaroo liyastayqina allatheena ootoo alkitaba wayazdada allatheena amanoo eemanan wala yartaba allatheena ootoo alkitaba waalmuminoona waliyaqoola allatheena fee quloobihim maradun waalkafiroona matha arada Allahu bihatha mathalan kathalika yudillu Allahu man yashao wayahdee man yashao wama yaAAlamu junooda rabbika illa huwa wama hiya illa thikra lilbashari

Translation: Kuma ba Mu sanya ma'abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: "Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum.

74:32

كَلَّا وَٱلۡقَمَرِ ﴿32﴾

Transliteration: Kalla waalqamari

Translation: A'aha! Ina rantsuwa da watã.

74:33

وَٱلَّيۡلِ إِذۡ أَدۡبَرَ ﴿33﴾

Transliteration: Waallayli ith adbara

Translation: Da dare a lõkacin da ya jũyar da baya.

74:34

وَٱلصُّبۡحِ إِذَآ أَسۡفَرَ ﴿34﴾

Transliteration: Waalssubhi itha asfara

Translation: Da sãfiya idan ta wãye.

74:35

إِنَّهَا لَإِحۡدَى ٱلۡكُبَرِ ﴿35﴾

Transliteration: Innaha laihda alkubari

Translation: Ita (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce.

74:36

نَذِيرٗا لِّلۡبَشَرِ ﴿36﴾

Transliteration: Natheeran lilbashari

Translation: Mai gargaɗĩ ce ga mutum.

74:37

لِمَن شَآءَ مِنكُمۡ أَن يَتَقَدَّمَ أَوۡ يَتَأَخَّرَ ﴿37﴾

Transliteration: Liman shaa minkum an yataqaddama aw yataakhkhara

Translation: Ga wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta.

74:38

كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡ رَهِينَةٌ ﴿38﴾

Transliteration: Kullu nafsin bima kasabat raheenatun

Translation: Kõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce.

74:39

إِلَّآ أَصۡحَٰبَ ٱلۡيَمِينِ ﴿39﴾

Transliteration: Illa ashaba alyameeni

Translation: Fãce mutãnen dãma.

74:40

فِي جَنَّـٰتٖ يَتَسَآءَلُونَ ﴿40﴾

Transliteration: Fee jannatin yatasaaloona

Translation: A cikin Aljanna suna tambayar jũna.

74:41

عَنِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ ﴿41﴾

Transliteration: AAani almujrimeena

Translation: Game da mãsu laifi.

74:42

مَا سَلَكَكُمۡ فِي سَقَرَ ﴿42﴾

Transliteration: Ma salakakum fee saqara

Translation: (Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin Saƙar?"

74:43

قَالُواْ لَمۡ نَكُ مِنَ ٱلۡمُصَلِّينَ ﴿43﴾

Transliteration: Qaloo lam naku mina almusalleena

Translation: Suka ce: "Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba."

74:44

وَلَمۡ نَكُ نُطۡعِمُ ٱلۡمِسۡكِينَ ﴿44﴾

Transliteration: Walam naku nutAAimu almiskeena

Translation: "Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba."

74:45

وَكُنَّا نَخُوضُ مَعَ ٱلۡخَآئِضِينَ ﴿45﴾

Transliteration: Wakunna nakhoodu maAAa alkhaideena

Translation: "Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa."

74:46

وَكُنَّا نُكَذِّبُ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ ﴿46﴾

Transliteration: Wakunna nukaththibu biyawmi alddeeni

Translation: "Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako."

74:47

حَتَّىٰٓ أَتَىٰنَا ٱلۡيَقِينُ ﴿47﴾

Transliteration: Hatta atana alyaqeenu

Translation: "Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana."

74:48

فَمَا تَنفَعُهُمۡ شَفَٰعَةُ ٱلشَّـٰفِعِينَ ﴿48﴾

Transliteration: Fama tanfaAAuhum shafaAAatu alshshafiAAeena

Translation: Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba.

74:49

فَمَا لَهُمۡ عَنِ ٱلتَّذۡكِرَةِ مُعۡرِضِينَ ﴿49﴾

Transliteration: Fama lahum AAani alttathkirati muAArideena

Translation: Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya.

74:50

كَأَنَّهُمۡ حُمُرٞ مُّسۡتَنفِرَةٞ ﴿50﴾

Transliteration: Kaannahum humurun mustanfiratun

Translation: Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne.

74:51

فَرَّتۡ مِن قَسۡوَرَةِۭ ﴿51﴾

Transliteration: Farrat min qaswaratin

Translation: Sun gudu daga zãki.

74:52

بَلۡ يُرِيدُ كُلُّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ أَن يُؤۡتَىٰ صُحُفٗا مُّنَشَّرَةٗ ﴿52﴾

Transliteration: Bal yureedu kullu imriin minhum an yuta suhufan munashsharatan

Translation: A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa

74:53

كَلَّاۖ بَل لَّا يَخَافُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ ﴿53﴾

Transliteration: Kalla bal la yakhafoona alakhirata

Translation: A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira.

74:54

كَلَّآ إِنَّهُۥ تَذۡكِرَةٞ ﴿54﴾

Transliteration: Kalla innahu tathkiratun

Translation: A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce.

74:55

فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ ﴿55﴾

Transliteration: Faman shaa thakarahu

Translation: Dõmin wanda ya so, ya tuna.

74:56

وَمَا يَذۡكُرُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ هُوَ أَهۡلُ ٱلتَّقۡوَىٰ وَأَهۡلُ ٱلۡمَغۡفِرَةِ ﴿56﴾

Transliteration: Wama yathkuroona illa an yashaa Allahu huwa ahlu alttaqwa waahlu almaghfirati

Translation: Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara.

Transliteration source: English Transliteration by Tanzil. Used under Tanzil's non-commercial terms; see the source and latest updates at Tanzil. Tanzil translation download